Skip to content
Home » Yadda ake yam balls (kwallayen doya)

Yadda ake yam balls (kwallayen doya)

A yau zamu koyi yadda ake yam balls wato kwallayen doya, to uwar gida komade ba’a fada maki ba kinsan made wannan kalan abinci zaiyi dadi sosai.

Musamman ma idan wajen yinshi kinkara da fasa harki ta iya girki.

To uwargida idan zakiyi yam balls anason kitanadi Kayan hadi kamar haka:

Kayan hadin

  • Doya
  • Kwai
  • Mai
  • Nama
  • Albasa
  • Attarugu
  • Magi
  • Gishiri

Yadda akeyi

Dafarko zaki fere doyarki ki wanketa ki zuba a tukunya ki dafa, bayan ta nuna sai ki sauke ki tace ruwan ki ajiye dayar a gefe.

Ki yayyanka albasarki da attarugu ki zuba a turmi ki daka, sannan ki zuba magi da gishiri a ciki kadan kidaka.

Sannan kidinga debo dafaffar doyarki kina dakawa sama-sama zakiyi dakan doyar.

Idan ta daku sai ki juye a kwano ki dauko namanki ki zuba aciki, idan gishiri bai jiba sai ki kara kimotse

Kisani Shima fa naman dazaki zuba bawai tsokoki zakisaba a’a sulalalle Wanda aka daka.

Kidinga debowa kamar cubrin hannu kina mulmulawa kina tsomawa acikin kadadden ruwan kwai kina soyawa a mai.

To idan kikaga yayi brown ya soyu kenan sai ki tsame.