You are currently viewing Yadda ake Gano Waya Bayan ta Bace ko an Sace ta

Yadda ake Gano Waya Bayan ta Bace ko an Sace ta

Yadda za’a iya gano waya wadda ta bace ko aka sace ta abu ne mai matukar mahimmaci ace ka sanshi saboda yadda yanzu wayoyin hannun mu irinsu android ko iphone muke aje masu abubuwa da yawa na amfanin yau da kullun wanda ya shafi kasuwanci, karatu da ma sauran harkokin yau da kullun.

A yau zamu yi dubi akan muhimman abubuwan da ya kamata ace wayarka tana da su kuma suna akai idan da ya kamata ka sani kafin samun damar ganinta saboda zakayi amfani da wata wayar ko comfutaer ce sannan ka iya gano ta.

yadda zaka gano wayarka bayan ta bace

Abubuwqan da ake bukata domin gano wayarka da aka sace ko ta bace

A da idan barawo ya  sace maka waya ko kuma ta bata shikenan babu yadda zaka iya yi, to amma yanzu an samu cigaba wanda zaka iya ganin inda take ta hanyar taswirar map, Ga jerin abubuwan da ya kamata ka sani kafin farawa wanda ya kamata ka tabbatar kana sda su:

  • Samun wata waya ko computer mai hade da internet 
  • ka tabbatar waccen wayar da kake nema a kunne take ba’a kashe ba kuma location kunne yake da internet
  • ka tabbabatar kana da Email Address ka kuma yi login dinshi a wayar.

Wadannan abubuwa guda ukku da muka ambata sune suke da muhimmaci da ya kamata ka tabbata kana da su domin ka gano wayar ga kuma mattakan da zaka bi domin haka.

Karanta: Yadda ake Bude Email Address a waya ko Kuma a Computer

Yadda ake login din Email ko Gmail address a cikin wayar Android ta hanyar amfani da Gmail App

 

Mataki na Daya 1

Da farko zaka shiga wannan addreshin na yanar gizo a wata wayar ko computer cikin browser chrome ko opera amma kayi da chrome yafi https://android.com/find inda zai kaika wajen da zaka sa Gmail dinka wanda yake akan wayar da kake nema.

Mataki na Biyu 2

Bayan  ka shiga zai nuna maka wayar sai ka zaba inda zaka ga suna wayar ka da kuma alamun map na garin da take ko wurin da take ba lalle ka gane sosai ba sai ka natsu.

Amma ana tura ma wayar sako ne kana iya sata tayi kara ko ka goge abubuwanka.

map na gano wayar da aka sace ko kuma ta bace

Mataki na Ukku 3

A wannan matakin kana iya kokarin fidda abubuwan da ke ciki ka goge su inkuma wajen kusa ne inkasa stayi ringing zatayi kara kana iya fahimtar inda take idan har tana kusa da kai ne in kuma bata kusa bazaji karar ba.

wannan shine yadda zaka gano wayarka da aka sace ko kuma ta bace a matakin farko kafin bincike sosai.

Karanta: Yadda zaka fara Sana’ar Saida Data

Bayani akan Samuwar Gas daga Shara ko Bola

Adashe: Sana’ar Adashe da yadda ake yinta