You are currently viewing Hanyoyin Samun Kudi a Tiktok

Hanyoyin Samun Kudi a Tiktok

Hanyoyin samun kuɗi atiktok:
Manhajar Tiktok ba wajen fitsara bace kaɗai wadda zaku ga mata na ɗora videos aTiktok?
Idai zaka yi kokarin karanta wannan rubutun to zaka gano yadda zaka samu kudi da tiktok.
Tsaya kaji hanyoyin samun kuɗi a Tiktok wanda baka sani ba;
Dafarko menene Tiktok?
Tiktok social media platform ne wanda yafito daga ƙasar China wanda akafi sani da Douyin a ƙasar ta China, Tiktok mallakin bytedance ne wani shahararren kamfani a china ankafa kamfanin tare da samar da manhajar Tiktok a Watan Disambar 2016, manhajar de tafi maida hankali ne akan kaiwa da komowa na ƙananan bidiyo daga sakwan 15 zuwa mintina 15 wacce galibin matasa suka karɓe ta saboda yadda tazo da abubuwa sababbi na nishaɗi.
a wannan darasin zan kawo wasu hanyoyi ne kaɗan na samun kuɗi a Tiktok locally wato ta hanyar improvisation.

1.Kasuwancin Affiliate a Tiktok;

Ba’a buƙatar wani ƙayyadadden tarin ko yawan followers a Tiktok domin fara wannan kasuwancin.
dafarko menene kasuwancin Affiliation?
Kasuwancin Affiliation yana nufin tallata kasuwanci da kamfanonin wasu ta hanyar amfani da Link Ɗin da suka bayar (affiliation link) domin tallata wannan kasuwancin dazaran anyi amfani da affiliation link ɗin mutum an siya wannan Kayan ko anbuƙaci wannan aikin to zasu adanawa Mutum kuɗin daya samu wanda daga ƙarshe kuma mutum za iya cire kuɗin sa in yakai wani adadi gwargwadon irin affiliation ɗin dayake amfani dashi.
Misalin kamfanonin da za’a iya kasuwancin affiliation dasu daga ciki akwai: Babbar kasuwar duniya ta Amazon, Jumia affiliation program, konga affiliation program, da Alibaba express affiliation program dss.

  1. Hanyoyin samun kudi a tiktok

2. Sayar Da Kayayyaki a Tiktok

kamar sauran social media platform irin su facebook, WHATSAPP da Instagram da kuma twitter wuri ne na tallata harkokin kasuwanci wanda suka haɗar da digital Product, digital services, da non digital Product and services duba da cewa dubban miliyoyin mutane ne ke amfani da shafin domin nishaɗantuwa da abubuwan da ake wallafawa daban-daban wannan babbar hanya ce ta amfani da gajerun bidiyo domin tallata kasuwanci da yaɗa manufofi manufofin kasuwanci.

3.Dillacin Tiktok Account;

Hada-hadar siyar da Tiktok Account tayi shura yanzu kamar masu dillacin gidaje ne a zahiri wannan sune akeyiwa laƙabi da “digital estate agent” wato masu ƙoƙarin nemowa mai neman Tiktok Account mai mabiya dayawa dafarko za’a tambaye shi mai mabiya nawa yakeso? Sai kuma a bazama nemo masa hakama ga wanda yakeson siyar da nashi Tiktok Account Ɗin zai garzayo ne wajen dillalin yace masa yanada account mai adadin mabiya kaza yanaso zai siyar haka nan ma zai bazama nemo mai siye kuma shima abashi kason shi gwargwadon yadda aka tsara yarjejeniyar kasuwancin bisa yadda aka kulla a yanzu anata hada-hadar ƙulla irin wannan cinikayyar a Tiktok

4.Tiktok sponsored Post;

wannan ɓangaren kuma ya ƙunshi Local sponsorship da Advance sponsorship.

Dafarko menene Tiktok sponsored Post?

Tiktok sponsored Post shine karɓar talla na kai tsaye daga wajen masu siyar da Wasu abubuwa (merchandise) ko masu yin wasu ayyuka (services) ko tallata harkokin wani kamfani ko yaɗa wasu manufofi, Locally wato direct daga Masu buƙatar ayi musu posting ɗin na gida kokuma Manyan kamfanoni a faɗin duniya.

a Tiktok sponsored Post ana matuƙar samun kuɗi abun buƙatar shine yawan mabiya a ƙalla 50k zuwa sama

5.Tiktok Media Licensing;

Menene Tiktok Media Licensing?

Wani salon talla ne da kamfanoni ke neman izinin amfani da videos Ɗin da Tiktoker ya wallafa a account ɗinsa suna amfani da wannan creative Ɗin domin sanya tallukan su aciki gwargwadon yawan mabiya gwargwadon yawan samun irin wannan damar a Tiktok abunda ake buƙata shine ƙirƙirar sababbin videos da samun Followers

6.Tiktok Creator Fund

Domin samun kuɗi a Tiktok Creator Fund sai ancika sharuɗɗa kamar haka:

Shekara 18 ga me account ɗin

10k Followers

video da’aka wallafa a ƙasa da kwanaki 30 ya samu 100k Viewers

Dole video Ɗin yacika sharuɗan ɗora Video na Tiktok

Da wannan tsarin ana matuƙar samun kuɗi a Tiktok wanda zanyi rubutu na musamman akan yadda ake amfani dashi ga wanda suke da Followers 10k Kuma a shawar ce in kuna sha’awar Digital Entrepreneurship zaku iya siyan Tiktok account me 10k Followers Ɗin.

7.Tiktok Account Manager

Wani Ɓangare ne na Social Media Management (SMM) a Tiktok account manager ana neman ƙwararru masu ƙwarewar iya sarrafa Tiktok Account wajen kasuwanci sai abasu ragamar amfani da Tiktok Account na wani kamfani ko wata masana’anta ko wasu mashahuran mutane da ke gudanar da wasu abubuwa a Tiktok

8.Tiktok Video Editor/ virtual Editor

sanin kowa manhajar Tiktok kacokan ta maida hankali ne akan ɗora video masu ƙayatarwa hakan yasamar da ƙwararru dasuka iya video editing dake aiki domin tacewa da gyara Video kafin a ɗora Wanda dayawa videos da ake ɗorawa na tallace-tallace a Tiktok sune suke editing ɗinsu kuma su tsara su yadda zasu dace tare da jan hankali a Tiktok ba kawai Video editing suke ba suna kuma video creation domin tsara talla kamar irin su jingle ta hanyar amfani da hotuna a mayar dashi video dss

9.Tiktok Like da Comments

itama manhajar Tiktok tabi sahun wasu takwarorin ta na biyan kuɗi ga Masu mabiya da yawa a shafin waɗanda suke samun comments da liking a posting ɗinsu domin ratsa talla aciki a wannan tsarin Tiktok tana biyan kuɗaɗe gwargwadon yawan liking da comments a yawan posting.

Haƙiƙa manhajar Tiktok na sahun gaba cikin Social Media platform dasuke da hanyoyin samun kuɗi dayawa wannan kaɗan ne na tsakur