You are currently viewing Yadda ake Samun Kudi da Affiliate Marketing

Yadda ake Samun Kudi da Affiliate Marketing

Zakaji a online ana ta cewa ana samun kudi da irin wannan kasuwanci na affliate ka zo ka koya, tabbas abu ne mai kyau kuma ana samun kudi da shi kwarai da gaske shiyasa a yau mukayi rubutu akan shi amma da farko mi ake cema affliate marketing?

Minene Affiliate Marketing?

Tallace-tallacen haɗin gwiwa ko affliate marketing a turance  dabara ce ta tushen talla inda kasuwanci ke ba da lada ɗaya ko fiye masu alaƙa ga kowane baƙo ko abokin ciniki wanda ƙoƙarin tallan haɗin gwiwar ya kawo.

A cikin sauƙi, hanya ce ta tallata kayan mutane ko kamfanoni (abokan haɗin gwiwa) don samun commission wato wani kaso  ta hanyar haɓaka samfuran haja ko sabis na wasu kamfanoni.

Yadda Affliate Marketing Yake

Kamar dai yadda nayi bayani a baya wannan kasuwanci kamar kowane kasuwanci ne yadda kuma yake shine mutum zai yi register ko ya hada kai da mai sana’a ko kamfani don tallata masu hajar su.

Idan kamfanin ya yarda zai bashi kamashon ko wani yanki na kason ribar duk abu daya ko yanayin yadda aka tsara duk idan ya saida haja yadda za’a ba shi.

Shi wanda ya hada gwiwar da kamfanin zai je ne ya nemo refeeral wato mutane da zasu saya ko su yi register ga kamfanin duk idan aka saya ta hanyarsa zai samu wannan kamashon.

Affliate marketing kala-kala ne amma ga wandanda yanzuu duniya ta fi amfani da su kamar haka wanda ake samun kudi da su

Nau’in Affliate Marketing

Akwai nau’ikan shirye-shiryen tallan haɗin gwiwa suna da yawa kuma kowanne yana da halayensa da fa’idodinsa. Ga wasu nau’ikan gama gari  wanda ake fi yawan yin su kamar haka

  • Pay-Per-Sale (PPS) =>Biya-Kowane-Sale (PPS)
  • Pay-Per-Lead (PPL)=>Biyan-Kowane-Jagora (PPL)
  • Pay-Per-Click (PPC)=>Biyan-Kan-kowane dannawa (PPC)

Akwai nau’in affliate da yawa amma wadannan amfi yawan amfani da su yawanci yanzu tunda a zamanin Digital muke link dinda aka ba mutun a wajen register duk idan wanda ka tura mawa yayi wani abu za;a biyaka ya danganta da irin tsarin da muka ambata a sama da kuma suke biya

Yadda ake Farawa

Domin fara wannan kasuwanci yana bukatar ka mallaki ko ka san yadda zaka hada wadannan abubuwa kamar haka wanda su zasu taimaka maka wajen saurin saida haja ko sabis dinda ka amso daga kamfanin

Mataki na Farko Zabi Rukuni

Zaɓi wurin da kuke sha’awar ko kuma kake  da masaniya a ciki. Yana da sauƙin haɓaka samfura ko sabis waɗanda ka fahimta kuma ka yi imani da su domin ta nan ne zaka yi saurin saida hajar misali kana fannin gurki ko kana fannin computer kana da class a whatsapp

Mataki na Biyu Shirya Haɗin gwiwar

Nemo Afflite programe dinda kake son jonawa ko farawa wanda kana iya bincikawa online ko kuma ta  tuntuɓar kamfanoni kai tsaye waɗanda samfuran / ayyuka kuke son haɓakawa.

Yi la’akari da abubuwan da suke saidawa kuma wane programe suke yi cikin wadanda muka ambata a sama, daga nan sai ka yi register ka samu referal link dinka ka fara watsawa a kafafen sada zumunta dinka ko kuma a Youtube Channel ko duk wata kafar da kake ganin za’a a iya saye abun ko tuntuba.

yadda zaka fara tsara kasuwanci

Gina Dandali

Ƙirƙiri dandamali inda za ku iya inganta samfurori / ayyuka masu alaƙa. Wannan na iya zama blog, shafin yanar gizo, tashar YouTube, bayanan kafofin watsa labarun, wasiƙar imel, da sauransu. Tabbatar cewa dandalin ku yana ba da abun ciki mai mahimmanci don jawo hankalin masu sauraron ku.

Karanta: KAFAFEN SADA ZUMUNTA: CIKAKKEN BAYANI GAME DA SU

 Ƙirƙirar Content mai kyau

Samar da ingantaccen abun ciki mai alaƙa kuma mai ma’ana wanda zai iya jan wanda ya zo ya sayi wani abu idan aka yi mashi talla a ciki.

A turance shi ake cema content marketing mutum zai dora abu mai amfani sai ya yi tallan abun da zai taimaka ma mutane a ciki.

Samun Traffic (Drive Traffic)

Anan ana amfani da abubuwa masu amfanin da aka dora video ko rubuce-rubuce domin jan hankalin masu shigowa, amfani da dabarun talla daban-daban don fitar da zirga-zirga zuwa dandalin.

Wannan na iya haɗawa da SEO, tallan kafofin watsa labarun, tallan abun ciki, tallan da aka biya, da sauransu.

Maida Masu Shigowa zuwa masu saye

Daga nan kuma a mataki na Kasrhe shine ƙoƙrin maida waɗanda suka shigo zuwa customers waɗanda zasu sayi hajar ta hanyar sanbya link din da aka baka domin su shiga su sayi abun to ta nan ne zaka samu commisuion kason da ake magana

Karanta:

YADDA AKE FARA KASUWANCI

Business Plan: Yadda ake Tsara Kasuwanci

 Muhimmancin Talla da Kuma Gudummuwar da ta ke ba Kasuwanci

Kammalawa

Affliate marketing dai abu ne wanda yake bukatar nastuwa kuma yake son ka fahimci abubuwa kamar haka ana son ka yi promoting ko ka taimaka a saida wani abu wanda daga ne zaka samu kaashon ka inka tallata aka saya ta hanyar link dinka ko ta hanyar ka a takaice.