Skip to content
Home » Maganin Kurajen Fuska ga Mata da Maza

Maganin Kurajen Fuska ga Mata da Maza

Kuraje a fuska basu da dadi musamman ace suna da yawa sukan canza ynayin fuskar mutum namiji ne ko kuma mace ta yadda kusan har kyan shi ma yana raguwa.

A cikin wannan post din zamuyi magana akan kurajen da suke addabar mutane a fuska wanda a trurance ake cemasu pimples da kuma hanyoyin da ake bi domin magance su a cikin sauki.

Maganin kurajen fuska

Kurajen Fuska

Kurajen fuska kurajen fuska kamar dai yadda aka sani a idan sukayi yawa kusan sun a bata fuskar mutum su sata tayi baki duk fuskar mutum ta baci musamman ma mata.

Akwai abubuwa daban bdaban da suka sa kuraje su fito a fuskar mutum wani lokacin kamar yawan shiga rana samun bacteria a saman fuska da sauran su duk abubuwa ne wanda zasu iya hadasa faruwar kuraje a fuskar mutum.

kuma akwai abunda ya kamata ka sani shine a koda yaushe idan kana son samun lafiya a cikin jiki ka rika yawaita cin kayan marmari wanda suka nuna saboda suna dauke da sunadaran da ke taimakawa sosai wajen inganta lafiya.

Ga kuma wasu muhimman abubuwan da ke taimakawa wajen magance kuraje a fuska zaniyi bayanin su a kasa.

Karanata: Amafanin Motsa JIki a jikin Dan Adam

Yadda ake magance su

Waddannan abubuwan da zan lissafa suna taimakawa wajen magance kuraje cikin ikon Allah.

Zuma

Kamamar yadda a baya mukayi bayani akan amfanin zuma a jikin mutum, gaskiya zuma tana magani sosai mkuma itace aka ambace ta a cikin Al qurani tana yin magunguna da dama na ciki dana waje.

Wanda idan kana da kuraje zaka iya ka rinka shafa masu kamar safe da marece inshallahu cikin kankanin lokaci zaka ga sun warke ko kuma wani tabo shima da wuri zaka ga ya kafe.

Karanata: Amfanin Zuma 10 ga Jikin dan Adam

Ganyen Magarya

Ganyen magarya yana magugun guna da yawqa kamar yadda a baya mukayi magana da bayanin akan yadda ganyen magaraya yake gyara jikin mutum, to a kuraje ma yana taka rawa sosai.

Karanata: Yadda Ganyen magarya Yake Gyaran jiki

Yadda ake yi kuma shine za’a samu dakakken ganyen magarya sai a samu wuri a kwaba da ruwa  yayi kumfa daga nan kuma sai a rika shafa ma fuska  a shafe ta duka a bar shi yayi karanci minti talatin.

Amfanin shine yana maganin kuraje kuma yana sa jiki tafshi tare wanke dauda a saman fatar mutum.

Lemun Tsami

Abu na gaba kuma shine lemun tsami wanda a kimiyyance lemun tsami yana wanke dauda da cututtuka a jikin dan adam, to a fannin fuska ma idan kuraje suka dame mutum ana yanka shi sai a rika shafawa a fuska inshallahu cikin karamin lokacin za’a samu saukin su.

Aloe vera

Aleo vera tana maganin cututrtukan da ke da alaka da da fata to a fannin fuska ma ganyaen aloe vera yana taka rawa sosai wajen magance cututtuka da ke da alaka da fuska, to da an samu ganyen sai a ringa shafa ruwan a fuska inshallahu cikin karamin lokaci zasu warke.

Lalle

yana da matuykar amfani wazen tsotse cututtuka da kuma kauda wasu bacteria da ke a saman fata to a fusaka ma idan ana kwaba shi ana shafawa bayan kamar minti talatin ana wankewa yana kyara fusaka kuma ana iya hada shi da ganyen magarya domin kara kyalli da magance cututtukan da suka shafi fuskar.