Skip to content
Home » Koyon Sana’a: Muhimman Abubuwan Dubawa kafin koyon sana’a

Koyon Sana’a: Muhimman Abubuwan Dubawa kafin koyon sana’a

Koyon sana’a yana da matukar amfani ga rayuwar dan Adam saboda dole ne mutum yayi kokari yaga wane abu ne zai yi domin ya dogara da kansa na daga cikin sana’oi imma na Gargajiya ko kuma na zamani.

Inshallahu a cikin wannan post din zamu yi magana akan ma’anar sana’a da kuma yadda zamani ya sauya sana’oi da yawa zuwa kashi daban daban, amma bari mu fara da ma’anar sana’a.

sana'a da jerin misalan sana'oi da ya kamata mutum yayi

Micece Sana’a?

Sana;a tana nufin iya wani abu wanda zai zamar ma mutum wani abun dogaro da kansa wanda zai dauke shi a matsayin hanyar sa ta samun kudi, kuma kamar yadda hausawa suke cewa a san mutum  a san sana’arsa hakan a bun yake.

Saboda ma damar mutum bashi da wani abu da yake yi za’a ringa tuhumarsa ko kuma mutane su rinka canza tunanin da su ke masa saboda wannan illar rashin abun yi.

Yanayin yadda zamani ya sauya sanaoi a fadin Duniya

A dalilin cigaba da aka samu na kimiyya da fasaha sana’oi da dama sun canza akala daga yadda aka sansu wasu a baya ba’a yinsu amma sanadiyyar canzawar zamani wasu sabbin sanaoi sun shigo wadanda suke taka rayuwa sosai a fannoni daban daban na rayuwar alumma.

Sanaoi sun kashi zuwa gida biyu akwai na gargajiya akwai kuma na zamani wanda dukansu mutum indai ba tashi yayi yaga ana yinsu ba a gidansu dole yatsaya ya koya yadda ya kamata.

Karanta: Yadda ake bude YouTube Channel

YouTube: Bayani Game da YouTube da Yadda zaka Amfana da Shi

Abubuwan da ke taimakawa wajen zaman Hardar Qur’ani

Saboda ko bayan fara sana’a sanadiyyar canzawar zamani ita kanta yanayin talla ya canza akwai ta internet wadda ta bullo wadda kuma tana taka rawa sosai wajen taimakawa yan kasuwa.

Bari mu tafi akan wasu muhimman abubuwa kamar yadda post din yayi magana da ya kamata mutum ya natsu ya koya kafin fara sana’a.

Muhimman Abubuwan Dubawa

Ra’ayin sana’ar ga mai koyon

A farko dai kafin ka fara kowace irin sana’a ka tabbata kana da ra’ayin yinta ma’ana zaka iya ware lokacinda ka domin ka tsaya ka koyi abunda ya dace dangane da ita sosai.

Domin kowace sana’a da kake gani a duniya ana bukatar idan mai saye ya zo yaga akwa kwarewa musamman ma sana’oin hannu wanda mutane ke neman kwararre ido rufe.

To don haka yana da kyau ka tabbatar ka sadaukar da lokacinka kai har da ma kudinka domin ganin ka kwarea a fannin hakan yana taimakawa sosai.

Yanayin jarin da take Bukata

Kasuwanci ko ko kuma muce sana’oi kala kala ne akwai manyan kasuwancin da ake samun kudi  da su wanda suna bukatar hari sosai akwai kuma kanana wanda karamin jari ma ya ishe su.

To yana da kyau kaga kuma ka auna yanayin kudin da kake samu da kuma abunda sana’ar take bukata saboda yana da kyau fa kasani cewa shi kasuwanci ko kuma duk wata sana’a da muke da ita a duniya fa tana bukatar jari kuma iya yawan jari iya yadda kasuwancin yafi gudana kuma aka fi samun riba indai har akwai ribar.

To idan kamar kananan sana’oi ne kamar su hada man shafawa, arfreshner da sauran kananun sanaoi da sauransu dan karamin jarinka ma yana isa kamar kasa da dubu 10 ya hada maka komai.

karanta :

Yadda ake hada man shafawa verseline

Inda zaka koyeta

inda zaka koyi sanaoi a internet

Inda zaka koyeta dole ma ne sai kayi tunanin akan haka wannan tun kafin mutum ya fara sana’ar ake butar hakan saboda kamar yadda nayi magana a baya akwai bukatar kwarewa kafin farawa.

Akwai wurare a yanxu da dama wanda zaka iya zuwa ka koyi sana’oi kamar a garinku inda ake bada horaswa ta yan kasuwa.

A fannin online ma haka in dai har da gaske ne kake ko littafi nawa yake akan sana’a kana iya fidda kudinka ka saye shi saboda amfanin da yake da shi a wurinka.

Kuma ko bayan ka koya karika shiga groups na kafafen sada zumunta kamar su facebook wadanda ke magana akan sana’oi irin naka kana karuwa da sabbin abubuwa da suke shugowa saboda ba’a son ka koyi sana’a da kuma abubuwa sabbin na zamani sun zo kace baka aiki da su matsala ce a kasuwanci sosai wannan.

Suwanene Customomin?

Sanin suwanene kake tunani su zamto suke sayen hajarka yana da amfani kuma kwaraewa akan fahimtar su na taimakawa matuka wajen inganta ko wane irin kasuwanci ne a fadin duniya baki daya.

Ta hanyar fahimtar su ne zaka san cewa wadanne hanyoyi ne ya kamata ka bi domin inga sana’ar yadda kullun zaka rinka burge su sosai ta hanyar hada masu ko kuma yimasu abunda kaga suna sha’awa hakan yana kara danko sosai tsakanin kai dan kasuwa da kuma masu zuwa wajenka sayayya.

Kammalawa

Akwai iri irin sana’oi da dama dai a fadin duniya wanda yanzu cigaba yazo na internet mutum da kansa ma yana iya yayita bincike a shafukan internet domin ya habbaka kansa ta fuskar karatu koda kau da yanren hausa ne domin shi google yana jin yarukan duniya da dama.

Kuma kamar yadda nike yawan cewa kasuwanci ko kuma sana’oi suna bukatar hakuri, juriya da kuma naci indai ana son cimma abunda ake so koma abunda ya wuce wanda ba’a tsammani ba kamai tambaya yana iya yi a comment section da ke kasa mungode.