Table of Contents
Yadda ake sunasur a saukake da shinkafar tuwo mai dadi
A cikin wannan post din inshallahu zamu yi Magana ne akan yadda ake hada sunasur na shikafar tuwo, to kamar dai yadda aka sani sunasur wani daya ne daga cikin abinci na hausawa wanda aka dade ana yin shi har yau.
To bayan wannan yar matashiya yanzu zamu tafi izuwa yadda ake hada sunasur din amma kafin nan kamar yadda muka saba a cikin wannan website din muna fara lissafa kayan hadin kafin muje ga yadda ake hada duk yawan cin abun da muke koyawa.
To ga kayan da zaa sawo a kasuwa ko a samo in akwai a cikin gida
Kayan da ake hada sunasur da su
1. Sugar
2. Shinkafar tuwo
3. Yeast
4. Man gyada
5. Albasa
Yadda ake hada kayan hadin sunasur
To yanzu zamu yi bayni ne akan yadda ake hada wato su kayan hadin.
To akaron farko dai zaa samu shinkafa ta tuwo mai kyau tsaftatacciya a sa ruwa a wanke ta sosai sannan kuma a jika ta.
Daga nan kuma sai a bayan an jika ta a bar ta ta kwana, to bayan ta kwana daya sai a kai ta a marka do ta a injin markade ta amma fad a sharadi kada a markade ta akan wake.
To bayan an kawo markaden ta sai a aje ta a zuba yeast a buga ta a aje ta a gefe daya
To bayan tad an jima sai a zuba sugar da gishiri kadan yadda ake son dan dano, wasu ma sukan zuba nono saboda ya kara tashi kuma da kayau.
Daga nan kuma abunda ya rage sai a dauko albasa a yanka a zuba sai juya ko a motsa sosai .
Daga nan kuma sai a dauko farantin suya a dora akan wuta wato (non – stick) kokuma a samo irin wanda ake soya sunasur das hi na zamni. Kamr dai kusan yadda ake wainar filawa sai a kawo wainar filawa a rinka zubawa sai a samo mari a rufa amma baa juya shi idan ya soyu sa a cire a zuba a kwano ko tasa .
A karshe
muna fatan kun ji dadin wannan post din kuma duk mai tambaya yana iya yi a comment section, akwai post na yadda ake hada yamball sai a duba mun yi shi sai anjima mun gode.
Author Profile

- IBRAHIM BUHARI Shahararren marubuci ne game da sana'oi, Digital Skills da sauransu shine kuma shugaban kamfanin HS Global Wato Shugaba a Wannan Website ta Hausawa Site
Latest entries
KasuwanciAugust 23, 2025YADDA AKE HADA LIQUID SOAP – DA FARA KASUWANCIN SA
KasuwanciJuly 31, 2025KASUWANCIN AIR FRESHNER: YADDA AKE HADA AIR FRESHNER
KasuwanciJuly 28, 2025SANA’AR INVITATION: YADDA AKE FARA SANA’AR DESIGN NA INVITATION
KasuwanciJuly 28, 2025SABBIN DABARUN KASUWANCI: Yadda Matasa Zasu Fara Sana’a da KUDI (₦10,000–₦50,000)