Skip to content
Home » Addua ko Wuridin Samun Kudi

Addua ko Wuridin Samun Kudi

Idan akayi magana akan samun kudi kowa yana so kuma kamar yadda aka sani arki na Allah ne kuma nufinsa ne, to a addinance ma akwai wasu wuridi ko ince addu’oin da mutum zai rika yi wanda hakan cikin ikon Allah idan mutum nayi inshallahu koda bai zama mai kudi na azo a gani ba zai samu rufin asiri.

Sai dai kuma hakan ba yana nufi ba kuma daga samun addua ka samu waje ka zannan ba kabar yin sana’a ko kuma kasuwanci ba hakan illa ce da kuma hasara kake jama kanaka.

wuridi da adduar samun kudi

Abubuwan da Mutum ya kamata ya lazimta

Akwai abubuwa daban daban daban da ya kamata a matsayinka na musulmi ka rika yawaita yi idan kana son Aallah ya taaimaka maka a fannin kasuwancin ka kasa samu kudi.

Karanta: Maganin Yawan Kasala a Jiki

Yawaita Istigfari

Yawaita neman gafara a wurin Allah wato istigfari yana kara arziki, ya kai dan uwa ka rike yawanita tuba da neman gafara ga Allah indai kana son tsira a ranar gobe kiyama da kuma yalwar rayuwa da ta arziki a nan gidan duniya.

Yawaita Rokon Allah a cikin Dare

sallar dare tana da matukar mahimmanci kuma addu’a a cikin sallar nafila ta dare tana daya daga cikin adduoin da ake saurin amsa a wurin Allah.banda ita kanta tashi a lokuttan da mutane ke bacci ana addua ana samun lada mai tarin yawa sosai.

Yawaita karanta Al Qur’ani

Yawaita karanta Qurani abu ne mai tarin lada garkuwa ne kuma abu ne wanda indai da kyakkyawar niya ake samun tsira a wurin Allah ranar gobe kiyama.

Duk mutumin da ya rike Qur’ani to inshallahu badai ya ce ya shiga matsatsi mai muni ba wanda ya rasa yadda zai yi sai dai in bai rike littafin Allah da kyau ba.

Karanta:

Abubuwan da ke taimakawa wajen zaman Hardar Qur’ani

Abubuwan da ke taimakawa wajen zaman Hardar Qur’ani

Biyayya ga Iyaye

Yawaita yima iyaye biyayya abu ne da ke sama rayuwar mutum albarka banda ga kuma samun addu’ar su wanda kamar yankan wuka take.

To idan kana son samun kudi ka yawaita yi masu biyayya tare da neman surika yi maka addu’a ta samun tsara da rabauta a Duniya da KUma Lahira.