Skip to content
Home » Sana’ar Bookshop Littafai da yadda ake fara ta

Sana’ar Bookshop Littafai da yadda ake fara ta

Sana’ar saida littafai sana’a ce wadda ake samun kudi da ita sosai musamman ma a wannan zamnin na da mu ke ciki.

Inda mafi yawancin mutane suke yinta kuma idan suka sa hakuri da kula suna samun nasara sosai, to a wannan post din zamuyi dubi akanta da kuma yadda zaka fara ta kai harma matakan da zaka bi ka samu sasukin wasu kayan ka rinka hadasu da kanka.

Bayani akan Sana’ar littafai (Bookshop)

Ita dai kamar yadda ake fi saninta ta kunshi saida litattafai ne amma kuma ba su kadai ba da sauran abubuwan na karatu wanda dan makaranta yake da bukata a fannin karatunsa.

bayani akan sana'ar bookshop

Kuma zaka ga mafi akasarin abubuwan da ake saidawa suna da riba musamman ace akwai ciniki sosai.

Kuma wadansu abubuwan ma kana iya hada su da kanaka idan ka tsaya ka kula ba sai ka saro ba saboda akwai wanda zakaga kananun yan kasuwa ke hada su misali kamar emvlope.

Ba irnsu envelope ma kawai ba kana iya hada abubuwan printings na karatu kamar chart na yara na lambobi da haruff, kai koma kana da wani littafin da kake son ka hada shi kana iyawa ka kai a buga maka ka saiada.

Kuma ita waannan sana’ar tana da bukatar abu daya wato shine fitowa da wuri sosai saboda tarbar dalibai yan makaranata da wuri suke tafiya.

Dole sai kayi hakuri akalla wajen bakwai kana shagonka ka bude saboda yanayin custom ominka na wuri ne.

Yadda zaka Fara

Domin fara saida abubuwan littafai yana da kyau ka tsaya ka kula da wasu abubuwa kamar haka a zagaye ko area da kake son fara ita wannan sana’ar sadoda abu ce wadda yawanci zakayi ta’ammuli da masu neman ilimi ko kuma alaka da shi ilimin.

Ga wasu daga cikin muhimman abubuwan dubawa.

 • Shin wajen center ce da mutane suke wucewa lafiya lau.
 • Shin akwai yan makarantar da suke wucewa ta hanyar waje
 • Shin kuna da yawa a wajen da zakayi sana’ar an san wajen da yinta koko kai kadai ne.

karanta: Kananun Sana’oi 10 Masu Saurin Kawo Riba Wanda ake Iya Farawa Da karamin Jari

Abubuwan da zaka iya saidawa

A sana’ar Bookshop ta saida littafai mayaki- mataki ce idan kana matakin karanta zaka ga abubuwan karatu dana printing kawai kake saidawa.

Amma ahankali idan ka girma ka zama babba kana iya hadawa da abubuwan da za’a iya buga kayan karatun da su kamar computoci. photocopyer printer da ma sauransu.

Ga lissafin abubuwan da zaka saro a kasuwa domin ka fiddo kasuwancin ka kana iya kara wasu ma har wanda ba’a ambata ba, amma ya zama karanci kana da su saboda ana neman su.

kayan karatu wanda zaka iya saidawa

Hajar da zaka saro

 • Biro
 • Pencil
 • Cleaner
 • Ruler
 • Plan sheet A4, A3 da sauransu
 • Envelope
 • File
 • Sum Papper
 • Math set
 • Stepler pin
 • Selotape
 • Charts
 • Alli
 • Marker
 • Sharpener
 • bubuwn Binding
 • Littafan Girape dana zane
 • Correction fluid
 • Littafai na Koyon Hausa
 • Littafai na koyon Turanci

Karanta: Gyaran Waaya: Yadda ake Fara Sana’ar Gyaran Waya

Yadda Zaka Samu Saukin Kaya

kamar yadda na fada a farkon post din nan kana iya yin wasu abubuwan da kanaka idan kana son samun riba sosai to idan kana son ka samu saukin kaya a irin wannan sana’a ta bookshop akwai hanyoyi kamar haka.

Hadawa da kanka

Ko shakka babu idan kana son ka samu sauki to ka rika hada wasu abubuwan da kanka da kake ganin zaka iya samun sauki.

Abubuwa kamar su envelope, file ko kuma ma kayan chart wanda ake likawa da ake amfani da su wajen koya ma yara kana iya sa masu sana’ar art ko kuma masu printing su hada maka.

Kuma kaima kana iya hada littafai naka nakanka da zaka iya saidawa zuwa ga mutane hakan ma yafi riba kaga kana saidawa kuma kana iya ba wasu sari.

Hadin Kwiwa

Hadin kwiwa  a nan ta zama a hanya biyu ce kodai da masu rubutun littafi ko kuma da masu bugawa.

Idan ka yi hadin kwiwa da masu rubutun littafi suna iya baka damar buga editoions ko nsamsur kala kala na rubutunsu kuma kaga kai ke kula da abun.

Idan kuma da masu buga littafai ne kaga su suna da alaka da masu rubutun littafin shima lafiya lau hanya ce ta samun sauki

Buga ma wasu

kana iya tsayawa ka dauki nauyi ka buga ma wasu wato wasu su rubuto littafi sai ka buga masu ka saida ma yan sari da dai daya.

Duka kana iya yin haka kuma idan ma kai sa’a a ka san ka kana wannan harkar kayi fice to ita ma kanta sana’a ce ko ince kasuwanci ne mai zaman kanasa da zaka samu kudi sosai.

Karanta:

 Yadda ake koyon Computer da kuma Bayani akan Ilimin Computer

Sana’ar Communication da Abubuwan da Suka Shafe ta