Skip to content
Home » KAFAFEN SADA ZUMUNTA: CIKAKKEN BAYANI GAME DA SU

KAFAFEN SADA ZUMUNTA: CIKAKKEN BAYANI GAME DA SU

Kafafen sada zumunta suna daya daga cikin muhimman wurare da ke taka rawa a rayuwar al’ummar wannan zamanin musamman matasa saboda yanayin yadda suka sauya yanayin rayuwar mutane dayawa ta hanyar basu kaso mai tsoka na lokaci.

Ayau inshallahu zamuyi duba akan muhimman abubuwan da suke kunshe a ciki tare da duban mutane mi ke kai su a ciki kuma wace dama ta kasuwanci, ilimi ko habbakar tattalin arziki kafafen sada zumunta take ba mutane da ya kamata suci moriyarta.

Mi ake nufi da Kafar Sada Zumunta?

Kafafen Sada Zumunta dandalin kimiyya ne da ke ba mutane damar hada abubuwa masu wanda suka kunshi ra’yoyi, yadda, tunanin, shawarwari masu amfani domin watsawa ga alumma domin su amfana a kuma dayan bangaren Kafar Sada Zumunta wani dandali ne da mutena da dama suke amfani da shi domin gaisawa ta hanyar sakonnin rubutu, sauti ko kuma bidiyoyi daga wuri zuwa wani wuro ko daga wata kasa zuwa wata kasa ta hanyar fasahar yanar gizo.

A baya sai mutum yayi tattaki har zuwa inda danuwanshi yake musamman ma lokacinda babu waya sannan zasu iya gaisawa zuwan waya ya sauya wannan fasalin inda daga nan ne kuma aka samu cigaba na shigowar kafafen sada zumunta wanda ya canza yanayin labarin gabakidaya inda ana iya yin zumunci ta hanyar sakonni, sauti koma video ana ganin mutum.

Takaitaccen Tarihin Kafafen Sada Zumunta

Kafafen Sada Zumnta sun saiko asali ne tun farko zuwan computer a shekarar 1960 inda wata jami’a d ake kira da University of Illious dake Amuruka ta hada wani abu da ake kira da PLATO System da yake ba jami’anta damar tura sakonni hada rubuce-rubuce da sauransu.

Daga nan kuma cigaba bai tsaya a nan ba kawai an ta samun ire-irensu amma yanayin labari ya canza a yan shekarun1990san samu wasu daga cikin kafafen sada zumunta kamar su SixDegress.com, GeoCities da Classmates.

Inda bayan nan cigaba ya cigaba da tafiya a shekarin 2000s inda yanayin fasalin kafafen sada zumunta ya sauya saboda yadda ake samu bullowara kafafen sada zumunta kamar su Facebook a 2004 wanda Mark zukerberg y kirkira, sai irinsu YouTUbe a 2006 inda sauran suka kunshi twitter, instagram da sauransu

A shekarar 2015 masana sunyi hasashen cewar mutanen duniya suna bata kusan kashi 22% na lokuttan su akan kafafen sada zumunbta wanda hakan ya nuna karfin da kafafen sada zumunta sukayi da kuma yadda sukayi suna a fadin duniya baki daya.

Jerin Manyan Kafafen Sada Zumunta da Muke da su a Yau

Idan mukayi magana akan kafafen sada zumunta kusan yanzu kowa zai fahimci cewar akwai wadanda sunyi suna sosai an sansu wanda idan ka samu followers da yawa ba karamin jari bane saboda misali kana iya samun mutum fiye da Million Daya kaga ko haja ka sa indai mai kyau ce ya kake tunanin mutum nawa zai saya wannan ga yan kasuwa kenan.

Ga dai wasu daga cikin sanannun da aka fi amfani da su kuma duniya tafi rakja’a ko tafiu maida hankali akansu kamar haka:-

  1. Facebook
  2. Tiktok
  3. Instagram
  4. Whatsapp
  5. Twitter
  6. Linkedin
  7. Printerest
  8. Snapchat

Karanta: 

Yadda Zaka Hada Facebook Page Don Habbaka Kasuwancinka

Hanyoyin Samun Kudi a Tiktok

Mike Kai Mutane Kafar Sada Zumunta

Yana dauya daga cikin abu mai mahimmanci da ya kamata ka sani shine cewar mi yake kai mutane a kafafen sada zumunta ta kuma wace ghanya ya kamata a ci ribar wadannan dumbin mutane masu yawa haka wanda duk wanda yazo yana neman wani abu ne cikin wadannan abubuwa daga su ba sauransu:

  • Kasuwanci
  • Labarai
  • Nishadi
  • Karatu
  • Zumunta

Amfanin Tare Mabiya a Kafafen Sada Zumunta

Kafafen sada zumunta wurere ne da mutane bila adadin suke kuma kaga duk wurin da akace akwai mutane to yana da daraja kenan kuma tara mabiya yana taimaka ma mutum sosai ta hanyoyi kamar haka:-

  • Kasuwanci
  • Samun lada
  • Suna
  • Girmamawa da Mutuntawa

Muhimman Abubuwa da Ke sa Ake Samun Mabiya Masu yawa

Samun mabiya masu yawa kamar yadda muka ambata yana da matukar amfani sosai musamman ma ga yan kasuwa, maruba ko malamai, to sai dai yana da kyau ka san cewa wadanne hanyoyi ne ake bi ake samun mabiya masu yawa a kafafen sada zumta saboda wasu zasu dade a dandalin amma mabiya yan kadan wasu kuma basu dade ba kaga sun tara da yawa wasu kuma sun dade kuma ga mabiya masu yawa kamar.

To kamar dai yadda na ambata mabiya kamar jari ne a ko da yaushe kuma ga wasu muhimman abubuwan dasu ke sa mutene su bi ka kamar haka kuma ka tara da yawa.

  1. Watsa Abu Mai Jan Hankali
  2. Watsa Abubuwa masu Inganci da sahihanci
  3. Yawan Samun Hudda Tsakanin mabiya
  4. Tallar Shafin
  5. Dadewa a Kafar

Karanta:

Forex Trade: Bayanin Forex Trade da Yadda ake yinsa

Yadda ake samu kudi ta Hanyar Referral Mobile App Referral Marketing

Kammalawa

ya ishi mutum mai hanakali ya tsaya yayi tunaniu ya amfana da waddannan kafafe saboda yanzu haka maganar da ake yi akwai mutanen da a nan suke samun wuraren da suke cin abinci suke samun kudade masu yawa, wasu kuma kasuwancinsu yake kawomasu wasu kuma talla akwai damammaki da yawa a kafafen sada zumunta.