Skip to content
Home » Bayani akan sana’ar daukar hoto da yadda ake yinta

Bayani akan sana’ar daukar hoto da yadda ake yinta

Sana’ar Daukar hoto wata sana’a ce wadda a duniya aka dade ana yinta kuma duk yadda zamani ya juya zaka ga akwai bukatar a cigaba da yinta kuma akwa masu yinta din.

Kamar yadda a baya mukayi pos akan ma’anar sana’a da abubuwan da suka shafe ta kuma da wasu muhimman abubuwan da ya kamata ka san kafin farawa aa yau mun zakulo ta kuma zamuyi bayanin akanta da abubuwan da suka shafe ta.

Ya sana’ar daukar hoto take?

Wannan dai sana’a kamar yadda na fada an dade ana yin ta kuma tana daga cikin muhimman sana’oin da da wuri sun canza kama da salon yadda ake yindsu saboda canzawar zamani.

Sana'ar hoto

Sauye sauyen na zuwa ne a dalilin yanayin yadda abubuwan cigaba na kimiyya da fasaha suke cigaba da habbaka a fadin duniya.

Yadda zan baka misalin yadda ta canza salo a shekarun baya bayabayan nan gashiu kamar haka yadda zaka fahimci abun dalla- dalla.

Yadda ta canza shekara 20 da suka wuce

Zamanin Wanki Chemical

A farko dai ana kasance wajen shekarar 2000 bari in dauketa saboda shekara ashirin na ce, to a wannan lokacikn ana amfani ne da flom da chemicals wajen wanke hoto kafain a samu damar ba wanda ya dauka kuma yana dan daukar kwanaki in aka daukeka kafin a wanko maka.

A lokacin duk mai hoton da yayi kuskuren fiddo film dinsa a ckn haske to lalacewa yake kuma wani abun matsala na gaba akwai adadin da sai yayi taka tsan tsan in yana wanke hoyon da chemical in ba haka ba hoyon ya kone.

Zamanin Digital na wanki

Zamani na biyu kuma shine lokac in da cigaba ya fara zuwa na camera mai karfi wato ta digital inda an samu sauye sauye da dama sosai ba kamar na farkon ba.

Saboda lokacin an bar amfani da film ne an dawo amfani da memory na camera wanda da kwara daya sai kayi tayin hoyuna da dama bai cika ba koma ya nuna ya motsa saboda a Gigabyte yake.

Wannan zamani kusan har yanxu ana amfani dashi wajen wamnke hoto ba’a bar sa ba sai dai abubuwa suna janyewa saboda zigaban wayoyin hannu da ko ina ga camera nan.

Zakaga yanzu idan ba ta ,mutum so yake a yi mashi passport ba ba’a cika damuwa da wanke hotuna ba kamar da.

karanta: Hanyoyin Samun kudi masu saukin ga Dalibai

Zamanin Dagital na ma’adana

Wannan zamani shine yanzu muke akansa yadda fasalin sana’ar ya canza kuwa shine zaka ga sai dai kaga an kira mai hoto ya dauki hotuna.

Bayan ya gama sai a ce ya gyra su da computer wasu ma masu hotunan camera dinsu tana da kyau da inganci yadda tana daukar hoto da kyau sosa.

Da ya kama sai a biya shi ya tura ma wanda tyayi ma hoton a cikin memory, waya ko kuma a cikin computer wanda shi kuma yana iya daurawa a Google drive ko cloud domin ajiya.

Karanta : Yadda ake amfani da Google Drive don aje waka hoto video ko filolo ajiya ta har abada

To tunda munji gabatarwa akan yadda zamani ya canza yanayin sana’ar bar mu tafi akan yadda zaka fara

Yadda ake farawa

Akwai wasu muhimman abubuwan da ya kamata ka fahimta kafin ka fara wannan wannan sana’ar tare da kayan aikin da kake  bukata kafin yin hakan ga su kamar haka.

fara daukar hoto

Yanayin ya zaka fara?

Yadda zaka fara ta dole ne ka tabbatar da zaka bi zamani kumaa ka koyi daukar hoton  kana iya daukar mutum hoto ka kuma wanke masa kayansa ka bashi idan har yana da bukatar hakan.

Idana kuma so yake ka dauke shi kawai ba tare da ka wanke masa ba ka tura masa a cikin wayar to hakan ma yana kyau a ce ka saita camerar ka kuma kana da kayan gyaran hoton.

Kuma yana da kyau ka san cewar ita wannan sana’ar ka samu jari yadda zaka mallaki kayan aiki wanda zan lissafa maka su kamar haka.

Karanta: Yadda ake fara kasuwanci da karamin jari

Kayan aiki

Ga lissafain kayan aikin kamar haka

  • Camera
  • Triport
  • Almakashi
  • Rezar
  • Memory
  • Computer
  • Card Reader da sauransu.

Wadannan abubuwan da na ambata maka a sama suna da matukar amfani a harkar hoton naka ka mallakesu bayan nan sai ka kama shagon wanda zaka yi.