Skip to content
Home » Kananun Sana’oi 10 Masu Saurin Kawo Riba Wanda ake Iya Farawa Da karamin Jari

Kananun Sana’oi 10 Masu Saurin Kawo Riba Wanda ake Iya Farawa Da karamin Jari

Sanaoi akwai su kala daban daban sai dai wasu sunfi wasu riba kuma ya danganta ga yanayin yadda abun ya kasance sai dai ya danganta ga inda kake da yanayin yadda zaka samu custominka.

To inshallahu a yau zamu yi dubi a kan wasu kana nun sana’oin da ya kamata ka yi domin dogaro da kai da kuma yadda suke tare da bayani akansu.

Mi ake nufi da Kananun Sana’oi

kananun sana’oi na nufin duk wani nain sana’a ko kuma kasuwanci wanda za’a iya fara shi da karamin jari da kuma karancin masu hannun jari, in ma na mutum guda ko kuma da yawa mafi yawanci ma na mutum gudane.

Kananunsana'oi

kananun kasuwanci ko sana’oi sune suke habbaka su koma manya wadanda ake kira da Kamfani wanda an samu cigaba idan aka kai wannan matakin saboda karuwar jari, kayan aiki, da kuma ma’akata kai har ma da masu zuba hannun jari.

To amma yana kyau kasani cewa karamar sana’ar ce ake raino ta koma babbar abunda dai ake so komin kankantar sana’a kada ka sake ka raina ta saboda hakan shine ya sa duk wani mai arziki ya kai matakin da ka hango shi idanda ya raina da bai kai wannan mataki ba.

Ga wasu daga cikin su wanda kananun su da naira 5000 ma ko kasa da haka kana iya fara su ka cigaba da samun ribar ka a koda yaushe.

Lissafinsu

  • Gyaran Waya
  • Saida Abinci
  • Odar kaya
  • Saida Data
  • Saida kayan Chemicals
  • Sana’a Art
  • Saida Magunguna
  • Sana’ar Communication
  • Saida Kayan Awo
  • Saida Takalma

 

Gyaran Waya

Gyaran waya sana’a ce wadda ake samun kudi da ita sosai saboda nan take gyara daya mutum yana iya samun dubu biyar ko goma karanci dari biyar ake basu kudin gyara kuma yanzu gashi ana yawan amfani da waya.

Kowa yana amfani da ita wanda shiyasa dole ne yau da gobe su samu matsala wanda sai an ga mai gyara da jari kalilin ana iya fara ta kuma munyi bayanin ta sosai a wannan post din kana iya duba shi.

Karanta:

Yadda ake Fara Sana’ar Gyaran Waya

Saida Abinci

sana’ar saida abinci ba karamar sana’a bace indai akwai masu ci kuma yawanci indai da dadi kuma an inganta zaka ga ana saye saboda abu ne wanda karanci kowa ya  ci sau uku wasu ma har fiye da hakan.

yawancin ribarta yana rubawa indan kana son fara sana’ar abinci na daga abunda tafi so shine kyau, dadi da kuma kawata wajen cin abincin saboda mutane suna son abu mai kyau musamman a ce wanda za’a ci ne.

Karanta:

YADDA AKE GIRKI COMPLETE SANWA YADDA ZANI GIRKA ABINCI KALA KALA

Girki Adon Mace: Kala-kalar Girki da yadda zaki kware akan kirki don shine adon mata

Odar Kaya

ordar kaya tana nufin shigo da kaya daga wata kasa zuwa taka ana samu sosai kuma yanzu zuwan zamani abubuwa sun canza.

Domin ada idan zaka fara dole sai ka bar kasa amma yanzu ta online a wayarka kana iya sayen kaya koda kwara uku ne a kawo maka gida Nigeria daga China.

Karanta:

Yadda zaka sayi kaya daga China a kawo ma su har Gida

Abubuwa biyar 5 da ya kamata ka sani kafin sayen kaya online

Saida Data

Abua na gaba kuma shine fannin sadarwa saida data da abunda ya shafi kati ana samun kudi da data sosai kuma karamar sana’a ce wadda ko da kudi kalilan ana iya farata.

Da naira 2000 ma kana iya farawa kuma ana samun riba saboda karancin ribar data 1GB shine naira hamsin to ka gani wani ma na iya cewa a samashi 3GB kaga 150 lokaci daya a matsayin riba to indai akwai customer to ana samun kudi da data sosai gaskiya.

Saida kayan Chemicals

Kayan chemicals idan mutum ya san inda zai same su da sauki ana samun kudi abubuwan sun kunshi hada manshafawa da saida shi sai sabulu da kamar su ai freshner da sauransu dyk abubuwa n da ake samun kudi da su.

Sana’a Art

sana’ar art ta kunshi zanen rubutu akan rikag ko bango wanda kudade ake biya sosai  yi aikin, ana samu da ita sosai kuma abaya munyi magana akan sana’ar da yadda ake yinta da abubuwan da suk shafe ta kana iya dubawa.

Karanta: Sana’ar Art da printing ta fenti da abubuwan da ta kunsa

Saida Magunguna

saida magunguna yana nufin che,mist kuma kar ka ce wane kala a’a duka kona gargajiya kona zamani duka ana samun kudi saida su sado yawan rashin lafiya mutane ba lafiya sosai.

dalilin samun kudi da wannan sana’a shine yadda magani yake linka ribar shi in na 50 ne sai kaga an saida shi 100 koma 150 to shiyasa kuma ga yawan rashin lafiya ga mutane.

Sana’ar Communication

Sana’ar communicationa abu ce mai kyau wadda take da riba kuma ta kunshi saida kayan waya, na gyaran waya, charji da sauransu wadda saboda yawan wayoyi a hannun mutane yasa sana’ar ta bullo domin ta zamani ce da babu ita da babu waya.

A baya itama munyi magana sosai akanta zaka iya duba rubutu na kan communication da yadda ake yinta.

Karanta: Sana’ar Communication da Abubuwan da Suka Shafe ta

Saida Kayan Awo

Kayan awo sune kayan da ake girbe daga gona wadda musamman duk bahaushe yasan lokacin kaka kayan abinci suna saukowa to saye daga manoma ana rabawa zuwa daidaya ko masu shaguna abun nada riba sposai saboda wani lokacin ma sun fi masu noman samun kudi.

Saida Takalma

saida takalma abu ne mai kyau wadda karamar sana’a ce wadda ake samun riba dari kaza zuwa dubu kaza saboda itama kaga kowa dole yasa takalmi a kafarsa.

Kuma ita wannan sana’a idan ka iya hada takalma an fi samun riba sosai kuma kana da yanci akan yadda ke ke son ka hada takalmi ka saida ma customer dinka.