Skip to content
Home ┬╗ Dabarun girki

Dabarun girki

To anade tacewa ki iya girki-girki de, to baki kasa a guiwa ba dai kin koyi girki kin iya harma kin kusa kwarewa a ciki, amma kuma idan wata matsala kadan ta kamaki acikin abicin da kike girkawa bakisan dabarar da zaki ki magance wannan matsalaba.

To uwargida tabbas da sauranki domin yakamata kisan dabaru kala-kala a wajen girkinki domin magance bacinshi watarana.

Ayau zamu koya maku wasu daga cikin dabarun girki wadan da sune;

Dabarun:

1) idan kwari na damunki cikin kicin sai ki samu kokumba bawonta bayan kin fare ki zuba duk wajen da kikaga kwarin.

2) idan kina yanka albasa mai yaji kuma yajin yadameki to abunda zaki shine kiringa tauna cingam.

3) idan zakiyi amfani da kanwa to ba’a lokacin zaki jikata ba, zaki jikatane ta kwana yadda zata narke sosai, idan ma da sansone kijikata dayawa kitace a cikin wuri mai marfi sai ki rika amfani da ita duk lokacin da kike da bukatarta saboda gudun kasa.

4) idan kina dafa shinkafa sai tafara konewa to ki samu biredi kidaura asaman shinkafar yayi tsawon minti biyar ko goma.

5) idan zakiyi kwabin fulawa to kiri kayi da ruwan dumi amma ba masu zafiba saboda masu zafi sosai na kashe karfin yis.

6) idan kina da lemun tsami ko na zaki kina bukatar amfani da ruwansu amma basuda ruwa to sai ki samu ruwan zafi ki sasu aciki kibarsu suyi kamar tsawon awa daya sai ki matse.

7) idan kina dafa kwai kuma bakiso yafashe to ki barbada gishiri kadan a cikin ruwan dahuwar kwan.

8) idan kina aiki da gas to karki jeda waya a wurin domin hakan ka iya sa gobara sosai.

9) karki markada cefane idan ba’a lokacin zaki amfani dashi ba, domin zai tsinke kuma zai yi tsami sosai.

10) idan cefanenki yayi tsami to sai ki jika kanwa ki zuba a ciki ko bekin foda.

11) idan zaki amfani da kayan lanbu to kiwankesu sosai kafin kiyi amfani dasu, misali; idan zakiyi amfani da alayyahu ko latas to anfiso ki fara wankesu domin dattinsu yafita baki daya sannan idan kin gama ma haka.

12) to idan kina girki sai tashshi yayi yawa aciki to abunda zaki shine sai ki markada tumatur ki zuba aciki zai tsotse yajin.