You are currently viewing Fasahar Biogas: Bayani akan Samuwar Gas daga Shara ko Bola

Fasahar Biogas: Bayani akan Samuwar Gas daga Shara ko Bola

Samun Gas na Abinci yanzu ba dole sai ya zama cewa an sawo shi ba, a’a daga shara kom kuma kashin dabbobi cigaban zamani ya zo da dabaru na tanada shi domin ya zama gas mai amfani wanda za’a iya amfani da shi a girki,hada wuta lantarki  da dauransu.

Kasashe da yawa kamar su india, Ameri da sauransu suna amfani da irin wannan fasaha wajen samun gas na abinci wanda kuma har kamfunna ke akwai wanda suke saida irin wannan gas din ko kuma su hada wutar lantarkin da za’a iya cigaba da amfana da ita musamman ma a wuraren karkara inda ke da gonakai.

bayani akan fasahar biogas samuwar gasa

Minene Fasahar Biogas?

Abunda ake nufi da Fasahar Biogas shine dabaru ne na samar da gas wanda a turance ake kiranshi da methan da sauran gas kamar hydrogine sulphide da carbondioxide domin ayi girki ko kuma a sama inji shi domin samar da wutar lantarki ko samar da zafi daga shara ko kuma kashin dabbobi ko na mutane.

Manyan kasashe kamar su ingila suna amfani da shi sosai wanda kamar yadda mujallar wikipedia ta tabbatar kusn kashi 17% na ababen hawar kasar na amfani da shi a matsayin man da ake zirga zirga da shi a kasar, banda wanada ake amafani da shi a fannin girgi.

Karanta: 

Nau’in Kamfani 5 da Zaka Iya Fara su a Natsayin Karamin Dan Kasuwa

Adashe: Sana’ar Adashe da yadda ake yinta

Yadda Zaka Bude Kamfanin Abunda Ya Shafi ko Abun Sha Abinci a Nigeria

Yadda Ake Samunsa

Idan ana son a samu biogas to yana kasancewa ne a dalilin rubewar bola ko sharar kayan gona ko kuma kashi na tsawon kwanaki ko sati wanda hakan zai sa abun ya gume ya haifar da shi gas din.

Ba’a son iska ya shiga inda aka zuba abunda aka rufe domin ya rube eanda a turance ake cema shi digester a cikin ta ne ake rufe abun saboda kar ya sha iska.

Bayan kwanaki abun ya rube wato bacteria ta rubar da shi daga nan zai haifar da gas mai lafiya wanda za’a iya amfani da shi a giriki ko kuma wajen wutar lanfarki.

Karanta: 

Bayani akan Bude Kamfani domin dogaro da kai

Samun kudi ta Zuba Hannun Jari

Shin Za’a Iya yinsa A Kasashe Kamar Nigeria

kowace kasama tana iya yinsa a matsayin hanyar da zata kara taiamaka mata wajen habbaka tattalin arzikinta wanda ta hanyar za’a iya samun kudin shiga ga mutanen da basu da aikin yi.

saboda abun ba wai dole sai da wasu ingina ake yinsa ba kawan sannin yanayin yadda fasahar take da fahiumtar ta yake bukata wanda amfanin sa bayan ma anfidda gas dinda za’a yi amfani da shi tofa sauran taki ner wanda shuka take matukar sonsa.