Table of Contents
YADDA AKE GIRKI COMPLETE SANWA|
YADDA ZANI GIRKA ABINCI KALA KALA
Assalamu alaikum jama’ a jamu yi magana a cikin wannan post din yadda ake girka abinci kala kala daban daban wanda kusan dun mun yi su a wannan website din mai albarka wato Hausawasite.com.ng wanda kuma kowane daya daga cikin su zamu bada link din shi inshaallahu daya bayan daya ga su kamar haka.
list din Yadda ake gika abinci
10. yadda ake meat pie da yadda ake sprong rolls
11. yadda mace zata zama tauraruwar girki
Ga lissafin yadda ake girkin daya bayan daya
1. yadda ake hada sunasur
Yadda ake sunasur a saukake da shinkafar tuwo mai dadi
A cikin wannan post din inshallahu zamu yi Magana ne akan yadda ake hada sunasur na shikafar tuwo, to kamar dai yadda aka sani sunasur wani daya ne daga cikin abinci na hausawa wanda aka dade ana yin shi har yau.
To bayan wannan yar matashiya yanzu zamu tafi izuwa yadda ake hada sunasur din amma kafin nan kamar yadda muka saba a cikin wannan website din muna fara lissafa kayan hadin kafin muje ga yadda ake hada duk yawan cin abun da muke koyawa.
To ga kayan da zaa sawo a kasuwa ko a samo in akwai a cikin gida
Kayan da ake hada sunasur da su
1. Sugar
2. Shinkafar tuwo
3. Yeast
4. Man gyada
5. Albasa
Yadda ake hada kayan hadin sunasur
To yanzu zamu yi bayni ne akan yadda ake hada wato su kayan hadin.
To akaron farko dai zaa samu shinkafa ta tuwo mai kyau tsaftatacciya a sa ruwa a wanke ta sosai sannan kuma a jika ta.
Daga nan kuma sai a bayan an jika ta a bar ta ta kwana, to bayan ta kwana daya sai a kai ta a marka do ta a injin markade ta amma fad a sharadi kada a markade ta akan wake.
To bayan an kawo markaden ta sai a aje ta a zuba yeast a buga ta a aje ta a gefe daya
To bayan tad an jima sai a zuba sugar da gishiri kadan yadda ake son dan dano, wasu ma sukan zuba nono saboda ya kara tashi kuma da kayau.
Daga nan kuma abunda ya rage sai a dauko albasa a yanka a zuba sai juya ko a motsa sosai .
Daga nan kuma sai a dauko farantin suya a dora akan wuta wato (non – stick) kokuma a samo irin wanda ake soya sunasur das hi na zamni. Kamr dai kusan yadda ake wainar filawa sai a kawo wainar filawa a rinka zubawa sai a samo mari a rufa amma baa juya shi idan ya soyu sa a cire a zuba a kwano ko tasa .
A karshe
muna fatan kun ji dadin wannan post din kuma duk mai tambaya yana iya yi a comment section, akwai post na yadda ake hada yamball sai a duba mun yi shi sai anjima mun gode.
2. Yadda ake yin Tsiren jan nama a cikin steps masu sauki
Yadda ake yin Tsiren jan nama a cikin steps masu sauki
A wannan post din inshallahu zamu yi magana ne akan yadda ake hada tsire wato na jan nama in baa manta ba a baya mun koya yadda ake hada yam ball in baka karanta ba ka karanta wanda shi dai kamar yadda aka sani tsire abune ko kuma in ce daya ne daga cikin abincin hausawa wanda suka dade suna yi yun kaka da kakanni, to ba tare da bata lokaci ba bari mu fara zayyana kayan da ake hada tsiren wadanda zaa nemo a kasuwa sanan sai mu cigaba da da bayani akan yadda ake hada wato su wadannan kayan.
Kayan da ake hada tsiren jan nama
- nama
- Koren tattasai
- Albasa
- Tumtur
- Maggi
- Kwai ina ana da shaawar sa shi
- Citta
- Attarugu
- Thyme da curry
- Tafarnuwa
To wadannan na sama suna kayan da zaa a samo yanzu zamu tafi izuwa yadda ake hada wato su kayayyakin.
