Bude YouTube channel nada matukar amfani, musamman a zamanin yanzu a dalilin haka ne a wannan post din inshallahu zamuyi magana akan yadda ake bude YouTube channel wadda zaka rika daura Bidiyoyinka kyauta kamar yadda baya mukayi yadda ake download YouTube video a waya da kuma a computer.
To amma kafin mu tafi akan yadda zaka bude taka channel din bari mu fara bayani akan micece ita kanta youtube channel.
Table of Contents
Mi ake nufi da YouTube Channel?
Idan aka ce YouTube channel ana nufin bude wata tasha a kafar sada zumunta ta youtube wadda mutum zai ringa daura videos dinshi ta yadda mutanen duniya zasu rika gani musamman waddanda sukayi subscribing a channel din.
Tun bayan mallakar youtube da kamfanin Google yayi yacigaba da samun karbuwa a wajen mutanen duniya inda kullun biliyoyin mutane na kallon bidiyoyi a kafar.
Sanadayyar hakan ne ya bada damar kasuwanci kala kala da kuma abubuwan amfani na inganta rayuwa suka habbaka a kafar.
karanta: Yaron da ya samu dala miliyan 22 a internet
Ina tabbatar ma idan kayi amfani da abubuwan da suka dace zaka samu da youtube sosai tun daga lada kamai dora abubuwa irin na wa’azi, kudi da sauransu,
Matakan bude channel din
Bayan karamar matashiyar da muka yi a sama a wannan fannin kuma zamu yi magana akan matakan da zaka bi domin ka bude taka channel din.
Mataki na farko
Abu mai amfani na daya shine ya kasance kana da Google account wato kana da gmail account idan baka da shi ga yadda zaka bude Gmail account nan. Idan ka bude sai ka shiga kayi login a ciki.
Ga link din da zaka shiga nan kayi login in kana da accoun dama.
Link: https://www.youtube.com/create_channel
Bayan kasa Email address dinka da kuma password dinka wato bayanin sirri sai kayi login kamar yaadda ka gani.
Mataki na Biyu
Daka gama loga email dinka to shikenan zakaga batare bata lokaci ba sun bude maka YouTube channel dinka ta fito kamar haka da sunan ka wanda kake amfani da shi.
Daga nan kuma sai mu tafi a mataki na ukku.
Mataki na Ukku
A wannan mataki kila mai karatu zaka ce to ina zan daura bidiyo a youtube channel din? to ga wurin a nan sai ka danna upload video zaka ganshi a ztsakiya.
Daka danna shi to zai baka yimaka welcom sai ka danna continue daga nan sai kaga ya kaika a inda zaka zabi bidiyon da kakeson daurawa daga wayarka ko kuma computer dinka.
kaga ga wani mashiya kalli sama ga kuma wani malatsi sai ka danna upload zai nuna maka abubuwan da ke cikin computer dinka koma waya sai ka zabi folder da ka aje bidio wadda kake son daurawa a cikin channel dina.
To da ka zaba shikenan. Barka ka daura bidiyonka ta farko to yanzu abunda ya rage maka shine gyara channel din da kuma yawan daura mata bidiyoyi a kai yadda masu kallo zasu iya shiga a cikinta.
Ta yaya zan samu yan kallo?
Nasan mai karatu bayan ka dora video dinka zaka zaku a kalle ta saboda zakaga a cikin youtube wasu har samun yan kallo milayan suke koma fiye da haka.
To ga wasu daga cikin abubuwa masu mahimmanci wanda zaka kula dasu kafin ka daura bidiyonka a youtube channel wanda zai taimaka maka sosai ka samu yan kallo.
- Bidiyon tana da amfani a rayuwar mutane
- Ya kasance ka inganta Video din ka gyra ta yadda zata buge yan kallo
- Ya kasance kana ba yan kallonka shawara suyi subscribe a channel din
- Ya kasance ba abubuwan batsa kake watsawa ba da abubuwan da basu da amfani a rayuwar mutane ko kuma suka tsana.
- Kar ka rinka dora abubuwa na karya a YouTube channel dinka har kama ka ana iay yi.
karata:
Yadda zaka bude karamar website na Blogger | Lesson 1
Fannonin computer wanda ake koyo da aka fi samun kudi da su
Wuren da zaka samu yan kallo
Akwai wurare da dama da zaka samu masu kallon abubuwan da kake daurawa a youtube channel dinka ga wasu kadan daga cikinsu da bayanin su.
Kafafen sada zumunta
Ana samun yan kallo sosai a kafafen sada zumunta imma dai ka bude facebook page dinka wanda zaka habbaka wanda a wurina ma yafi.
ko kuma ka ringa bi group group kana watasawa yadda duk wanda yake cikin group din zai gani amma akwai abun lura a nan dole sai ka samu group dinda ake yawan magana a ciki.
Fadakarwa
Wannan ma wata hanya hanya ce da zaka kimata channel dinka da hada ta hanyar kaya ma abokai yanuwa da mutanen arziki saboda da ka gaya ma wani shima zai je ya kaima wani rahoto hakan yana taimakawa sosai shima.
kammalawa
To kamar dai yadda mukayi bayani a baya wadannan sune bayanai dalla dalla akan yadda ake bude youtube channel da kuma yadda zaka inganta ta.
karanta:
Fannonin computer wanda ake koyo da aka fi samun kudi da su
Yadda ake koyon Computer da kuma Bayani akan Ilimin Computer
Ma’anar Sana’a da kuma Amfaninta
Ga mai taambaya ko kuma wani karin bayani kar ya damu yana iya yinsa a comment section wanda yake a kasa zan bashi amsa a cigaba da kasancewa da mu a WWW.HAUSAWASITE.COM.NG a koda yaushe domin saun post masu amfani mungode.
Author Profile

Latest entries
Kimiyya da FasahaSeptember 22, 2023Wuraren da Zaka Samu Kayan Kere-Keren da Kake Bukata
Wayar HannuJuly 17, 2023Yadda Ake Amfani da WPS Software
Wayar HannuJuly 4, 2023Yadda Zaka Zama Dillalin Yanar Gizo
Wayar HannuJuly 3, 2023Yadda Ake Samun Aiki Online ta Hanyar Linkedin