Skip to content
Home » Yadda Ganyen magarya Yake Gyaran jiki

Yadda Ganyen magarya Yake Gyaran jiki

Magarya dan icce ne wanda aka dade ana amfani da shi a duniya, kuma yana taimakawa sosai a fannin lafiyar dan Adam a wannan post din inshallahu zamu yi magana akan amfanin da ganyen magarya yake a wajen gyaran jiki.

Amma kafin nan bari mu fara magana akan micece magarya ya take kuma da yadda launin ganyenta yake daga nana sai mu tafi akan amfanin da yake a jikin dan adam.

Gyaran jiki da ganyan magarya

Micce magarya?

Magarya wani dan icce ne karami mai dadai wanda ake tsotsar sa kuma yana da kwallo a cikin sa wanda mafi akasari tafi yin yayan ta a lokacin bazara wato bayan damina ta wuce.

Tana da kayoyi zagaye da iccen ta kuma tana da ganyaye tsanwaye ganan wanda suke fitowa a jikinta wanda sune zamuyi bayanin amfanin su da rawar da yake takawa a lafiyar dan adam da kuma rayuwarsa.

Amfani da yake a Jiki

Ga wasu daga cikin munhimman amfanunnukan da yake a jiki tare da bayani akan yadda ake sarrafa shi domin yin hakan.

kara kibar Jiki

Yana sa jikin mutum yayi giba musamman ida ana hada shi da zuma ana sha ana kuma cin abinci mai gina jiki, idan ana yinhakan cikin ikon Allah zaka ga jikin mutum yayi kyau kuma mutumin yana kara kiba da haske.

Yadda zaa hada shi shine samu busasshen gyanyen sai a ruka sha da zummuwa bayan anci abinci koda sau biyu ne a rana.

Karanta : Gyaran Gashi: Yadda ake wanke gashi da lalle ga mata

Kauda daudar jiki

Yana gyaran jiki tare da kauda duk wata dauda wadda take a cikin jikin mutum cikin ikon Allah indai ana amfani da shi.

Yandda ake amfani da shi shine za’a sa shi a cikin ruwa sai a goga a fatar ko kuma inda ake son a wanke sai a shafa shi a fatar jikin kafin ayi wanka da wajen wanka sai a wanke shi.

Amfanin hakan inshallahu zai kauda daudar jiki tare da wasu yan kurajen da suke dan addabar mutum da izinin Allah.

Karanta : Tsawon Gashi: Abubuwa guda 5 dake sa tsawon gashi

Magance Gyambon ciki

Ga masu fama da ciwpn ulcer musamman wadda tayi yawa yana cikin ikon Allah idan suna amfani da ganyen magarya suna samun sauki koma su rabu da ita gabakidaya musamman irin wadanda ko azumi basu iyawa.

Yadda ake amfani da ita shine ana hada shayin ganyen magarya ne da kuma yayan habbatus sauda ana sha to ana samun sauki soi a cikin yadda Allah.

Karanta : Maganin Ulcer da tayi Yawa(chronic) har abada