Skip to content
Home ┬╗ Yadda ake wainar alkama

Yadda ake wainar alkama

Wainar alkama wainace mai dadin gaske musamman ma idan Wanda ya iyata yayita wato Wanda yasan makamar girki kenan.

Awajen yin wannan wainar muna bukatar kayan hadinta kamar haka

Kayan had

  • Alkama
  • Farar shinkafa
  • Yeast
  • Gishiri
  • Sugar
  • Baking powder

Yadda ake hadawa

Kisamu shinkafarki kijikata idan tajiku sai ki wanke sannan kibada a markado maki ita da daddare yadda zaki barta ta kwana zuwa safe.

Da safe sai ki samu alkamarki mai kyau nukakka kitankadeta ki zuba baking powder, yeast, gishiri kadan da dan suga idan kinada ra’ayi.

Sai ki kwabashi kamar kullun wainar shinkafa.

Idan kika gama sai ki kawo kullun shinkafarnan naki kadan Kar yakai yawan na alkamar ki zuba aciki kimotse.

Sai ki barshi ya taso sannan sai ki soya.

Idan sauran kullun shinkafarki yarage zaki iya yin sunasir dashi.