Skip to content
Home » Sana’ar Kiwon Kaji da yadda ake samun kudi da ita

Sana’ar Kiwon Kaji da yadda ake samun kudi da ita

Kiwon kaji yana daya daga cikin muhimman sana’oin da aka dade ana yinsu wanda ana samun kudi sosai ta hanyar su musamman yadda zamani ya sauya yanayinta daga dadewa ana kiwo zuwa yan kananun satuka ko watannani.

Amma Dudda kasancewar ta hanya samun kudi bata tsaya a nan a ce kawai cikin sauaki, a’a kafin ka fara akwai wasu muhimman abubuwan da ya kamata ka tsaya ka duba kuma kayi tunanin tun daga yanayin kajin da zaka sa.

Wannan a matakin kasuwa kenen baccin abubuwan kula da ya kamta su biyo baya yadda zasu kasance masu lafiya a koda yaushe.

kiwon kaji

Ya kiwon kaji ya canza

A zamanin da kamar yadda aka sani muna da kaji wadanda muke ceme yan hausa su samfuri ne na kajin da muna su a nan gida wadda zaka ga kaza ta dade bata girma ba kana iya ganin kafin a ce an cita sai bayan kamara wata shidda ko fiye da haka.

Amma cikin ikon Allah sanadiyyar cigaban zamani da aka samu na ilimi a fannanin noma abubuwan sun suya ta yadda duk wata kana iya saida kaza to kaga a wannan fuska abun ya koma kasunci zannanne kenen.

Kuma ana iya yinbshi a samu riba da wuri fiye da na baya na da kenensaboda canzawar yanayin lokaci da kuma yanayin girma, ka sa sun girma sosi cikin karamin lokaci.

Nau’in kajin zamani

Kajin zamani wanda aka fi samun kudi da su sun rabu ne zuwa gida biyu kamar haka wanda ya danganta ga yadda ka shiga kasuwar da kuma wanda kake bukatar yi:

 • Na Nama (Broilers)
 • Na kwai (Layers)

Karanta: Sana’oin Gargajiya: Manyan Sanaoin Gargajiya na Kasar Hausa wanda Hausawa Ke yi

Na Nama (Broilers)

Idan mukayi magana akan Broilers wato wasu naui na kajin turawa wanda ake kiwata su domin samar da nama kawai.

Zaka zuba su domin su girma cikin wanda bayan sati hudu ma kawai kana iya kwashe kayanka ka kai kasuwa ka saida saboda suna da saurin girma sosai.

Suna riba sosai amma kuma yana da kyau ka kula da abubuwa sosai a lokacin da kakre kiwata irn wadannan kajin saboda suna saurin mutuwa idan ba’ayi taka tsantsan ba.

Ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da ya kamata ka kula da su idan a lokacin da kake kiwon irin wadannan kajin saboda suna daga cikin nauin kajin zamani da ke da saurin mutawa musamman idan ba cikakkiyar kulawa.

Muhimman Abubuwan Kulawa

 • Yanayi ba ma zafi sosai ba ba kuma sanyi kwarai ba
 • Ba su allurai tun suna kanan
 • Kula da tsafta ce su
 • Basu abincin su zallah batare da hadi ba
 • Yawan kiwo na safe rana da kuma dare

Na kwai (Layers)

Kajin kwai ma abun dubawa ne sosai kuma ana samun kudi da su sosai idan ka san yadda zaka shiga kasuwan saboda su idan har suka fara maka kwai to kaka kusan kana maida kudin abincinsi da suke ci.

Kuma bugu da kari ga nama wanda bayan sun gama zaka saida su baccin taki wanda daman abu ne mai tsada.

Su suna da bambanci da na sama saboda ana yinsu ne domin a saida kwai kuma suna dan dadewa kafin su fara kwai.

Duka yanayin rayuwarsu kusan wata hudu ne amma zaka yi ta basu abinci har kusan wata biyu kafin su fara yimaka kwai.

Bayan sun yi kusan kullun kana yi samun kwai daya koma biya akan kowace kaza ya danganta ga yanayinsu.

Muhimman Abubuwan Kulawa

 • Yanayi ba ma zafi sosai ba ba kuma sanyi kwarai ba
 • Ba su allurai tun suna kanan
 • Kula da tsafta ce su
 • Dauke kwai bayan sun fara kafin su snaye shi
 • Basu abincin su zallah batare da hadi ba
 • Yawan kiwo na safe rana da kuma dare

Karanta: Sana’ar Kiwo da Abubuwan da ta Kunsa

Yadda zaka fara

fara kiwon kaza

Kafin ka shiga a cikin wannan sana’a yana da kyau ka tsaya kayi tunani ka duba kaga yanayin shin kana da wurin da zakayi ta da kuma kudin abincinsu da na kuma kula da lafiyarsu.

Bayan ka ga kana iyawa to sai ka shiga kana iya farawa kadan 25 ko kuma hamsin tunda a farko ne.

Kuma ga abubuwan da zaka kula da su kafin zubawa

Na’in Jarinka da Kasuwar

Da farko zaka tsaya kayi tunani shin kiwon da zaka yi domin ka samu nama ne ko kuma domin ka samu kwai ka saida ne kuma ya yanayin jarin da kake da shi.

Saboda kamar yadda na bambance tsakanin masu kwai da kuma na nama suna da bambanci ko a wajen kashe kudi wanda zaka zuba.

Karanta: Ma’anar Sana’a da kuma Amfaninta

Misalai idan kana da karamin jari kaga kuma ga yanayin bukukuwa kamar na sallah ya taho to kaga na nama ya dace kayi saboda yadda zaka saida da sauri ka samu riba.

Idan Kuma misali kana da kudi kaji zaka iya daure ma sayen dussa na dsan lokaci mai tsawo kuma kamar irin kafin azumi da yan watanni kana iya sa na kwai yadda da ka kiwata ka samu kwai kuma bayan ka sun gama ko kuma sallah ta taho ka saida naman.

Yanayi

Su kaji ba wai kawai hakanan musamman kana dan koyo zaka zuba sun ba suna kanana akwai dan okacin da ya kamat ka gujemawa musamman idan yanayin wurin da zaka zaka yi su ba wani mai girma da ingantawa bane.

Abunda ya kamata ka fahimta a nan shine ba su son yawan zafi sosai kumar yadda shima sanyi yake yawan illata su.

Wannan inamagana ne musamman a yanayin da suke kananu kafin su girma domin misali koma a ce sun girma idan ana sanyi sosai sai ka ruka rufe daki ko kuma kejion da suke inba haka ba suna iya mutuwa.

Haka ma yake a lokacin zafi dole ya kasance akwai tazara da kuma walwala a inda suke yadda iska yana kaimasu sosai domin yawan zafin shima yana kashe su.

Yanayin da zaka saida

A kowane irin kasuwanci akawai bukatar ka san wanenen customer dinka wanda zaka saida ma hajarka.

A fannin kiwo ma haka wani lokaci zaka ga kila wani mai gidan abinci ko kuma hotel ne zai rika kwashe ma abunda ka kiwata.

Ko kuma kila mutane zasu sani ka rika saida masu daidai daya dalilin sanin hakan shine kasani yadda yanayin idan lokacin cikar girmansu yayi ka kara ko kuma kar ka ida kaiwa.

Wannan yafi alak ne musamman ga kajin nama sune zaka ga wasu har suna wuce sati hudu kaga suna da bambanci dana sati hudu a yanayin girma nesa ma kawa ba kusa ba ba za’a hada su ba.