Skip to content
Home » Yadda ake hada dilka

Yadda ake hada dilka

Dilka dai wani abune nagyaran jiki wanda mata keyinshi musanman ma amare.

Dominko duk macenda keyin dilka ba dai-dai take da wadda batayiba, domin ita dilka tana gyara jikin mace ta tsaftaceshi sosai ba tare da tabar wani dattiba.

Idan zaki hada dilka yar’uwa ana bukatar ki tanadi kayan hadi kamar haka:

Kayan hadin

  • Madarar ruwa
  • Kwai 2
  • Kurkur
  • Lalle
  • Madarar turare
  • Humra
  • Madarar gari
  • Ruwa

Yadda ake hadawa

Zaki samu kwai guda biyu kifasashi kidebe yalo din zagayen dake cikinshi domin ba’a bukatarshi sai ki juye farin ruwan acikin kwano.

Sannan kisamu madarar ruwa ki zuba acikin farin kwan, madarar gari teaspoon ukku, madarar turare kadan, ruwa kadan.

Sai kisamu lalle cokali ukku ki zuba aciki kimotse, sannan ki shafema jikinki shi duka ko ina.

Bayan kin gama shafawa duka sai ki zauna yayi tsawon awanni biyu sana ki wanke.