Skip to content
Home » Kafafen Sada Zumuntar Zamani(Social Media) da Yadda ake samun kudi da su

Kafafen Sada Zumuntar Zamani(Social Media) da Yadda ake samun kudi da su

Kafafen Sada Zumunta wada ake kira da social media a turance suna matukar taka rawa  arayuwar dan adanm ta yau da kullun kama daga fannonin addini, karatuttuka, sana’oi, kasuwanci. kiwon lafiya da sauran harkokin da dan adam yake gudanarwa.

A cikin wannan post din namu na yau zamuyi magana ne akan yadda ake hanyoyin da ake samun kudi da su bayan tsakulo manya ko kuma sanannu daga cikin tare da yin sharhi akan abubuwan da ya shafe su.

Mi ake nufi da kafar sada zumuntar zamani. kuma ya Dunaya ta samu cigaba a fanninsu?

Kafafen sada zumuntar zamani wasu shafukan yanar gizo ne wanda ya zama matattara ta mutane da yawa inda suke kokarin yada abubuwa kala daban dabam kama daga karatuttuka, kasuwanci, al’adu da kuma harkoki rayuwa.

Kafafen sada zumunta social media

A da bau irinsu ace zaka shiga wani wuri da zai hada ka da mutanen duniya amma a yanzu an same su ta yadda kana gida saman gado kana iya magana, rubutu ko kuma daukar hoton video da wanda yake wani gari ko kuma wata a kasa a ko’ina a fadin duniya.

Cigabansu ya zo ne ta sanadiyyar cigana da aka samu na yanar gizo wato internet kuma wanda tunda a nan munfi maganar fannin samun kudi akwai abunda ake cema Digital Marketing wato samun kudi ta hanyar na’ura mai kwakwalwa.

A cikinsa ne aka samu fanni da ake kira da Social Media maeketing wato kasuwanci ta hanyar kafafen sada zumuntar zamani da muke magana akai yanzu

Wanda ta hanayr shi ce kamfanoni da kuma ma’aikatu suke watsa tallace tallace  da kuma abubuwan da ya shafi harkokin kasuwan su wanda kake gani mjusamman idan ka hau a saman su.

Karanta: Koyon Internet da Abubuwan da Suka Shafe ta

 

Wadanne Hanyoyi ne ake samun kudi da su?

Kafin nan mafi yawancin kamfanonin da suka kirkira irin wadannan kafafen sada zumuntar suna yin wasu tsare tsaren da ke taimakama yan kasuwa misa,li kamar ta hanyar hada page a facebook, store a whattapp, da sauransu.

Akwai hanyoyi da dama da ake samun kudi da su a kafafen sada zumunta wanda hanyoyin tallar kasuwanci ne ko kuma sana’a kuma gasu kamara haka.

samun kudi

karanta: Bayani game da tallar da facebook ke ma yan kasuwa da yadda zaka fara tallata hajarka

Post

Mafi akasari zakaga kamar ;post kawai dole sai kana da mutane da yawa zasu iya gani a’a ba haka abun yake bama kwata kwata ko kana da mutane idan ba active bane ko basu comment sosai to kamar facebook bai yada maka shi sosai.

Amma idan kana son post na page na kasuwancinka a yada maka shi to sai ka sayi ads yadda abun yake shine zaka biya kudi iya yanayin mutanen da kake son su watsamawa kuma iya kudinka iya shagalinka.

Video

Video kusan yanzu ita duniya ta raja’a kanta ta maye rubuta da hotuna, saboda tafi jan hankalin jama’a fiye da rubutu.

Abun lura a nan shine mafi yawancin mutane basu iya tsayawa su karance rubutun da kayi duka ba kamar bidiyo ba saboda sun san baza su sha wahala ba sosai.

Karanta: Video Coverage da Kuma Bayani akan Sana’ar

Banner

Idan mukayi magana a wannan fannin banner shine hotuna na design wanda kake watsawa donn jan hanakalin custometrs dinka ko kuma yi masu barka da wani lokaci, biki ko kuma halin da ake ciki don kara tunantar da su akan kasuwancinka.

Mafi akasari ana watsa banner a matsayin talla ce a social media saboda a kara samun cutomomi da kuma followers masu yawa na zshafin kasuwanci, nayi bayaninsu a baya kana iya duba post din da nayi bayaninsu a kasa don kara samun cikakken bayani akanta

Karanta: Yadda zaka kyara kasuwancinka da hanyar hotuna don jawo hankullan masu saye

Wasu daga cikin sanannu da yadda zaka ci moriyarsu

ga wasu daga cikin sanannun da muke da su da kuma yadda zaka fara neman kudi da su a yanayin yadda mutanen suke ciki da kuma abubuwan da suka raja’a akansu.

Linkedin

Shi wannan kafar ta linkedin yawancin amfi samun auka a ciki da zaran ka je kayi register zasu tambaye ka akan abubuwan da ka iya da kuma garinka.

samun aiki linkedin

To da zaran auka sun zo har message suke turo maka ta email idan baka online ka safka, gaskiya kusan shi anfi ma samun kudi da auka sosai saboda shi ba yan wasa a cikinsa sosai kawai don wannan aka yi sa.

Cikinsa kamfanoni suke neman wadanda zasu yi masu aiki na gida da kuma kasashen waje kayi su biya ka hakkin ka ya danganta full time ne ko kuma part-time.

Munyi post akan yadda ake samun ayyuka a kafar sada zumunta ta linkedin wanda kana iya karanta shi idan baka karanta ba domin fahimtar abun.

Karanta:  Yadda Ake Samun Aiki Online ta Hanyar Linkedin

Facebook

Facebook yana daya daga cikin baban kamfanin social media wanda yana dade ana amfani da shi, kuma kamfanoni da yan kasuwa da yawa sun dade suna tallar hajar su suna samun kudi da shi.

Akwai hanyoyin samun kudi a facebook kamar ta hanyar market place da ya bullo a kwannan nan zaka dauki hoton hajarka ka sa mata kudi kayi bayani akanta yadda mai saye zai taya.

Da ya taya zaka ga sako an turo maka akan hajar iyaka ka tura mashi idan ya turo maka kudinka.

Wasu kuma suna amfani da Facebook page ko kuma groups wajen yin posting. amma akwai wani sirri a duk wani post a facebook da zaran ana yaewaita masa comment da like to suna yawan watsa shi a gani da yawa.

Whattsapp

Wahatsapp ma yana taimakawa sosai musamman a sabon tsarin kasuwancin da suka bullo da shi mai suna Whatsapp Business domin muyan kasuwa su bude store din hajarsu.

Whatsapp Business yadda zaka samu kudi da shi shine idan kana da wata haja ko kuma wani abunda kake yi kake son ka samu kudi da shi to sai kayi download dinshi a play store.

Da kayi ka saida sunan Kasuwanci, lokacin da kake hotunan hajar da kuma farashin yadda kake saidawa da ka zaka rinka turawa a group group kuma duk mai lambarka da ya duba profile din ka zai gani.

Karanta: Koyon Sana’a: Muhimman Abubuwan Dubawa kafin koyon sana’a

 

Kammalawa

Kafafen sada zumunta suna taka rawa sosai a wajen  habbaka kaasuwanci kuma basu da iyakar yanayin abunda mutum zai iya samu a cikinsu sai dai suna bukatar hakuri da samun mabiya wanda hakan baya yuwuwa sai da rubuta ko daura ma mabiya abubuwa masu amfani wanda zai taimakesu