Skip to content
Home » Video Coverage da Kuma Bayani akan Sana’ar

Video Coverage da Kuma Bayani akan Sana’ar

Video coverage tana daya daga cikin sna’oin da ake samun kudi da su kuma aka dade ana yi a fadin duniya tun bayan samuwar camera a duniya wadda suna tafiya ne kamar yanayin sana’ar daukar hoto.

A cikin wannan post din na yau zamuyi magana akan ida wannan sana’a yanayin yadda ake yinta, yadda  ta kasance a baya da kuma yanayin yadda zamani ya sauya ta tare  da kuma abubuwan amfani wanda kake bukata kafin ka fara yinta.

sanaar video coverage

Ya Sana’ar video coverage take kuma mi ta kunsa?

Ita dai wannan sana’a ta daukar bidiyo ko kuma a ce video coverage a turance sana’a ce da aka dade ana yinta saboda yadda bidiyo take taka muhimmiyar rawa musamman ta fannin adana abubuwa a matsayin na tarihi.

Baya ga hakan a ce bidiyo kawai ana amfdani da a je abubuwan tarihi kuma wani daga cikin muhimman amfanin ta shine adana abubuwan karaantaswa.

Saboda bincike ya nuna abu idan aka dauke shi a faifan bidiyo anfi fahimtar shi sosai fiye da ace a hogto yakde kuma a wani yanayin na daban dalilin haka ne dalibai koda basu je makaranta ba suna iya kallon bidiyo na karatu su amfana sosai akamar a gabansu a kayi musamman zamnin nan na Internet.

Karanta: Bayani akan sana’ar daukar hoto da yadda ake yinta

A yanayin wannan sana’ar a da da yanzu kamar yadda na fada ta canza salo sosai saboda shigowar saabbin abubuwa na cigaban kimiyya da fasaha wanda ya canza launintaa kgabakidaya

Yanayin sana’ar a zamanin da

Ita yadda ake yin wannan sana’ar a zamanin da shine ana amfani ne da camera wadda bayan an daukin bidiyon za’a zo a sa shi a cikin cassette.

wanda shi wannan casette din shima ya rabi kusan gida gida biyu akwai na nada mai tape a cikinsa akwai kuma wanda ya ke a zagaye wanda ake cema na disc amma shi daga baya ne ya shigo.

A lokacin da duk da ana gyara bidiyo ba’a cika samun kayan gyaranta ba sosai, saboda karancin cigaba da ake fuskanta ba kamar a yanzu ba.

Kuma a zamanin da hanyoyin sjigon hanyar samun kudi ta wannan sana’a idan ba daukar ka akayi ba kayi waniu aiki a biyaka ba kamar masu kamfani suna samu ne ta hanyar saida caseete.

Wanda idan aka saida casette da yawa shine zai tare makudan kudade kamar dai yadda kasuwar film take a da kana iya ganin an saida dubunnan copies zuwa miliyoyi.

Yanayinta a Zamanance

A zamanin yanzu kwata- kwata ta canza yanayi da kuma kama kuma ana samu cigaba sosai ta fannin kayan aiki da kuma hanyoyin samun kudi duk da wata hanyar an tauyeta.

kayan daukar bidiyo

Idan zamuyi magana akan yanayin yadda ake samun kudi da ita ana iya daukar mutum ya yiyi bidiyo a biya shi ya tura format din ko kuma idan shi yake son ya samu nashi na kansa wanda zai dogara yana iya bude YouTube Channel dinsa.

Saboda a yanzu dalilin cigaban da duniya ta samu kota hanyar daura bidiyo a youtube ana samun kudi hanya ita ma mai zaman kanata kana iya duba bayanin da nayi akan samun kudi a youtube channel.

Karanta: Hanyoyi 5 da Ake Samun Kudi da su a YouTube

Yadda zaka fara

Abu nagaba kuma tunda munga matashiya akan yanayin wannan sana’a da kuma yadda zamani ya rinka canza mata yanayi daban daban daban a wannan fannin kuma zamuyi magana ne akan yadda zaka fara da kuma abubuwan da yakamat aka sani.

Amma kafin nan yana da kyau ka fahimta cewar ka zaba zakayi ne domin a ringa kiranka kana dauka ana biyanka kudi kokuma a kana so ne ka zama mai daukar bodiyo wanda yake son bude kamfaninsa ta hanyar daura bidiyoyi a soscial media ko kuma a youtube.

Wannan ya kamata ka natsu ka san ina zaka nufa ko kuma minene makasudin yin wannan sana’a, amma dai yanayin yadda ka zaba ga dai wasu daga cikin kayan aikin da kake da bukataarsu kamar haka.

Kayan aikin da kake Bukata

  • Video Camera
  • Casette
  • Editing software
  • Triport
  • Computer
  • Memory Card
  • Card Reader da sauransu

Bayan ka mallaki abubuwan dana zayyana a sama kamar ka kuma koyi yadda ake daukar bidiyo da kyau abu na gaba shine zabar sotwarea wadda zaka gyara Bidiypoyin da ke nada.

Karanta : Manhajar software da ya kamata ka zaba domin Kasuwanci

Domin duk bidiyon da ka kyara tafi kyau da kuma daukar ma yan kallo0 hankali do haka kana da bukatar iya gyaran video wanda ya kunshi sa rubutu, datsewa, sa hoyuna da sauran abubuwan da zasu fiddo bidiyon tayi kyau soasai

Karanta : Manhajar Software wadanda ya kamata ka koya domin dogaro da kai

Kammalawa

Kmar dai yadda nayi bayani wannan sana’a tana canzawa domin munga yadda rta sauya salo daga da zuwa yanzu don haka duk sana’aar da zakayi ka tabbata kana tafiya da zamani yadda ba sai wani zamnai yazo ba kaga an wuce ku samun kudi.

A nan zan tsaya idan kana da tambaya neman karin bayani ko kuma wani abun fada kana iya yinsa a kasa wajen comment section.

Karanta :

Bayani akan Bude Kamfani domin dogaro da kai

Blog da Abubuwan da ya Kunsa

Sana’ar Kiwo da Abubuwan da ta Kunsa

Ma’anar Sana’a da kuma Amfaninta