Skip to content
Home » Maganin Yawan Kasala a Jiki

Maganin Yawan Kasala a Jiki

Kasala a jikin mutum tana da matsala sosai tana da hadari ga ayyukan sa kuma kai har ma ga lafiyar sa, wanda idamn aka ce mutum ya zama kasalalle duk yawancin al’amurran sa zasu koma baya.

To yau inshallahu a cikin wannan post din zamu yi magana a kan wasu hanyoyin da suke taimakawa sosai wajen magance kasalar jiki tare da bada wasu muhimman shawarwari da zasu taim aka wajen samun kuzarin yin aiki sosai.

Mi ake nufi da Kasala?

Abunda ake nufi da kasala shine jin jiki yayi ma mutum nauyi ko yaji babu karfi da kuzarin aiki kwata-kawata wanda kowa ya sani cewa an san dan Adam kullun yana da wasu muhimman ayyukan da yake yi ko kuma yake son yayi wanda hakan shine chigaba rayuwarsa.

Maganin kasala

Kasala idan tayi yawa zaka ga mutum yayi ta yin bacci sosai wani na iya share fiye da awa 5 a rana yana ta bacci saboda yadda yake jin baya iya yin komai.

Kawai abunda zai iya shine ya ci ya sha sannan ya kwanta yayi ta sharara baccinsa abunsa ba tare da yana jin zimmar aiki ba wani kuma koda yana jin zimmar aikin to baya iya yinsa saboda nauyin jikin.

To ga yanayin yadda kasala ta rabu zamu yi magana  akanta.

Gida nawa ta rabu

To kasala ta rabu gida biyu akwai wadda take ta sanadiyyar ciwo musamman basir ko kuma wani ciwo dna daban akawai kuma wadda ita lalaci ce da mutum yake sama kansa yaji baya sha’awar tabuka komai a rayuwarsa ta duniya.

Kasalar Rashin Lafiya

Idan baka da lafiya tabbas kasala tana zuwa wanda kusan ma kashi 60 cikin dari na rashin lafiyar da mutum yake yi zaka ji kasala ta biyo baya hakan yana faruwa ne adalilin nakasa da wani bangare da jikin ya ji ko kuma ciwo.

Irin wannan kasalar koda a cikin zuciyarka kana son ka yi wabni abu saboda rashin kuzari na garkuwar jiki da kuma wasu sassa na jiki ya kan sa baza ka iya yinsa yawanci  sai an samu saukin rashin lafiyar irn wannan kasalar take tafiya.

Karanta : Hanyoyin da ake bi Domin Rage Kiba

Yawan cin kayan kwalam da maiko yakan jawo cutuka kamar cutar basur wadda zaklaji kugunka na kaikai ga kuma kasala to sai ka nemi maganin zafi sannan zaka ji ka samu saukin irin wannan.

Karanta: Hanyoyi 10 Domin Karin Kiba a Jikin Mutum

Kasalar Lalaci

Nau’i na biyu kuma itace kasalar da mutum lafiyarsa lau babu inda yake masa ciwo amma inda matsalar take a zuciyarsa shedan baya barin sa yayi komai sai yaji ya kaji abun akwai wahala

Waanda kuma da ya tashi zai ji ba wata wahala ke akwai ba sosai to wannan akwai matsala daga hali ne. yana da kyau ka sani ba wai sai ka zo bauta ba ne shedan ke hanaka ba.

A’a koda wani abu ne mai amfani a rayuwarka yana kokarin hana ka domin in ka barshi zaka tafi kaje kayi wanda yake na illa na alfasha ko abun ki.

ka zabura ka motsa jikinka ka tuna mahimmancin abun da yadda zaya amfane ka sai kaji ta tafi.

Karanta: Amafanin Motsa JIki a jikin Dan Adam

maganin kasala

Karanta: Maganin Kurajen Fuska ga Mata da Maza

Hanyoyin magance

Akwai hanyoyi da dama da ake bi domin magance kasala wanda a nan zamu kawo su na nau’ikan kasalar ta rashin lafiya da kuma ta lalacin baki daya wanda indai mutum ya bi su inshallahu zai ji dadin jikinsa.

  • Yawan motsa jiki yana magance ta
  • Karanta cin abubuwa masu maiko ko suga
  • Barin shan giya da duk kayan shaye shaye.
  • Barin shan taba da abunda ya shafe ta baki daya.
  • Yin bacci isashe
  • Barin cin abinci gaf da lokacin kwantawa bacci
  • Sallar dare da karatun alkur’ani kafin kwantawa bacci
  • Tsara abubuwan da zaka yi a rayuwa
  • Tunani mai kyau na nasara idan ka yi aiki
  • Jin dadin aiki a lokacin da kake yinsa

wadannan abubuwa da muka ambata a sama suna taka rawa sosai a wajen magance kasala, ga m ai tambaya ko kuma karin bayani yana iya yi a comment section.