Soya fara nada saukin yi, a cikin wannan post din inshallahu zamuyi magana akan yadda ake soyawa tare da bayanan matakan kamar yadda muka saba yi ga kowane nau’in abinci.
To kafin mu fara bayani akan yadda zaki soya, yana da kyau ki san san wani abu ita fara akwai mai rai wadda da aka kamo maki da ranta zaki soya ta akwai kuma marar rai wadda ake awna ta a buhunna ana saida ta a kasuwanni.
Table of Contents
Kayan hadin soya fara
- fara
- maia
- yaji
- magi
- gishiri
- kayan kamshi kamar su thyme da korry da sauransu
Yadda ake ma fara mai rai
Da farko abunda ya kamta kiyi idan tana da ranta kafin ki fara saya farar zaki daura ruwan zafi a cikin tukunya ki zafka farin a cikin ruwan zafi domin su daina motsi gabakidaya.
Daga nan kuma bayan sun daina motsi sai ki juye ta ki canza ruwan zafin ki sa wasu ruwan, a wannan ruwan na biyu zaki gyara ta ne ki fidda kai daban, jiki da kuma kallema har da ma gashin da ke a bayanta daman shi wannan kusan dole ma ne ki fidda shi.
Byan nan kuma sai ki samu ruwa ki dauraye ta ki sata ta a wani wuri mai fadi ta bushe a rana ko kuma wajen da take samun iska yadda ruwan jikinta zai dan tsane.
Yadda ake soyawa
A wajen soyawar zaki samu tukunyar ki mai kyau sai ki dora ta a saman wuta, bayan nan kuma sai ki dakko farar amma yana da kyau a wajen gyarawar a ce kin rabe tsakaninin jikin farar da kuma kallema da kaia.
Daga nan ki fara soya jikin saboda yafi wahalar soyawa idan kamar bayan kin zuba shi yayi rabin soyuwan sai ki kawo sauran kallemar da kai ki hada su su soyu tare gabakidaya kina yi kina juyawa yadda zai soyu da kyau.
Karanta:
Yadda Ake Hada Cin-Cin mai Gurus Gurus
Yadda aKe hada Alkaki a saukake
Yadda ake ma wadda batada rai
ita kawai bayan kin fara gyara ta kin bambance tsakanin kafa, kai da kuma jikin sai ki samu ruwa mai zafi kidan zafka ta a ciki yadda datti, hoda da duk wata kura wadda ta dangance ta zata rabu da ita sai ki sanya ta a cikin rana.
Bayan kin sa ta a cikin rana da kin ga ruwan jikin ta ya dan tsane haka sai ki dauko ta ki sata a tukunya ta ki samu kayan hadinki kamar mai ki sa a cikin tukunya tare da farar.
kar a manta ana tare da website din Hausawasite.com.ng ne wanda ta Al’ummar Hausa ce inda ake koyon abubuwa daban daban daga masana da dama a cikin harshen hausa musamman sana’oi don dogaro da kai Domin kasancewa damu kana iya Rubuta Hausawa SIte a Google don samun sabbin rubuce – rubucenmu
ki fara soya jikin yadda soyen zai yi kyau sannan sai ki dauko sauran kayan kamshi kamar yadda muka ambata su a sama ki sanya su a cikin tukunya kina soyawa kina motsawa har ta soyu yadda ya kamta sosai
karanta:
Yadda ake Spring Rolls Cikakken Bayani Tare Da Hotuna
Hanyoyi da ake bi don adana Naman Sallah ya jima ana Amfani dashi
:
Kammalawa
Kamara yadda nayi bayani a wajen soya fara akwai abunda ya kamata a ringa kula wanda shine idan kika zuba ta duka, ma’ana jikin da kafar da kuma kan to zaki ga cewar kai da kafa sun yi saurin soyuwa sun bar jikin.
Amma yadda zaki magance wannan matsalar a cikin hanya mafi sauki shine ki fara zuba jikin ki soya shi ya fara soyuwa koda kamar rabi ne ko kusa da haka ko sannan jikin.
ko kuma ki saya su daban daban yadda zata yi dadin ci aamma da zaran kika zuba duka zaki ga ba kamar yadda in kika raba ba kina ma iya ganin sun kone kafin jikin ya fara soyuwa yadda ake so.
karanta :
Yadda Ake hada Alala mai Kwai a cikin matakan yi masu sauki yi
yadda ake Spring rolls da meat pie
Author Profile
Latest entries
- Sana'o'iJanuary 6, 2025Koyon Sana’a: Muhimman Abubuwan Dubawa kafin koyon sana’a
- Kiwon LafiyaJanuary 3, 2025Maganin da Ganyen Parsely yake da suka hada da sanayi, cancer da sauransu
- KasuwanciJanuary 1, 2025Hanyoyi 5 na Juya Kudi da Suke da Riba mai Yawa
- Sana'o'iJanuary 1, 2025Gyaran Waaya: Yadda ake Fara Sana’ar Gyaran Waya