You are currently viewing Sana’ar Kiwo da Abubuwan da ta Kunsa

Sana’ar Kiwo da Abubuwan da ta Kunsa

Sana’ar kiwo wata sana’a ce wadda ta dade ana yinta a kasar hausa kuma tana daga cikin sana’o’in gargajiya wanda aka gada daga kaka da kakanni wanda har a yanzu dinma ba a bar ta ba ta shiga  a cikin manyan sana’oi  zamani wanda in mutum yayi su a zamanance.

Ita dai kowa yana iya yinta da karamin jari ne ko kuma da babban jarinsa duka lafiya lau mutum yana iya fara shi daidai bakin karfinsa da kuma yadda yaga yana iyawa.

A cikin wannan post din inshallahu zamuyi bayani akan minene ita wannan sana’a take nufi wadanne abubuwa ta kunsa da kuma yadda zamani ya sauya ta tare da hanyoyin da ake samun kudi da ita na zamani.

sana'ar kiwo da kuma bayani akan ta

Mi ake nufi da Sana’ar Kiwo?

Ana nufin mutum ya riki kiwon babbobi musamman ma na gida a matsayin abun yi wanda zai rika samun kudi da shi. akwai abubuwa da yawa da hausawa suka dade suna kiwatawa tun kafin zuwan turawa da kuma ma har yanzu da zamani ya zo bayn abubuwa sun sauya.

Mutumin da ya riki kiwi a matsayin sana’a ana kiranshi da makiyayi a hausance, wanda ya hada da shin shi yake kiwata ma wani ana biyansa ko kuma sunyi tsari ko kuma a’a da kansa yake yin sana’ar yayi ya saida idan dabbobin sun girma.

Karanta : Koyon Sana’a: Muhimman Abubuwan Dubawa kafin koyon sana’a

Kananan Dabbobin da Hausawa Suke Kiwatawa

Hausawa suna da wasu dabbobin da suka fi yawan kiwatawa kuma wannan ya samu ne a sabili da alakar su ta tarihi da suka samo daga larabawa tun zamanin kakanni wanda dabbobin sun hada da.

  • Shanu
  • Awaki
  • Raguna
  • Tsuntsaye
  •  Rakuma

 

Yadda ta kasu

Ita dai wannan sana’a game da yadda ake yinta ana iya kasa ta zuwa manyan gidaje guda biyu wanda suka hada da bada kiwo da kuma mutum yayi shi da kansa.

Bada Kiwo

Bada kiwo salo ne na kiwo amadadin mutum ya kiwata dabbarsa da kansa sai ya ba wani ya kiwata masa da sharadin idan an saida su raba ribar a tsakaninsu a fidda uwar kudin sannan a fidda ribar daban sai a raba a kan sharadin da suka tsaya akan shi.

Ita irin wannan salon musamman ga wadanda basuda wurin kiwo sun fi yinshi ta nan ne zasu kaima  yan kauye ko kuma fulani su basu dabbinsu su kiwata masu su kuma suna zanne a gida ya danganta ga yadda suka tsara amma yawanci mai dabba yana biyan na abinci sosai.

Kiwon kai

Fanni na biyu kuma shine mutum ya kiwata abunsa da kansa wanda shi zai samu fili mai fadi inda zai sa dabbobin ya rika basu abinci da ruwa ko kuma yana kaisu su ci a waje.

A nan fannin ne wadanda suka bunkasa a harkar kiwpo suke samun ma’akata su dauke su aiki su rika biyansu albashi ya danganta ga yadda suka tsara sati ko kuma a duk wata.

Yanayin na gargajiya

A zamani da kusan alummar hausawa  kashi 95% suna yin sana’a kiwo inda suka hada ta tare da noma wanda da haka suke rike kansu suna samun abunda zasu cida iyalai.

Bayan rike gida sai kuma yadda sukeyi shine suna yin noma a shekara bayan kaka tayi amfanin gona yayi an yi girbi dan abunda aka samu ana saida wani kason wani kuma kason sai a ajiye shi a cikin rumbu, wanda aka saida da shi za’a sayi dabba kamar sa sai a  aje shi a saida idan wata hidima ta tashi.

Yanayin kiwon da ba kamar na zamanin yanzu bane babu cigaba kudsan idan dabbar mutum tana rashin lafiya babu cigaban magunguna kamar yadda zamani yazu aka same su kuma dabbobin basu saurin girma kamar kaza sai ta yi watanni amma na yanzu cikin wata daya ana iya ci.

Yanayin na Zamani

A dalilin cigaba da aka samu na kimiyya da fasaha sana’ar kiwo ta canza salo sosai kuma a yanzu makiyaya sunfi samun kudi ba kamar a da ba sodoba samun magunguna da kuma yanayin yadda ake sarrafa abubuwan da ake fiddawa daga dabbobin ba kamra a zamanin da bane.

Kamr dangane da kiwon shanu misali  a da madara idan aka dibe ta to kawai za’a yi nono da man shanu ne amma a yanzu zuwan zamani takai ga ana iya fidda yougut, butter, cheese, da kuma ita kanta madarar kaga ba karamin cigaba aka samu a wannan fannin ba.

Karanta : Ire-Iren Sana’o’in Zamani 5 da ake yi da waya don samun kudi

Yadda aka fi samu da shi

Ita wannan sana’a gaskiya an fi samu ne da ita musamman idan mutum ya  hada ta noma yafi samun sauki saboda wasu abubu kamar haka.

Na farko abincin da ya noma zai samu saukin hada abincin dabbobi da shi ba sai ya sha wahalar kashi kudin abincin dabbobi ba sosai.

Na biyu kuma takin dabbobin da ya samu koda mutum ya saida wani to idan ya tashi yana da wani wanda zai iya ajewa domin yayi noma da shi kaga ba sai ya sha wahalar yawan sayen taki ba.

Na ukku kuma shine kamar ga masu kiwon shanu suna iya amfani da dabbobinsu domin yi ma kansu hida, kuma wani abun burgewar kuma suna iya yima wani huda a biya su wanda dama ce ta samun karin kudin shiga a sana’ar.