Skip to content
Home ┬╗ Yadda zaka riga yin transfer na katin MTN zuwa MTN cikin hanya mai sauki

Yadda zaka riga yin transfer na katin MTN zuwa MTN cikin hanya mai sauki

    

     Assalamu alaikum jama’a to kamar yadda aka saba a wannan website mai albarka wadda take da address din hausawasite.com.ng mun saba kawo maku post masu amfani, to a yau ma inshallahu zamu  yi magana ne akan yadda zaka tura ko transfer na katin mtn zuwa yan uwa da abokan arziki ko ma duk wanda yake so imma sai da mai zakai ko kyauta.


      To idan kana son turama wani katin mtn daga cikin kudin mtn din ka ya kamata ka san cewar a kwai wani tsari wanda kamfanini MTN ya samar domin yon irin wadannan aikace aikacen wanda suna shi share “N” sell wanda zakai amfani dashi domin turama wani mai mtn kudi.

      Shidai wannan tsarin MTN sun tabbatar da cewar idan kana amfani da shi zaka yi amfani ne da wasu pin domin tura kati ga wanda kake son turamawa, wanda kana iya tura kudi har zuwa kusan N10,000 .

     To kafin ka fara tura katin zuwa wani ana son ka canza pin dinka wanda ke asali wanda shine 0000 na kowa a asali haka yake bayan ka canza ne zaka samu damar turawa, to bari mu je ga matakan da zaka bi wajen turawa.

         Matakan da zaka tura katin da kuma  yadda zaka canza pin dinka na Asaali
Ga su kamar haka:

1. Dafarko dai zaka canza pin din Asali wato 0000 zuwa wadda kake so ka sa wadda itama harafi hudu ce misali 1023 ( a wannnan matakin zaka yi tunanin pin din da zaka sa ne).

2. A mataki na biyu kuma sai ka tura sako zuwa 777 da pin din da kake son sawa misali 0000 1023 1023, bayan ka tura ma  777  to indai yayi daidai zaka ga sakon yayi lafiya lau daga MTN.

ko kuma kana iya amfani da hanyar kiran amadadin  kayi message di shi kuma haka zakai misali ka kira *600*0000*1023*1023#.

     ka kula da cewar nan na yi mafani ne da 1023 a matsayin sabuwar pin ita kuma 0000 tsohuwar pin misali.
    
    To yanzu ka canza pin sauran abunda ya rage ka fara turama mutanen da kake son turamawa, idan zaka tura ma wani misali naira 1000 sai ka kira 
*600*09037157675*1000*1023#, da zaran ka tura ya shiga za’a turo ma message cewa yayi.

     To Alhamdulillah wanda ke da tambaya yayi a comment section kada ku manta ku cigaba da kasancewa da www.hausawasite.com.ng domin samun post masu amfani mungode.