Zuma wani abun sha ne wanda aka dade ana amfani da shi a fadin duniya, musamman ma ga musulmai sun san cewa har a cikin Al Qura’ni Allah ya ambace ta a matsayin abun da yake waeraka ga mutane.
A cikin wannan post din inshallahu zamu yi duba ga zuwa wasu magigunguna ko kuma amfanunnuaka goma da take yi a cikin jikin dan adan.
Table of Contents
Micece Zuma
kafin nan dai Zuma abun sha ne wanda take fitowa daga cikin wani kwaro wan da ake kirans a da kudan zuma, a yanayi tana da zaki a cikin wasu abubuwa take kamar container wanda ake kira da saka.
To a wajen wadanda ke tace ta an raba ta zuwa gida biyu akwai farar saka wadda zaka ganata fara akwai kuma bakar saka mai launin duhu daga kalar ta ta rywan kasa.
Sai dai dudda magungunan nan da take yana da kyau mai karatu a kula idan ka tashi neman ta ka nemi tatta mai kyau wadda ba’a yimata hadi ba.
Saboda wasu masu saidawa suna yimata hadi da sugar ko kuma wasu ma suyi hadi da kwaro to wannan shima abun lura ne saboda an cakude ta da wani abu na daban.
Magungunan da take yi
Zuma har masannan sun tabbatar da cewa tana yin magunguna da dama a cikin jikin dana adam wanda a kullun bincike ake kara yi akanta amma ga wasu daga cikin muhimman da aka fi saninsu a fadin duniya.
Maganin Ciwon Ciki
Gamasu fama da ciwon ciki suna bukatar su rika yawan shan zuma musamman a lokacin da abun ya motsa masu saboda tana taimakawa sosai wajen kawar da datti ko kuma wata dauda dake a cikin cikin mutum.
Maganin Ciwo ko Rauni
A fannin rayni zuma na taka muhimmiyar raw sosai saboda idan ana asama rauni kusan idan ya warke wani lokacinma ko tabo baya yi sosai kamar wanda ba’a sama masa ita ba.
Kuma bugu da kari tana taimakawa sosai a wajen saurin warkar da raunin ya kame ba tare da an dade ana yin doguwar jinyar sa ba saboda tun yana karami ba tana kashi bacteriyoyi da wasu fungi dake neman addabar sa.
Sa hasken Fata da Fuska
Ga masu son maganin hasken fuka ko kuma maganin hasken fata ba tare da an yi bleaching ba to su rike zuma tabbas sun samu mafita inshallahu.
Saboda tana kashe kwayoyin cuta na saman fuska ko fata ta sa fatar tayi kyalli ytayi sulbi kwanin kyau idan ana sawa ana bari zuwa wasu yan mintuna sai a wanke to duka wasu yan kurajen fuska ko kuma fata zasu mutu da izinin Allah.
Maganin Rage kiba
Ga masu son kibar su ta daidaita bayan tayi yawa tana daya daga cikin abubuwan da ke taimakawa wajen rage yawan kitse a cikin jikin mutum kuma mutum tya kula da yawan cin abubuwan da ke sa saurin kiba.
Karanta: Hanyoyi 10 Domin Karin Kiba a Jikin Mutum
Kara Karfin Garkuwar Jiki
Tana taimakwa sosai wqajen kara karfin garkuwar jikin Dan adam saboda sinadaran da take da su wanda suke maganin bacteria da kuma kara karfin cells a cikin jikin mutum.
Maganin Karatu / Kara Karfin kwakwalwa
Yawan shan zuma yana taimakawa wajen kara kaifin kwakwalwa da kuma kara karfin memory dom in a ro=ike karatu da wuri, da kuma taimakawa wajen magance yawan kasalar jiki.
Taimakawa Gum Na Hakora
Tana kara karfin Gum na hakora wanda sune suke rike da hakori a cikin bakin mutum, bugu da kara tana taimakwa wajen magance kwayoyin cuta da ke neman kama hakokar ko kuma suke takurama hakora.
Maganin Dandrup
Tana ytaimakawa wajen magancedandrop na gashi bama a wannan kawai ta tsaya ba shi kanshi gashin tana taimaka masa wajen sa shi yayi laushi sulbi da kuma gyalli.
Mata masu son maganin tsawon gashi da kuma sulbi ko gyallin gashi su rika sama kansu zuma kafin shamfoo yadda ake yi shine za’a sa karamin cokali 2 sai a sa mai a motsa gashin a barshi tsawon minti 15 daga nan sai a wanke a sa shampoo, hakan yana sa sulbi da kyawon kashi ga shi ya magance cuttukan da ke tattare da shi.
Karanta:
Gyaran Gashi: Yadda ake wanke gashi da lalle ga mata
Tsawon Gashi: Abubuwa guda 5 dake sa tsawon gashi
Taimakawa Wajen samun Bacci
Zuma tana taimakwa sosai wajen samun isashen bacci ga wadanda suka gaza yin bacci su sha ta bayan mintuna insahallahu zasu samu damar yin bacci mai dadi.
Maganin Tari
Ko shakka babu tana taimakawa w ajen magance tari ko kuma mura, ta ta fara kamaka ka dauki cokaci karika sha na zuma koda sau biyu ne da safe da kuma yamma inshallahu za’a warke daga tarin.
Karanta:
Maganin Tari da Mura da sanyin Maza da Mata
Maganin Fitsarin Kwance ga Manya da Yara
Author Profile

Latest entries
Kimiyya da FasahaSeptember 22, 2023Wuraren da Zaka Samu Kayan Kere-Keren da Kake Bukata
Wayar HannuJuly 17, 2023Yadda Ake Amfani da WPS Software
Wayar HannuJuly 4, 2023Yadda Zaka Zama Dillalin Yanar Gizo
Wayar HannuJuly 3, 2023Yadda Ake Samun Aiki Online ta Hanyar Linkedin