You are currently viewing Amafanin Motsa JIki a jikin Dan Adam

Amafanin Motsa JIki a jikin Dan Adam

Motsa jiki yana da matukar amfani ga lafiyar maza da mata musamman a irn wannan zamanin da muke ciki na abuybuwa kala daban daban da kuma naukan ayyuka wanda ba’a cika yawaita aiki ba.

Masu kiwon lafiya suna cewa motsa jiki yinsa ko yaya ne yafi rashin yinsa saboda koda a ce minti 30 ne kullun mutum yake yi ko awa yafi ace baya yi kuma koda ace yana fama da cututtuka irinsu hawan jini, ciwon sugar, gawut dadai sauransu yana taimakaewa wajen inganta lafiyarsa.

Motsa JIki

Abubuwan da Motsa jiki ya kunsa

Idan mukayi magana akan motsa jiki mutrane da dama suna daukar shi a matsayin abu na wasa kawai ba tare da la’a kari da amfanin da kuma yake kara haifar ma mutum ba wajen inganta lafityarsa.

ya kunshi dukkan wasu abubauwan da zai rinka canzawa ko kuma ince motsa sassa nko kuma gabobi dake a cikin jikin dan adan wanda hakan yake taimakawa wajen zagayawar jini a jijiyoyi  cikin sauki.

karanta:

Hanyoyi 10 Domin Karin Kiba a Jikin Mutum

Hanyoyin da ake bi Domin Rage Kiba

Abubuwan da ya kunsa sun hada da Gudu, tsalle- tsalle, kai harma da tafiya wadda ake rainawa tana daga cikin na’uin motsa jiki wanda suke inganta lafiyar a cikin jikin mutum.

Saboda idan kana yana yawan tafiya lafiyarka tafi bisa ga ace baka yawan yi kuma wannan ma ne dalilin da yasa yan kasar waje musamman ma a kasashen da suka cigaba suke yawan yin tafiya a kafa bisa ga abun hawa kamar ,mu nan sun rage kudin kashewa kuma lafiyar su ta kara inganta.

Karanta:

Hanyoyin da ake bi Domin Rage Kiba

 

Amfaninsa ga Lafiyar Jiki

kamara yadda na ambata a baya yana taim akawa sosai wajen inganta lafiyar jiki to ga wasu muhimman abubuwa da ya kamata ka sani akan haka.

  • Magance Hawan Jini
  • Maganace Ciwon Sugar
  • Kara karfin Kwakwalwa
  • Rage yawan kasala
  • rage yawan damuwa
  • Kara karfin kashi
  • Sa Girman jiki da wuri#
  • Kara karfin Garkuwar Jiki

Karanta:

Maganin Ulcer: Yadda zaka magance gyanbon ciki ulcer Babba da karama