Duba: yadda ake samosa
Yadda ake hada kayan tsiren jan nama
To da farko dai abunda ake yi shine zaa dora shi nama din a saman tukunya sannan a zuba maggi da gishiri da albasa da kuma tafarnuwa to bayan an zuba su a tukunya sai a dan sulala su har su yi laushi sosai.
Bayan an yi haka sai a sauke ita tukunyar a yanka albasa da tumatur sannan a dauko jajjagagen attarugu da tafarnuwa sannan a soya su daban su soyu sosai idan suka kama soyuwa sai a aje su a gefe.
Daga nan kuma sai a dauko wannan naman da aka dafa a soya shi, to bayan an soya shin sai a samu sinke a ringa soka naman sannan sai a dauko koren tattasai a yanka da albasa da kuma tumatur daga nan kuma sai a sa naman a tsinken ana daukowa ana tsirawa a cikin tsinken kamar nama ukku ko hudu haka a cikin tsinke guda amma ya fa danganta ga yawan naman da ake so.
Daga nan kuma sai tsoma tsiren a cikin kwai ana soya ko a gasa har ya kasu lafiya law
3. Yadda ake hada samosa a cikin steps masu saukin yi
yadda ake hada samosa zamu yi magana a cikin wannan post din inshallahu,
to kamar dai yadda muka saba a wannan website din muna fara lissafa abubuwan ko kayan da zaa sawao a kasuawa a farko, to a cikin wannan post din shima haka ne zamu lissafa kayan da zaa tana don hada samosa.
Kayan da ake bukata
1. Filwa
2. Nama
3. Albasa
4. Attarugu
5. Maggi
6. Curry
7. Gishiri
8. Thyme
3 Yadda ake hada kayan hadin samosa
Sai a soya su sama sama sai a sa maggi a kara curry idan baijiba,
Daga nan sai a kwaba filawa amma gishiri kawai zaa sa a cikin kwabin daga nan kuma sai a
samu non -stick fryin fan sannan sai a ringa shafa filawar da aka kwaba da brush.
Amma fa baa shafa mai a fran din daga nan kuma idan tayi sai a ringa daukar rafers din wat
o wanada aka soya nan ajewa a gefa daya har sai an gama gasa su dukan su.
To bayan an gama soya wrafers din sai a dauko nama ana zubawa a kowace wrafer da aka
yi ta filawa sai a rika zubawa ana rufewa kamar dai yadda ake yi a meat pie.
Daga nan sai a dauko kowane gefe a ringa yazo tsakiya yayi kamar ninkin triangle a shape kamar haka.
Bayan an kama yin shape din triangle din daga nan kuma sai a dora mai mai zafi ak kasko a ringa dauka ana soyawa har ya soyu daga nan kuma sai a zuba a kaawano ko roba.
4 Yadda ake hada yam Ball a cikin steps masu saukin yi
4 Yadda ake hada yam Ball a cikin steps masu saukin yi
Yadda ake hada yam Ball a cikin steps masu saukin yi
A wannan post din zani yi Magana ne a kan yadda ake hada yam ball a cikin steps masu sauki wato a cikin hanya mai saukin yi, to kamar yadda dai kowa ya sani shi yam ball ana hada shi ne doya sannan kuma a hada wato ita doyar da sauran kayayyaki wadda zasu kara mata armashi kuma abinci ne wanda aka saba dashi kusan mafi yawancin mutane suna cin sa bama a kasar hausa ba a kusan fadinduniya gabakiya.
Ýam ball dai kamar yadda kowa ya sani abinci ne wanda yake hade da sinadaran da jiki domin yana kunshe da sinadarai irin su protein wanda suke kara gina jiki a sanadiyar a cikin kayan hadin akwai irin su nama da kwai,da kuma sinarai na starch wato daga ita kanta doyar.
To kamar yadda na saba a cikin wannan website din a kowane post ina fara zaayyana kayayyakin da ake amfani das u sannan sai kuma muje zuwa yadda ake hada wagto su kayan gabakidaya.
To inshallahu ma a wannan ma haka zamu yi da farko zamu fara lissafa kayan da ake bukata don hada yam ball sannan mu je zuwa yadda ake hada kayan da ake hada yam ball din.
