Kiba tana tana da matukar amfani a jikin dan adam wanda shiyasa musamman mata suke neman mi ke sa kiba ko tayaya zasu kara kiba a cikin karamin lokaci, to a cikin wannan post zamu yi bayani akan wasu hanyoyi masu ssaurin sawa.
Table of Contents
Micece Kiba kuma mi ta Kunsa?
Kiba ko kuma a ce cukowa a girman jiki tana da amfani amma idan tayi yawa tana zama matsala a jikin dan Adam wanda wani lokacin zakaga wasu na sha’awar hanyoyin da zasu bi domin rage ta.
Saboda kitshe da kuma yawan calories da ke a cikin jikin mutum wanda hakan yana saurin haifar da cututtuka a cikin jiki kamar irinsu diebeties.
Yin kiba ya kasu biyu akwai mai lafiya akwai kuma marar lafiya wadda ake cema obesity ita tayi yawa amma kiba mai lafiya ita bata da wata matsala kuma jiki yana iya yin aikace aikacen sa a cikin sauki.
Kamar yadda bincike ya nuna mata sun linka maza a fannin kiba a yawancin kasashen da suka cigaba, a irin kasashe masu tasowa kamar Nigeria ma kusan linkin yafi ukku saboda yadda suke, ga basu cika motsa jikinsu ba.
Karanta:
YADDA AKE GIRKI COMPLETE SANWA YADDA ZANI GIRKA ABINCI KALA KALA
Girki Adon Mace: Kala-kalar Girki da yadda zaki kware akan kirki don shine adon mata
Hanyoyin Karinta
Idan mukayi magana akan hanyoyin da ke kara ta ko kuma suke sa kiba ya danganta akwai na cin abinci akwai kuma wadanda dabi’u ne za’a a rika yinsa domin a cimma guri.
Kuma dama abunda ake so shine ya kasance calories dinda ake konawa a jikin mutum an samu wadanda suka fi su yawa to ta hakan ake samuta kada ya kasance konawar tafi samuwar yawa.
Amma ga wasu wadannad bincike ya nuna suna taimakawa sosai a wajen karinta a cikin jikin dana adam kamara haka.
Cin Abu Mai Gina jiki(Proteins)
Yawan Cin abubuwan da suke kunshe da proteins wato sinadaran amino acid yana taimakawa sosai wajen habbaka jiki da sa shi girma da wuri.
Irin wadannan na’uin abincin sun hada da nama, madara, kifi wake, waken suya da sauransu wanda idan ka lura yawancinsu da ka cisu zakaga cikin ka ya yi nauyi bakamar sauran abinci ba.
Su irin wadannan na’uin abincin ba wai kawai girma suke saurin karawa ba a’a harma da kara sa lafiya jiki da ciko da wasu cells a cikin jikin dan adam.
Abincin kasa
Abincin da ke tohowa daga kasa yawancinsu starch ne wanda suna taimakawa kwarai da gaske a fannin kara girman jikin mutum da lafiyarsa.
Irin na’uukan wannan abincin sun hada da su rogo, doya dankali da sauransu duka ana son wanda ke son ya kara girman jiki ya rika yawan cinsu akai akai yadda a fannin starch yana da wadataccens kuma suna saurin kara yawan calories a cikin jikin mutum.
Abincin Da ya shafi fannin gyada
Abubuwan da suka shafi gyada suna taimakawa sosai wajin gina jikin mutum. kuma ko mu nan a hausance ana yin abubuwa da yawa da gyada.
Kamar yaita ci da shan irinsu kuli, kunun gyada, Miyar gyada tunkuza da sauran abubuwan da ya kasance gyada ce aka sarrafa ta ta hada su suna taimakawa kwarai da gaske.
Madara
Madara babban abu ce wajen sa girman jiki kuma tana kunshe da sinadarin amino acid mai yawa ita kusan tana daga cikin abunda da wuri take sa kiba.
Duk wasu abubuwan da suka shafe ta yawaita shansu ko cinsa yana sa jiki girma da wuri kuma tanakara lafiya kyalli da kuma laushe na jikn mutum.
Isasshen Bacci
isasshen bacci nada matukar amfani a wannan fannin yana da kyau a kullun ga kowane baligi yayi bacci karancinsa na awa shidda yadda ake so ma shine a samu awa 8.
Samun isashen bacci yana kauda damuwa daga jikin mutum da kwantar mashi da hankali wanda yana daya daga cikin abubuwan da suka wajaba ga mai son kiba ya kasance hankalinsa a kwance yake.
Karanta:
Maganin Ulcer: Yadda zaka magance gyanbon ciki ulcer Babba da karama
Motsa jiki Madaidaici
Motsa hiki na taim akawa wajen gyara tsokar jiki da kuma kara karfi a jijiyoyin dan adam, wanda idan ba’a , motsa jiki yana sa kibar ta kasance marar lafiya saboda calories sun yi yawa sosai a cikin jikin sai suyi ta komawa kitse.
Ana son kitse a jikin mutum amma ba amai yawa ba sosai madaidaici saboda haka a rinka motsa jiki maidaidaici ba mai yawan da za’a rika kona calories ba sai a dawo rama.
Yawan Cin Abinci
Muhimmin abunda yake gaba a wannan maudu’i da muke magana shine daman yawan cin abinci wanda yake ci kadan ba’a hada shi da mai ci dayawa.
Inadai ana son saurin cimma guri to a rika cin babban kwano na abiunci mai gina jiki da sa lafiya a cikin jikin mutum tare da kaucema tasin hankali a lokacin cin ko bayan hakan.
Abinci Mai sa Karfi
Na’uin abinci masu dsa karfi kafin su masatra gero dawa da sauransu na taimakawa sosai wajen habbaka girmana jiki.
Saboda suna da saurin haifar da calories a cikin jikin fdan adam wanda suna kara taimakawa wajen lafiya da kuma karin karin jikin.
Kulawa da Cin Duka sinadaran Abinci
Abu mai mahimmaci kuma na gaba shine a rika kulawa da cin duka da’uikan abincin da a ke da su wanada a turance a ke kiransa da suna balance diet.#
Shi yadda yake shine ya kasance a kwanon abincin ka an samu amasu gina jiki kamar nama, abincin kasa kamar dankali, masu sa karfi kamar shinkafa, ganyaye da kayan marmari.
hakan to ka tattara dukan abunda jiki yake bukata a wanda hakan yana taimakawa sosai shima
Kaucema Shaye Shaye
Gaz duk wqanda yake son kiba to dole ne fa sai ya kauceme ashaye saheyen giya taba danma sauransu saboda suna lalata jiki gabadaya.
Da kuma tauye wasu sinadarai tare da kawar da hanakali a cikin jikin dan adam.
Karanta:
Maganin Tari da Mura da sanyin Maza da Mata
Maganin Fitsarin Kwance ga Manya da Yara
Maganin Ulcer da tayi Yawa(chronic) har abada
Author Profile

Latest entries
Kimiyya da FasahaSeptember 22, 2023Wuraren da Zaka Samu Kayan Kere-Keren da Kake Bukata
Wayar HannuJuly 17, 2023Yadda Ake Amfani da WPS Software
Wayar HannuJuly 4, 2023Yadda Zaka Zama Dillalin Yanar Gizo
Wayar HannuJuly 3, 2023Yadda Ake Samun Aiki Online ta Hanyar Linkedin