Skip to content
Home » Yadda Ake cike Application na Aiki a online da kanka

Yadda Ake cike Application na Aiki a online da kanka

Sau da dama zaka ga gwamnati ta ude wata dama ta daukar ma’akata kamar su yan sanda, civil defence, immigrations da sauransu, wanda kuma dole a on line ake cike shi, mafi akasari sai anje cafe ake dauka amma aka sani ba a gida da wayarka ko a computer dinka ma zaka iya yi.

A cikin wannan post din inshallahu zamuyi bayani akan yadda zaka koya koda wayarka kana iya cikema kanka koma waninka cikin hanyoyi masu sauki.

yadda ake cike application na neman aiki a online

Muhimman Abubuwa Game da Cike Abu Online

Cike application online abu ne wanda yake da bukatar sanin yadda ake browsing ko kuma yadda ake hawa shafin yanar gizo a cikin waya ko computer.

Saboda dole za’a shiga a shafin yanar gizo wato website wadda aka kayyade ta domin masu cike application din su shiga su cike a cikinta.

To ba iya nan abun ya tsaya ba kawai shafin ya zamana sahihin shafi ne wanda kamfanin ko kuma in na gwamnati ne ya kasanace shine ka shiga.

Saboda zamanin nan yadda aka samu cigaba sosai a internet hackers sunyi yawa wanada zaka iya shiga ka sa bayananka su kwashe su illata ka.

Amma akwai hanyoyin da ake saurin gane sahihin shafi na gwamnati kamar haka.

  • Ya kasanace ya kare da .gov.ng a karshen suna idan ma’akata ce
  • Ya kasance idan fannin soja ne .mil.ng
  • Idan kuma makaranta ce .edu.ng
  • Ya kasance ka bincika musamman wajen masu cafe sun tabbatar ma shine shafin

Karanta: 

Yadda ake koyon Computer da kuma Bayani akan Ilimin Computer

Matakan Da Zaka Bi

matakan da zaka bi wajen cike application online

Dafarko idan ka shiga a website din ka tsaya ka natsu ka fahimce ta sannan ka duba zaka ga cewaa kila su raba yanayin daukar aikin zuwa kashi kashi ya danganta.

Bayan nan kuma sai ka zabi wanda yayi daidai da kwalinka ma’ana certificate ko result dinda kake da shi wanda zakayi apply  da shi.

Daga nan kuma sai ka cike suna da Email address dinka wanda zakayi amfani da shi a inda ya dace yadda form din ya tsara ka tabbatar ka zai local government da state a daidai idan aakwai auuwan da zaka daura ka daura photon su ko kuma pdf dinsu.

Daga nan duk application a karshe ssuna baka summary ka tabbatar bayanan ka daidai suke idan komai daidai ne sai ka dannan sumit ka aika shi.

Bayan turawa ka tabata ka yi printing na slip din karshe ko waya yanzu tana print as pdf musamman idan kana amfani da chrome browser.

Ka kula documents dinka idan baka da scanner kana iya samun waya ka dauka hoto akwai apps ma na scanning sai kayi installing a cikin wayarka, ko kuma ka kai ayi maka scanning ka aje saboda idan hakan ta tashi don gaba.

Karanta:

Kasuwar Canji: Bayani akan Sana’ar Canjin Kudi

Yadda ake Gano Waya Bayan ta Bace ko an Sace ta

Bayani akan Samuwar Gas daga Shara ko Bola

 

Wasu Daga cikin Sanannun Portal na Gwamnatiu

Portal na Immigration da Civil Defence: https://cdcfib.career/

Portal na Yan sandan Nigeria: https://www.policerecruitment.gov.ng/

Portal na Navy: https://www.joinnigeriannavy.com/

Portal na Customs: https://customs.gov.ng/

Portal na duba result na Neco: https://result.neco.gov.ng