Kayan da ake hada yam ball da su
Kayan da zamu lissafa a kasa sune ake hada yam ball da su wadda zaa nemo ko kuma a sawo a kasuwa wanda basu da wahalar samu.
· Doya
· Kwai
· Albasa
· Attarugu
· Magi/gishiri
· Nama
· Mai
Matakan ko steps din da ake bi wajen hada kayan yam ball din
To dafarko dai zaa fere doya mai kyau sannan sai a sa ruwa a wanke ta sosai sai a sa ta a cikin tukunya a dafa idan ana da bukatar gishiri ana iya sawa kadan a wajen dafuwar bayan ta dafu sai a sauke tukunyar sai a tace ita doyar sai ki aje a wuri daban.
Daga nan kuma sai a yayyanka albasa da attarugu a zuba a turmi a daka ko a kirba, sannan sai a zuba magi da gishiri dan kadan a cikin turmin a cigaba da dakawa.
Sannan sai a debo dafaffar doya a daka ana dakawa sama sama sannan a juye a cikin kwano sannan a dauko nama sai a zuba shi a kai.
Idan ana so kamar gishiri bai ji ba sai a kara yadda zai daidai ta sai a juyasu a dunga mulmulawa ana tsomawa a cikin rowan kwai sai a dora kaskon mai yayi zafi sai a cigaba da soyawa har ya soyu daga nan kuma sai a kwashe a zuba a cikin kulak o kuma kwano.
To daga nan ne muka kawo karshen wanan post din na yadda ake hada yam ball a cikin steps masau sauki wanda ko wacce ked a tambaya ko Karin bayani akwai comment section sai a yi.
5. Yadda ake hada doughnut
Butter
Yadda ake hada Doughnuts
Post din yau yana Magana ne akan yadda ake doughnut mai dadi, inda za mu yi Magana inshallah ko kuma muyi cikaken bayani akan yadda ake hada shi Doughnut din da kuma kayan da ake amfani ko kuma kayan da zaka/ki sawo a kasuwa dmin hada wan nan kayataccen doughnut din.
To zamu farad a lissafa kayan kamar yadda aka saba sannan inshallahu mukuma yi maju bayanin yadda ake hada kayan.
Kayan da ake Hada Donut
Filawa
Kawai
Butter
Yeast
Madara
Baking Powder
Flavour
Yadda ake hada kayan Doughtnut din
Dafarko dai zaka/ki jika yeast da ruwa na dumi a cikin rubber ko kuma tasa tsaftatacciya, sai a aje a gefe sannan kuma sai a narka butter a hada da sugar sai ajuya shi ko kuma ince a motsa.
Bayan sugan ya narke sai a zuba rowan yeast akai wanda muka ambata a baya, a zuba baking da gishiri kadan da kuma madara, sannan kuma sai a zuba filawa a kwaba, a kawaba har yay kawri wato kwabin dai ya hade ake so .
Sai a rufe a aje a rana ko kuma wuri mai dumi don kwabin ya tashi , bayan an aje shi ya tashi sai kuma a sake kwabawa a rinka yimasa shape wato circle da huda a tsakiya kamar yadda yawanci aka san shi .
Sai a kara aje shi a cikin rana ko wajen dumi ya tashi. Sai a sa mai a kan wuta yayi zafi sosai ba kuma yadda zai toya shi ba , sannan sai a zuba a cikin kaskon man har yay brown ko kuma dan ja ja haka a kala. Sannan kuma sai a kwashe a zuba ma baki ko kuma mai gida .
Akwai wani post don ki/ka kara kwarewa a harkar girki duba shi wanda shine :Abubuwa 12 dake sa mace tazama taurarwar girki munyi bayani sosai a kansu.
wanda ke da tambaya kar ya ji komai yayi a comment section onshallahu zamu amsa mai a ci dadi lafiya kar a manta dani.
6.
