Skip to content
Home » Yadda ake koyon Computer da kuma Bayani akan Ilimin Computer

Yadda ake koyon Computer da kuma Bayani akan Ilimin Computer

Kana son koyon computer? to madallah idan akayi magana akan ilimin computer to ba wani abu ne mai wahala ba domin yana da saukin yi musamman indai kana da computer dinka mai lafiya to kawai bi ne cikin sati ukku kana iya kwarewa a fanin com puter.

A cikin wannan post din inshallahu zamu yi bayani akan yadda zaka koyi ilimin computer da kuma abubuwan da yakamata ka koya game da ita masu amfani kai dama yadda ake samun kudi da wasu daga cikin fannoninta.

A ina yakamata Inje Domin Koyon Computer?

Koyon computer

Tabbas idana aka fara magana akan computer ga duk wanda yake son koyonta to da wannan zai fara, to ba abiu ne mai wahala ba.

Saboda akwai wurare da yawa wasu a online ma kana iya koyo saboda cigaban da aka samu wani lokacin kuma kana iya zuwa wasu wurare domin samun iliminta.

Karanta: Fannonin computer wanda ake koyo da aka fi samun kudi da su

Amma kafin in lissafa maka inda zaka koya bari in dan yi bayani kadan game da wanene ya iya computer tsakanin wanda ya karanta da mai yi.

Wa ya iya computer?

iya computer

Amsar wannan tambayar itace wanda ya iya computer wanda yake yawan amfani da ita bawai wanda yake zuwa makaranta yana kwankwadar iliminta zallah ba.

Domin ita computer tana bukatar yawan yi abu ce a aikace wato practical a turance ba theory ba a karance ika’idar itace indai kana yi to kafi wanda bayayi yinta nesa ba kusa bama.

Inda ake koyonta

Akwai wuarare da yawa inda ake koyon computer amma ga wasu daga  cikin sanannanun wurare tare da bayaninsu dalla-dalla.

Koyo a Yanar Gizo(Internet)

Internet waje ne wanda mutum idan yayi amfani da shi yana iya habbaka kansa sosai ta fannin karatu ko wane iri ne.

To idan har kana da computer kana iya samun wani ya koya maka computer a groups ko kuma ta hanyar ziyartar shafukan yanar gizo.

Wata hanaya mai kama da wannan kuma kana iya amfani da YouTube domin kallon bidiyoyi masu kama da hakan amma ina baka shawara kana iya samun wani wanda zai kasance maka ta jagorance ka wajen koyon ya zama a matsayin mai koya ma.

Sanarwa

Ga mai son koyon computer ya tuntube mu a

+2349037157675 ko ta Email s a fasahaltd@gm,ail.com

 

Ta hanyar karantar ta

Kana iya koyon computet ta hanya shiga babbar makaranta ta gaba da sakabdire inda zaka iya karantar ta a matakin Degree, NCE ko ma Diploma.

Amma wannan a wani lokacin yana kasancewa kila ma wani fannin kake karaanta kuma kawai ita bwai sha’awar ka karance ta a matakin babbar makaranta kake ba to kana iya zuwa a mataki na ukku wanda shine.

Ta hanyar koyo a Inda ake bada Horo

Akwai wurare da suke dan hada certificate na computer wanda suke k,oya ma mutane yadda zasu yi aiki da computer to suma gaskiya suna taimakawa kana iya biyan yan kudi ka shiga.

Domin daga cikin amfanin koyo a nan ma zaka ga cewa zasu koya maku kuma su baku shedar gamawa alokacin da kuka kammala wannan karatu,

Muhimman abubuwan Koyo

Idan ka koyi yadda ake bide computer da kuma kashe ta bude cen wuri da kuma kullewa to bayan nan akwai ya kamat ka kware a wani fannin wanda kana iya samun kudi da shi yana ma iya zamar maka a matsayin sana’a.

Karanta:

Yadda Zaka samu kudi da abubuwan da ka iya da Computer su zama Sana’arka da inda zaka koye su

To ga dai wasu daga cikin muhimman wuraren kwarewa a takaice

  • Fannin office
  • Programming
  • Database
  • Browsing da kuma Downloading

Wadannan wasu wurare ne masu amfani da ya kamata ka samu daya ka kware a kanasa indai kana son ka samun kudi da computer.

Karanta:

Ma’anar Sana’a da kuma Amfaninta

yadda ake samun kudi online (Cikakken Bayani)

Farashin Dala zuwa Naira: Bayani akan yadda zaka ga canjin kudi online

Kammalawa

Computer dai abu ce mai amfani wanda ya kamata mutum ya tsaya ya koya kuma ana samun kudi da ita wanda wasu daga nan zasu samu sana’oin da zasu dogara da su a rayuwarsu ta yau da kullun.