Skip to content
Home » Bayani akan Dalibai da yadda zasu dogara da kansu

Bayani akan Dalibai da yadda zasu dogara da kansu

A matsayinka na dalibi wanda yake karatu a makaranta akwai hanyoyi daban daban da zaka iya amfana da kana karatu samun kudi ta sana’a irin ta dalbai, kuma bayan ka gama akwai hanyoyin da zaka bi domin ka c moriyar karatunka wanda ka kammala.

A yau inshallahu zanyi magana ne akan wasu muhimman abubuwan da ya kamata ka kula da duma wasu da ya kamata ka fara musamman ga dan talakka wanda aiki  yana da wahalar samu a wajensa duk da mai kudin ma yana fuskantar haka.

Da farko bari in baka haske akan yadda duniyar yanzu ta koma a kana rin wannan karatu na zamani ya sauya da yadda wasu kasashe suke cin moriyarsa.

Yadda zamani ya Juya ma Dalibai ta Fuskar dogaro da kai

A za,manin nan da muke ciki da dama daga cikin dalibai wadanda suke gama makaranta a kasashen da suka cigaba suna kokarin fara wani kasuwanci ko kuma su fara sana’a wanda hakan yake tunzura su na nyyar su maida wannan abun a matsayin kamfani na kansu.

hanyoyin dogaro da kai na dalibai

Abunda ya kamata ka sani a yanzu shine dunya ta gane aiki yana da illa amma kasuwanc sh ke sama da koma, saboda idan akace kowa yayi ta yin aiki suwa zasu bude kasuwanci da kamfan.

Kuma shima a fannin kasuwancin ka bude kamfanin ka yafi, nasan zaka ce ya za’ay nda bani da kud in bude kamfani na, aa ba haka abun yake ba.

Ai kamfanin Google dana Apple da kake gani daga garejin kofar gida suka fara kuma yanzu gashi sun zama manyan kamfunnan a duniya wanda ana takama da su a harkar kimiyya da fasaha.

Shi abunda ya kamat ka sani shine cewar kamfani yana nufin idea ce wadda kake son aiwatarwaa wadda zata amfani mutane a dalilin hakan sai ka samu kudi.

Don haka kaima a yau zaka iya abunda zaka sani shine cewar suma turawa ba wani abu suka fimu ba yan africa kawai naci ne, hakuri da kuma jajircewa.

Yadda zaka ci moriyar karatunka

Karatun da kake yi a jami’a ko kuma wata makaranta karamin tunani ne kace dole kai sai aiki kawai zakayi a’a kayi tunanin ya zaka maida shi sana’a ta hanyar duba abubuwa kamar haka.

  • Hanyoyin da zaka inganta wani bangare da kaga yana da rauni a cikin alumma wanda ya shafi karatunka
  • Kirkiro sabbin abubuwan da babu su a cen
  • Tunani akan yadda zaka samu wadanda zasu kama maka a tafiyar ka.

Idan kuma ka ce a’a ni abunda nakeyi ba shi nke so n dasa a kansa ba ina son in koma wata sabuwar hanyar neman to akawai mafita itama daman an fi son abunda zaka ya jurewa.a

Akawai abubuwan da suke shgowa na zamani wanada idan kana karatu ma sunfi yimaka saukin yi musamman wadanda suka shafi comfuter.

Ga wadansu wanda naga zasu amfane ka a matsayinka na dalbi.

Rubutun Littafi

Rubutun littafi yana da sauki musamman ga wanda yake yin karatu kuma a duniyar yanzu ko wane irin littafi kana iya saidawa idan ka shirya matakan da zaka bi.

A zamanin yanzu ko a PDF format kana iya saida shi ka samu daloli a Amazon Kinddle bayan kana iya hada hard copy wanda zaka daura kana ta sada ma jama’a suan saye hgakan fa yana kara taimaka maka wajen  habbaka har iliminka.

Karanta : Yadda Ake Fara Kasuwancin Printing da Photo Copy

Manhajoji masu amfani ga masu rubutun littafi kamar Hausa Novel

Kwarewa a computer

Akwai fannoni da dama na computer wanda ake samun kudi sosai da su idna mutum ya tsaya ya natsu ya iya, musamman ma dalibi computer tana taimaka mashi sosai ko a ayyukan makaranta kamar su project.

Kaga yana da kyau ka iyata kuma ni a fahimta ta tafi kowace hanya saurin samun kudi ga dalibsaboda akawa abubuwa irin na zane waanda zakayi a biya ka nan take da sauran aiyyuka makamantan su.

karanta : Fannonin computer wanda ake koyo da aka fi samun kudi da su

Manhajar software da ya kamata ka zaba domin Kasuwanci

Kananun kasuwanci

Abu na gaba kuma shine akwai yan kananun kasuwancin da kana iya ka fara duk da kana mtsayinka na dalbi wanda kana ya saida ma yaan ajiku.

Daga c ikin irinsu akwai irin sana’ar data, saida kati da sauransu kana iya farawa ko bakada wan jari babba a lokacn da kake so.

karanta: Kasuwanci guda 10 wanda aka fi saurin samun kudi da su

Kananun sana’oi

Akwa kuma wasu sana’oi kananu masu saukin yi wanda kana iya fara su suma kamar su man shafawa, air freshner, sabulu da ma sauransu wanda suka shafi abubuwan da ake yawan amfani da su a yau da kullun.

A cikin wannan website din nayi magana kan sana’oi kala daban daban wadanda zaka iya fara kana iya dubawa.

karanta :

Yadda ake fara kasunacin hada man shafawa a samu kudi dashi sosai

AIR FRESHENER: sinadaran da ake Hada air freshener da kayan hadinta

Samun kudi Nan Take Bonanza ga kowa da kowa