Yadda ake cake mai sauki zamu yi Magana akan shi yau inshallahu, wanda in aka bi steps din zaa samu nasarar hada shi, kowa dai ya san cake ya kuma san anfaninsa da kuma inda ake yawan yinshi
Kuma ma wasu sanaar su kenan yin cake su saida da kudi masu tsada domin da sun dan sawo kayan sai ka ga sun sai da tsaada. T o bari mu je ga steps din da ake bi don hada cake da kuma da kayan da ake sawowa don a hada cake din, ga kayan kamar haka.
Kayan da ake hada cake da su
1. Kwai kuda shidda(6)
2. Butter gwangwani (1)
3. Sugar cup (1)
4. Filawa cup(1)
5. Madara cup(2)
6. Bakin powder (½) tea spoon
7. Gishiri (½) tea spoon
8. Flavour
Yadda ake hada kayan hadin cake din
To dafarko dai zaa farad a fasa kwai a hada da butter da sugar har sai sun narke sannan sai a zuba madara dab akin powder sai a cigaba da motsawa kada a zuba ruba ruwa a cigaba da motsawa har sai
ta damu sosai ,
daga nan kuma sai a shafa butter a gwangwanin da zaa gasa sai a zuba kwabin a gwangwanin da aka shafa butter sai a gasa shikenan.
Idan akwai tambaya ayi a comment section.
7.Yadda ake tuwo ukku masu dadi
Manar tuwo ukku anan shine
* Tuwon masara
* Tuwon ruwa
* Tuwon shinkafa
Jama’a kamar yadda kuka saba ganin shirye shiryemmu akan kari to yama Allah ya dawo dani kamar kullun ku bi yoni domin jin yadda tuwo ukku zai kasana ce a gidanki
Tuwon masara
Abinda ake bukata:-
* garin masara
* Ruwa
Yadda akeyi
Idan ruwanki na bisa tukunya ya tafasda, daman ki tankada garinki saiki zuba tsaki daga nan saiki sa garinki ki talga shi har yayi kauri saiki jika kanwarki ki dan zuba kadan saiki rufe, idan yayi zaki kwashe abinki a leda ko a flate.
Ki sami danyar kubewarki ki ga mai gidanki ya kwashi dadinsa.
Tuwon ruwa
Abinda ake bukata:-
* Gero
* Ruwa
Yadda ake sarrafasu
Idan kika samu geronki saiki jika shi kwana biyu ko ukku, amman zaki dunga canza ruwan. Idan kin jika kamr yau da daddare, jibi sai kiyi abinki.
Saiki markado abinki ki tace ki dora ruwanki bisa wuta. Idan ruwanki ya tafasa, sai ki dama ki zuba ruwan zafin ki yi ta tukawa har kahwar tayi kauri sai kiyi ta lulayawa kina mai dawa cikin ruwan.
Ana cin tuwon ruwa da miyar ganye ko kubewa danya, ko ayi kwado dashi da daddawako da kuli. Yanada dadi ko a siyar da shi.
Tuwon shinkafa
Abunda ake bukata:-
* Shinkafar tuwo
* Ruwa
Idan kika gyara shinkafarki ki ka wanke ta sosai, idan ruwan ya tafasa sai ki zuba shinkafarki a ciki ki rufe. Idan ta fara dahuwa, sai ki dan rage wutar kadan ki dan bari ruwan ya dan tsotse, saiki tuka abinki. Ki tuka sosai ya dan tsotse , sai ki tuka abinki. ki tuka sosai har ki kammala tuwon shinkafarki, sai ki kwashe acikin leda ko plate ko tire.
Ki samu miyar da kike so ki kaima angon ki ku ci tare da shi, ki bashi ya baki. Zakuji dadin abincin.
Mai karin bayani zai iya yi a coment ko kuma wanda yaga wata matsala ko kuma wanda yayi sai ya bada labari a coment
Author Profile
Latest entries
- Sana'o'iJanuary 6, 2025Koyon Sana’a: Muhimman Abubuwan Dubawa kafin koyon sana’a
- Kiwon LafiyaJanuary 3, 2025Maganin da Ganyen Parsely yake da suka hada da sanayi, cancer da sauransu
- KasuwanciJanuary 1, 2025Hanyoyi 5 na Juya Kudi da Suke da Riba mai Yawa
- Sana'o'iJanuary 1, 2025Gyaran Waaya: Yadda ake Fara Sana’ar Gyaran Waya