Skip to content
Home » Yadda ake ice-cream na kwakwa

Yadda ake ice-cream na kwakwa

Toh a yau zamu koya maku yadda zakuyi ice-cream na kwakwa mai dadin gaske, Wanda zakiyishi dakanki uwargida base kinje kinsiyoba sede kiyi lokacinda kike da bukata.

Amma dafarko zaki fara tanadar Kayan hadinki wadanda ake bukata kamar haka:

Kayan hadin

  • Kwakwa guda 1
  • Madarar ruwa guda 1
  • Madarar gari cokali 2
  • Butter teaspoon daya 1
  • Flavor
  • Suga yadda kike bukata

Yadda ake hadawa

Kisamu kwakwarki ki fasata kijuye ruwan cikinta ki ajiye a gefe ki kankare bakin dake bayanta ki gurzata awurin kananan huji (greater).

Ajiye a gefe kifasa madarar ruwanki ki juyeta acikin tukunya kidama madaran garinki da ruwan kwakwa amma ba dukaba domin ruwan sunyi yawa.

Sai kijuye acikin tukunya ki dora saman wuta kijuye botarki, flavor tare da suganki kibarta ta tafasa.

Toh idan ya tafasa sai ki juyeshi acikin gurzazzar kwakwarki kimotsa ki rufe.

Sai kisa a firij idan yafara kankara sai ayanka asha.