Skip to content
Home » Azumin Watan Ramadan da Abubuwan da Ya kunsa

Azumin Watan Ramadan da Abubuwan da Ya kunsa

watan Ramadan wata ne mai alfarma wanda aka safkar da Al Qurani a cikins wanda kuma muslmai a fadin duniya suke azumtar shi gabakidaya tsawon kwana ashirin da tara ko kuma idan ba’a ganshi ba a cika na talatin.

Azumin Watan Ramadan

Abubuwan da Ramadan Ya kunsa

A cikin wata mai alfarma na ramadan wanda shine wata na tara a cikin watannin musulnci da muke da su ya kunshi abubuwa da dama amma muhimmiyar ibada wadda ta shahara a cikin watan ita ce ta azumtar shi wato kamewa.

Wajibi ne ga kowane musulmi na miji ko kuma musulma mace  baligi kuma mai hanakali ana son ya  kame daga ci, sha saduwa da kuma a cikin wannan watan har saai rana ta fadi.

A cikin shi kuma ana son dukkan musulmi ya kauracema aikata laifuffuka da yake ya tuba zuwa ga Allah madaukakin sarki tare da yawaita abubuwan alkhairi wanna zasu kusantar da shi zuwa ga mahaliccinsa.

A cikin Kwanakin Gomkan Karshe na watan akwai darare masu albarka wanda a nan a ke sa ran samun daren lailatul qadari musamman a cikin kwanakin mara 21, 25, 27, da kuma 29. ana son a dage damstse soisai saboda ibadar wannan wuni kadai yafi ta dare dubu wanda kusan shgekara tamanin kenan

Tambayoyi da amsa

A wannan sashen zamu duba akan wasu muhimman abub uwa da ya shafi azumi ko kuama ramuwar azum.

Shin Ya zabn ranma azumi banda lafiya?

Ga wanda Allah ya  jarabta da ciwo ko kuma jinya yana iya aje azumi ya ci abinci bayan watan idan ya samu sauki to yana sai ya tabbatar da ya rama azumin da ake binsa kafin wani watan ya kara zuwa.

Misalki masu ciwon Ulcer idan suka ce zasu yi azumi dole suna iya tagayyara to akwai rangwame su aje sun rama.

Ina shayarwa ya zanyi?

Ga Wadda take shayarwa kuma tana gudun kada danta ya tagayyara itama tana iya ajewa bayan lokacin sai ta rama saboda gudun kar danta ya shiga wani hali.