Skip to content
Home » Bayani akan karanta Qur’ani mai Girma da kyau domin samun lada

Bayani akan karanta Qur’ani mai Girma da kyau domin samun lada

Qur’ani yana daya daga cikin litattafan da Allah madaukakin sarki ya saukar ga Annabi muhammad (S.A.W) zuwa ga mutane baki daya a cikin shekara 23.

Wanda littafi ne da ya sha bamban da sauran litattafai karanta shi ma ana samun lada a wurin allah madaukakin sarki idan ka karanta shi yadda aka ce a karan ta shi.

Qur'an

Hanyoyin da ya dace a karanta Qur’ani

A wannan rubutun zanyi bayani akan matakai da kuma hanyoyin da ake karanta sh domin samun cikakkiyar lada a Wurin Allah.

Karanta shi domin Allah

Abu na farko da ya kamata ka saka a ckn ranka a duk lokacin da kayi niyyar karanta littafin Allah Al’qur’ani shine ka karanta shi da niyyar ka samu lada a wurin Allah madaukakin sarki.

Ba da nyyar samun wani abu na duniya ba, a wasu lokuttan kana iya fara karantawa sai shaidan ya bijiro maka da riya wato yi ba don Allah ba.

To a nan sa ka dage ka kori shaidan ka kyara zuciyarka ka manta da wancen tunann na gaba kar ka bari ya cigaba da rudar ka akan kayi ba don Allah ba

Domin yin hakan yana sa kata shi babu komai amadadn ka samu lada sa abun ya koma zuwa ga zunub Allah ya tsare mu

karanta: Yadda ake Hardace Qurani

Karanta sh da kyautatawa

Abu na gaba kuma shine karanta Al Qur’ani da kyautatwa wato ana nufin bashi hakokin sa na hukunce hukunce.

A wannan fannanin akwai bukatar ka samu ilimin tajweedi domin shne yake koya yadda ake karanta littafin Allah mai tsarki ta hanyar ba kowane harafi hakkinsa.

Domin a ciikin harrufa akwa na bayyaanawa, shigarwa, boyewa da kuma canzawa da kuma wadanda su jansu a ke yi to duk wadannan suna daga ckin abubuwan da ya kamata ma karanta littafin Allah ya kiyaye.

Domin shi wannan ilimin na tajweedi ba dole ne kowa ya neme shi ba ya iya amma kuma aiki da shi ko shakka babu dole ne kaga to dole ne a iya karanta quran da tajeedi.

Wanda rashin yin hakan ya ja ka riga canza ma’anar kalma wanda ba haka aka so ba.

karanta: Abubuwan da ke taimakawa wajen zaman Hardar Qur’ani

Karanta shi da Kushu’i

Abu na gaba kuma shine a lokacin da mai karatu yake karanta littafin Allah ana son ya rinka hararo ma’anar abunda yake karantawa.

Ba kawai ace kana karatu ba amma kwata kwata hankalinka baya wurin yana wani wuri na daban ana so ka maida hankalinka gaba daya a wurin.

Hakan yana taimakawa wajen samun cikakkiyar lada da kuma fatan samun rahama daga wurin Allah madaukakin sarki.