You are currently viewing Yadda ake samu kudi ta Hanyar Referral Mobile App Referral Marketing

Yadda ake samu kudi ta Hanyar Referral Mobile App Referral Marketing

Yadda zaka samu kudi ta hanyar referral

Harkar internet ko yaushe dabarun ka ne zasu cece ka wani nazari da nayi akan mobile App referral marketing yasa na fahimci cewa hanyar mai ɓillewa ce matuƙar Mutum yanaso zata iya zama hanyar samun kuɗin sa SBD ni ganau ne ba jiyau ba.

Menene mobile App referral marketing?

wani tsarin gudanar da internet task ne kuma mutum ya dinga samun kuɗaɗen sa da shi, sannan kuma gwargwadon binciken mutum da aikin sa gwargwadon yadda zai samu kuɗi.
Yadda akeyi shine refering ɗin mutane zuwa ga wasu mobile apps ta hanyar amfani da referral code/link ɗinka bayan mutum yayi rijistar application ɗin da farko.

Samun kuɗi ta App referral marketing

kamar yadda muka sani application ɗin da ake ɗaurawa a playstore ko App store kala kala ne kamar su:

1. Dependant commercial app

2. Ads monetisation app (total free app)

3. Premium-part app(partially free)

4. Direct monetisation app. Dss

Acikin wannan jerin apps ɗin guda biyu ne akafi amfani da su a harkar mobile App referral marketing Amma dafarko nasan mutane zasu so sanin bayanin kowane ataƙaice;

1. Dependant commercial app

application irin na bankuna, makarantu, ko application na saida data wanda shi dama ana buƙatar ne ayi amfani da shi dan wani dalili na kasuwanci kamar mai saida data daman haka yakeso ayi amfani da app ɗinsa dan haka baze saka kuɗin download ko na subscription ba.

2. Ads monetisation app (total free app);

shikuma wannan application ɗin kyauta ne daman dan haka kamfanin sa basa buƙatar biyan kuɗi ga wanda zeyi musu referral suma suna samun kuɗaɗen su ne a wannan App ɗin ta hanyar tallace tallace da suke sakawa shiyasa zakuga galibin application sunada yawan jefo muku talla kamar “in streaming ads” na YouTube to ta wannan tallan suke samun kuɗaɗen su sai kuma suna tallata kansu kuma baza’a rasa su da premium app ba koda ba Irin wannan ba.

3. Premium-part app(partially free)

shikuma application ne da rabin sa ana iya amfani da shi kyauta rabin sa kuma ana biya ne wato sai anbiya kuɗi za’a iya unlock na wasu features ɗin wato amfanin da za’a iya yi dashi misali idan application ɗin yana taimakawa ne wajen design to zai ware wasu ɓangarori na design da sukafi inganci yace sai anyi unlock kafin a iya amfani da su kuma unlock ɗin shine biyan kuɗi to SBD suma suna samun kuɗaɗen su ne ta wannan hanyar shiyasa suke biyan duk wanda yayi refering ɗin wani zuwa ga application ɗin su.

4. Direct monetisation app: shikuma Kai

tsaye application ne da tun farkon sa ma baze buɗe ba sai anbiya kuɗi wato daman kai tsaye sunyi shi dan samun kuɗaɗen shiga na kai tsaye ba wani inda-inda SBD haka kasuwa suka fito duk wanda zai musu talla zasu biya shi.

Menene referral?

Referral abune me sauƙin fahimta shine kawai a nemo mutane suyi rijistar wannan application ɗin su yi amfani da shi to me zai sa a gano cewa wannan mutanen kai ne ka nemo su? ta hanyar referral code ko link SBD a lokacin da kayi download ɗin wannan application ɗin kayi rijista da shi zasu bayar da referral code ɗin sannan kuma zasu faɗi abunda zasu biya ga duk mutum ɗaya da yayi amfani da wannan code ɗin yayi rijista.

Tayaya za’a iya fara wannan kasuwanci?

Nafarko kamar yadda na faɗa shine binciken application ɗin a playstore ko App store dakuma App description ta yadda za’a san yadda application yake aiki da kuma irin yadda zeyi amfani ya taimakawa mutane wajen wasu ayyukan su to abu na farko shine mutum ya lura cewa application ɗin zeyi amfani sosai ga mutane dan haka zeyi farin jini na biyu kuma ya zama cewa mutum ya lura application ɗin suna biyan referral commission mai ɗan gwaɓi misali wasu suna biyan $2 wasu kuma $10 ga duk mutum ɗaya da aka kawo musu abu na gaba dole ne mutum ya iya amfani da Application ɗin kuma ta gwada SBD yadda zai nunawa mutane komai sannan kuma ɗaya daga cikin hanyar da ake ƙara samun tabbaci akan application itace a bibiyi comments na mutane akan application ɗin a playstore ko App store ta nan ne hanya mafi sauƙi wajen a gane ingancin application da ma sauran wasu bayanai kuma tanan ma za’a iya tuntuɓar support team na application ɗin dan samun ƙarin bayani ko kuma ƙulla alaƙar referral ɗin.

Abun lura shine koda anyi referral ɗin an tara kuɗin dole sai anyi amfani da wani foreign wallet Kamar irin su PayPal ko Payoneer da makamantansu Kafin a iya dawo da kuɗin cikin account ɗin mu na gida wato Naira account sannan kuma dafarko mutum ya fahimci hanyoyin da suke biya kafin ya fara abu na ƙarshe shine mutum yayi bincike sosai akan cewa application ɗin suna biyan referral ko basa biya kuma abune me sauƙin gaske a iya yin magana da su ta email ba kamar yadda muka saba bane a Nigeria wasu ɓangarori da dama basa iya amsa tambayoyin kwastoma su ko yaushe suna nan wani lokacin robot ne zai saurari mutum wani lokacin mutum ne mai jini ba robot ba.

Ba kawai a application bane ake iya yin wannan harkar ta referral amma de a yanzu nayi magana ne akan application ɗin kaɗai.