Skip to content
Home » Abubuwan Zamani da Yakamata Matasa su Sani a Wannan Zamanin

Abubuwan Zamani da Yakamata Matasa su Sani a Wannan Zamanin

A wannan zamanin Musamman kasashe. Masu tasowa irin su Nigeria ana samun yawaitar matasa sosai wannan hakan ba illa bace abun alfahari ne da kowace kasa take so taga tanada matasa masu tasowa,, amma yanada kyau kowace al’umma tasanni yanayin yadda ta taimakawa matasanta hakan ne ke taimakawa wajen samun cigaba a yankin.

To kamar yadda a kullum ake samun cigaba abubuwa sabbi kullum suna kara fitowa munyi dubi akan wasu muhimman da suke taka rawa da matashi Yakamata ya sani wanda zasu taimake sa.

Abubuwan masu mahimmanci ga matasa

Muhimman Abubuwa ga Matasa

Yanayin da duniya take tafiya a yanzu tana cigaba da sauri kuma akwai abubuwa na zamani da suke yawan shigowa suna canza rayuwar al’umma na daga cikin wasu dake taka rawa a matasa wanda kowane matasa Yakamata ya sani kamar haka:

  • Ilimi
  • Sana’a
  • Kulla alaka da mutane

Wadannan abubuwan da muka ambata zamuyi bayaninsu yadda za’a fahimcesu da yadda suke taka rawa.

Ilimi

Ilimi Dukansu samunsa yanada mahimmanci matuka ga kowane matashi kuma ma shiyasa ake cemasa gishirin rayuwa samun fahimtar yadda ake karatu da rubutu yana taimakawa sosai musamman yadda yanzu da wannan mutum na iya amfani da shi domin duba wani abu a internet wanda yakan iya zamar mashi sana’a.

Sanun ilimin Matasa

Sana’a

Zama babu sana’a hadari ne ga rayuwar matashi dole a tashi a nemi abunyi Musamman ga wanda ya gama karatu koma wanda yake yi, yanzu internet tazo da abubuwa da yawa da suke sa cikin karamin lokaci mutum ya samu abun dogaro da Kai kamar su

  • Saida Digital Products
  • Freelancing aikin internet
  • Saida kaya online
  • Hada class ko courses na koyar da mutane wani abu
  • Crypto currency

Wadannan abubuwan da muka ambata da ma wasu masu kama da su duk ana amfani da su a samu kudi sosai a internet to amma in kanayinsu yakama ka san wannan abun na gaba shima.

Kulla Alaka da Mutane

Samun alaka ko yawan mutane yana taimakawa kasuwanci sosai saboda wani mai karin magana yana cewa yawan network dinka yawan kuɗin ka.