Skip to content
Home » Sana’ar Rubutun Littafi da Bayani akan Marubuta

Sana’ar Rubutun Littafi da Bayani akan Marubuta

Ruutun littafi yana da matukar amfani sosai a ce kana/kina da wani littafi wanda ka wallafa shin nalittafin hausa ne ko kuma kuma na wani yare dabam, kuma sana’ace wadda marubuta suke daukar ta wadda har skan iya dogara da kansu ta hanyarta kwarai da gaske.

To a cikin wannan post din na yau zamuyi dubi akan yadda zaka cimma burinka na rubuta littafi da kuma amfanin da hakan yake da shi sosai.

Rubutun littafi

Muhimman Abubuwan akan Rubutun Littafi

Littafi yana daya daga daga cikin muhimman abu ko kuma ince jigo wanda musamman dalibai suke tunkaho da shi kuma kuma yake da matukar amfani a garesu.

Kai bama kawai ga dalibai ba littafi shine jigon da ya ba,mbambanta tsakanin jahili da kuma mai ilimi ta kowace fuska a rayuwar dan Adan.

Masu yawan katranta littafi sun fi kima a idon mutane saboda ilimin da suke kwasa su kuma masu rubuta lkittafi sun zarce su saboda su suka yi bincike suka rubuta litattafan da ake karantawa.

Ka rubuta litafi koda daya ne a rayuwar ka yafi babu saboda abu ne mai matukar amfani koda ba don ka samu kudi ba balle idan kayi abunda ya dace ma har kudin sai ka samu.

Yadda zaka fara Rubutawa

Mfi yawancin mutane suna ganin gamar rubuta littafi abu ne wanda ba zasu iya shi ba su rubuta shafi da yawa tsammanin su shine marubutan littafi a lokaci daya suke rubuta shi wanda ba haka abun yake ba kwata-kwata.

kaima zaka iya rubuta naka ay da kadan ake farawa zuwa da yawa ga kuma wasu muhimman matakan da za ka bi wanda zasu taimaka maka wajen rubuta littafinka.

karanta: Manhajoji masu amfani ga masu rubutun littafi kamar Hausa Novel

Tsarin Rubutawa

Da farko zaka tsara yadda zaka rinka rubuta littafinka misali kullun zakayi shafi daya ko fiye dxa hakan burinka dai shine kana so a ce nan da wata 3 misali kasa da haka ko kuma sama da hakan ka gama.

Ya danganta ga yadda zaka iya rubutawa koda shafi daya ne duk kullun ba matsala kuma kar ka samu damuwa kaga wani wajen bai yimaka ba kana iya gogewa ka kara ko kuma ka rage abunda kake so.

Yana da kyau ka sani cewar ko suma manyan marubutan littafi suna yin hakan su kyara inda keda kyara ko kuma su rage ko kuma kari ya danganta ga yadda halin ya kasance.

Bincike akan Fannin Rubutunka

Abu mai mahimmanci wanda yake daga cikinmatakan da marubuta suke bi shine yawan bincike da kuma karanta litattafai masu alaka da da wanda suke rubutawa.

Hakan na da matukar amafani kuma yanaa taimakawa sposai saboda ta hanyar hakan hakan ne zaka ga basira da hikimar da wancen marubucin yayi amfani da ita ka sa a cikin naka.

Kuma baya ga hakan zaka kara samun ilimi sabaoda yana da kyau ka sani cewar kafin kayi rubutu akan wani abu cikin littafi ka tabbatar ka sana abun abun saboda wadanda zasu karanta bayan ka kammala littafinka suna iya fahimtar idan kana da kwarewa  akan abunda ka rubuta a littafinka ko kuma babu.

Binceke akan Rubutun Littafi

Idan kana son ka zama kwararre a fannin rubutun litattatafai to yana da kyau ka rika ywaita bincike akan marubuta da yadda suke rubutunsu.

Tare da gano hanyoyin zamani da kuma kayan aiki na zamani da zasu taimaka maka wajen rubunka saboda kamar yadda yadda na fadi a fannin sana’aoi shi bincike yana da amfani a koda yaushe.

Domin ta hanyar bincike ne zaka fahimnci cerwar ga wani sabon abun ya zo ya zaka tafi da shi dai dai da zamanbi yadda zaka samu karbuwa a wurin jama’a sosai yadda ya dace.