You are currently viewing Sana’ar POS da yadda ake yinta

Sana’ar POS da yadda ake yinta

POS ga zaka ga ya cika ko ina a yanzju kusan saboda tana daya daga cikin sanaoin da  mutane suna yawan b ukatar su saboda abu ce wadda ta shafi cinikayya ta kudi, a yau inshallahu zamu yi bayai akan yadda zaka fara wannan sana’a ta pos da kuma abubuwan da kake bukatar fahimta na kayan aiki da kuma mallaka.

sanar pos

Ya sana’ar POS take?

ita dai wannan sana’a ana yinta a yanayin yadda customer zai zo wajenka domin ya samu saukin cire kudinshi na ajiya a banki.

Ba yada bukatar sai ya tafi banki ya bi layi ko domin ya zuba kudi a cikin asusun bankin sa ko kum a ya cire saboda haka ne ake neman masu irin wannan sana’a.

kuma wannan shine abun kula a wannan sana’a ka tabbata idan ka fara ta zaka iya badawa kudi a cikin sauri ga wanda yazo kuma kana da da kudi availabe masu dan yawa wanda ake juyawa.

saboda zakaga idan mutane suka fahimci kullun suka zo a wajenka suna samun kudi kuma kana yin abun yadda ya kamata zaka ga yawan zo maka domin yin transaction.

To bayan haka kuma akwai wasu muhimman abubuwa da ya kamata ka mallaka kafin ka fara ta ga su kuma zan lissafa maka su kamar haka.

karanta:

Yadda zaka fara Sana’ar Saida Data

Sana’ar Kiwon Kaji da yadda ake samun kudi da ita

Abubuwan da kake bukata kafin fara ta

 • Shago ko wuri mai kyau
 • POS machine
 • Jari daga 50000 abunda yayi sama
 • Asusun baki

wadannan abubuwan sune muhimman wadanda kake bukatar ya kasance ka same su daga nan kuma sai mu tafi akan yadda zaka fara ita kanta sana’ar.

Yadda ake farawa

A karon farko dai abu mai mahimmaci shine zaka je bankin da kake sha’awar fara wannan hudda ta pos da su kayi masu bayani su bude maka asusun fara wannan kasuwanci wanda ya kunshi yadda zaku raba ribar duk transactiuon.

ya dai danganta da kamasho ko kuma kashin da suke dauka a wannan bankin wasu suce kai 40 su 60 wasu kuma suce 60 kai 40 da sauransu kamar yadda nace dai ya danganta

Muhimman abubuawan da banki ke bukata

wadannan suna daga cikin muhimman abubuawan da sai kana da su bankin zasu iya amsarka kafin ka fara wannan huddar kasuwancin da su.

 • National Id card, driver lisence ko kuma International passport
 • BVN
 • kudin farawa karanci 50,000

Wadannan abubuwan da na zayyana  a sama da ma wasu saura duk kana da bukatar ka mallake su hadi da kuma wasu ma wadanda ban ambata maka a nan ba.

Hanyoyin samu a kasuwancin

Bayan ka mallaki injin aikin wato POS machine abu kuma na gaba shine zaka iya yin wadannnan abubuwan kamara haka

 • Sa kudi
 • Turawa
 • Cirewa
 • Biyan Bills da ma sauran makamantan su

 

Yadda zaka samu riba

Masu sana’ar nan ta Pos yawaita transaction yana kawo masu riba sosai tunda idan ka dage kana iya ganin kana tashi da riba tas fiye da dubu ukku a kullun indai kana da jama’a

kuma matakan da zaka bi shine ka rika fitowa da wuri abu na farko kenen saboda da safe mutane da yawa na nemen masu pos uma yawancinsu bsu sfko ds wuri.

Sai kuma yawan samun kudi idan customer yazo wannan ma yana taimakawa sosai suji dadi suna dawo kullun saboda sun san zasu samu kudi a tare da kai yadda suke son su cire.

sai kuma saukin charges ma yana taimakwa ka kasance mai sauki ko yayay ne bama a wannan kasuwanci ba a kowane rage yanayin charges ko kuma ince sauki yana taimakawa wajen samun customers da yawa sosai.