Skip to content
Home » Hanyoyi da ake bi don adana Naman Sallah ya jima ana Amfani dashi

Hanyoyi da ake bi don adana Naman Sallah ya jima ana Amfani dashi

 

Soyen Nama

Hanyoyi da ake bi don adana Naman Sallah ya jima ana Amfani dashi

Sanin kowane cewa wani a lokacin sallah nama na wadatuwa wanda yawan cin shi yakan haifar da illa a lokutta musamman na sallah, a dalilin haka ne mutane da dama sna son su adana naman sallah dinsu yadda zai jima masu suna ci ko kuma a ajiye shi bayan watanni don a dauko a ci.

To shi nama ko soya shi akayi idan ba’a dauki matakai ba na adana shi lalacewa yakeyi ya rube, to a dalilin haka a wannan website ta Hauswa Site kamar yadda muka saba kawo maku post masu amfani na Kirki wirinsu Farfesun Nama, Cin-Cin, Fanke, Alkaki da sauransu a yau muka ga ya kamata muyi bayani akan hanyoyi da ake bi don adana naman sallah.

Hanyoyi da ake bi don adana Naman

Akwai hanyoyi tabbas da ake bi don adana nama amma ga muhimmai daga cikin su wadanda aka fi amfani da su a koda yaushe wanda wasu daga ciki yana iya yin kamar tsawon watanni ma ba tare da wani fargaba ba, gasu Kamar Haka.
Soya Nama

Amfani da Gishi

Wannan hanya tana damatukar amfani kuma gaskiya tana iya adana maka nama kusan tsawon watanni batare da ya lalace ba, yadda ake yi shina za’a samu soyayyen nama sai a barbada masa gishiri sai a samu wani abu wanda ba ya bari iska ya ratsa shi sai a ajiye ko a dana.
Idan ana son a yi amfani da naman bayan wani lokaci sai a dauko shi a wanke naman sosai wato a wanke duk gishirin sai a sulalashi a saman tukunya a ci.

    
Hanyar Fridge

Kamar yadda kowa ya sani cewa hanyar sanyi na daga cikin hanyar da ke hana abubuwan amfani musamman ma abinci kin lalacewa ba kawai ya ta’allaka a nama ba.

Yadda ake kawai shina a samu fridge wanda ana yawan kunna shi a zuba naman bayan an soya shi sai a sa yayi sanyi lokacin da ake bukata saia adauko a sulala

Kitse

Shin ko ka san cewa kitsen da yake dankarewa bayan gama soy ana iya amfani dashi  a jiye nama wannan ko shakka babu da an samu kitse sai azuba nama a cikin shi shima wata hanaya ce wadda ake aje naman da an tashi sdai kawai a dauko a silala shi.