You are currently viewing Fasahar Kirar Zamani ta 3d Printing da Yadda Take

Fasahar Kirar Zamani ta 3d Printing da Yadda Take

Kira abu ce wadda ta tade a fadin duniya anayi tun daga kira wadda aka gada kaka da kakanni inda ake kero abubuwa musamman na karfe, duk da cewa kira ba wai ta dogara kadai ga karfe ba a’a duk wani abu da ya shafi abun amfani, akwai kira ta zamani da tazo wadda ake kira da 3d printing.

Kamar yadda ake kera abubuwa a da yanzu abun ya kasa sauki ko ince an kara samun cigaba ta yadda zaka zana kawai kayi printing ba tare da an ta bin hanyoyin sa abubuwan da za’ayi kama da su shin ya take?

Yadda Fasahar Kirar 3d Printing

Fasahar 3d printing sabuwar fasaha ce da ta kunno kai a wannan zamanin, kuma an samu cigaba sosai ta hanyarta yadda take shine.

Za’a zana abu a cikin computer zane na nau’in 3d ayi modeling dinsa yayi kyau kala da sauransu a cikin computer wadanda suke wannan aiki sune masana computer.

Bayan tsara shi yadda ake sonsa ya danganta akwai wadda ake fiddowa ta roba wanda abun ko ince injin printer din roba take fiddawa akwai kuma wadda karfe take fiddawa.

To bayan an zana shi da ansa printers din zasu fidda shi a yadda aka zana abun misali idan roba ce ko kwallo aka zana kwallo zata fito kawai yadda aka zana a computer.

A cikin computer kuma ana amfanida  manhajar Software ne ake amfani da ita ake zana abunda ake so kafin ba injin bugawa wato printer ta fiddo abun.

Karanta:

 Manhajar software da ya kamata ka zaba domin Kasuwanci

Manhajar Software wadanda ya kamata ka koya domin dogaro da kai

Tasasirin Fasahar

fasahar Yanzu tana taka rawa sosai a fadin duniya saboda yanzu kasashen da suka cigaba suna ta kokarin amfani da ita, mayan kamfunna suna ta kokarin mallakar irin wadannan kayan aikin saboda yadda ake tunaninta a na gaba.

Kasashe kamar su Dubai, china, Amerika da sauran manyan kasashe  suna ta kokarin amfani da ita da samun kwararru a fannin saboda abu ne wanda komai zaka iya kerawa indai an zana.

A nan gaba kuma akwai binciken da akai da ke nuna zaya kawo aiki da kudi na billioyoyin daloli nan da shekarar 2029 shiyasa manyan kamfunnan suke rige rige a fasahar.

Karanta: 

Abubuwan da ke Haska Hajar Karamin Kasuwanci su maida shi Kamfani

Hanyoyin 5 da Suke Taimakawa Wajen Maida Karamin kasuwanci Zuwa Kamfani

Yadda Injin Printer yake Aiki

Shi wannan Injin ko printer wadda ake kirar da shi tana aiki ne kamar printer ta masu sana’ar printing da photocopy, ana samata pawder ta roba ko kuma karfe ya danganta abun na karfe ake so ko na roba.

injin kirar zamani ta 3d

Wanda daga nan ne za’a fidda abun, yana aiki ne akan maatakai kusan guda ukku wanda sune kamar haka zamu yi bayaninsu:

Zane da Manhaja Ko Modelling

Da farko dai za’a zana abun a manhaja cikin computer wadda za;a iya zana abu lafiya lau yadda yake wanda shine ake kira da 3d abu zai fito a surar shi da kuma yanayin kalar shi babu bambanci.

Ita wannan manhaja aikinta kawai shine tsarawa da kuma hada hoton da za’a tura wanda ake son a fidda shi zuwa abunda ake gani a fili daga surar da aka zana a cikinta.

Baraguzai ko Datsawa

Daga nan kuma Injin zai mayar da zanen sura a yanayin baraguzai, kamar yadda dai masu zane idan zasu yi zane zasu maida shi a baraguzai wato sahe-sahe ko kuma gunduwa gunduwa na gabar abun.

To shima injin a farko sai ya fara maida abun a irin wannan yanayin kafin a fidda shi ya zama abunda ake gani lafiya laua a fili wanda za’a yi amfani da shi.

Fiddo Abun

Daga nan kuma sai a fidda bayan an maidashi guduwa gunduwa kamar yadda mukayi bayani a sama, daga nan ne injin zai hade wanna gaba-gabar da aka hada.

Bayan hadewar sai a fidoo abun lafiya lau yadda ake ganinshi da siffar shi kamar dai yadda aka zana shi a cikin computer bashi da wani bambanci da yadda aka zana.

Abubuwan da ake Iya Kerawa

Ta hanyar wannan fasaha ana iya keara abubuwa da yawan gaske wanda suka hada da kayan amfani yau da gobe na plastic ko kuma roba bugu da kari akwai injin printer wanda akae iya kera abubuwan karafa da ita kamar yadda aka fara na roba wato plastic ga fannin abunwan da za’a iya.

  • Karfen da ake son ayi amfani da shi a asibiti a sama mutum za’a iya kaiwa a zana a sama mutum kamar a kashi
  • kayan wasa na yara
  • Bangaren ko part na JIrgi
  • Bangaren abunda ya shafi mota
  • Kayan amfanin yau da kullun kamar kofi da sauransu

Karanta: Bayani akan Bude Kamfani domin dogaro da kai

Wuraren da ake Samun Injin Printer

Akwai wurare da dama da suke saida printoci wanda kana iya shigowa da su kasashe irin namu na Nigeria, ya danganta kodai kai ka taka kaje kasar ka sawo ka hadu da makwara.

Kokuma kayi bincike sosai ka gane yadda abun yake ka saya a wiraen onlin kamar su Amazon, Aliexpress, MadeinChina da sauransu kana iya saye ayi maka shipping zuwa kasar Nigeria.

Karanta: 

Yadda zaka sayi kaya daga China a kawo ma su har Gida

Abubuwa biyar 5 da ya kamata ka sani kafin sayen kaya online