Skip to content
Home ┬╗ Littafin Bayajidda na Hausa

Littafin Bayajidda na Hausa

Asalin sunan bayajidda Abu Yazid bn Abdullahi, ya fito daga daular Bagadaza, yankin Bagadaza tana cikin kasar Iraki a yanzu, Babansa mai suna Abdullahi shine sarkin Bagadaza a wannan zamanin watau dai shine yariman Bagadaza. Bayan wata Sarauniya mai suna Sarauniya Zigawa taci kasar Bagadaza da yaki sai Yazid watau Bayajidda. ya ta shi daga kasar Bagadaza tare da rundunar mayakansa masu yawan gaske ya nufi afrika, ya ketara sahara ya shiga Chadi sannan ya isa kasar Hausa ya yada zango a daular Barno.
BAYAJIDDA YA ISA KASAR BARNO
Bayajidda ya shiga Barno don ya mamaye ta, kan hanyarsa ta zuwa
Barno yaci Bagarmi da yaki, daga nan ya tafi Barno, shi kuwa Shaihin Barno na wannan zamani ya ji tsoron ya yaki Bayajidda, sai ya shammaci shin ya ce in ya karaso zai bashi auren diyarsa mai suna Magaram ya aura.
lokacin da ya isa Barno baya jin yaren Hausa, a hankali sai ya fara koyon yaren Hausa, mutane suka rinka yi masa lakani da sunan “Ba ya ji da” a hankali a hankali sai aka hade lakanin da ake masa ya koma Bayajidda.
Bayan Bayajidda ya yada zango a Barno, sarki ya yankar masa kasa
ya zauna tare da rundunarsa, da yake rundunarsa mai karfi ce da tarin
sadaukai, ga kayan yaki gashi sun iya yaki, sai munafukai wadanda ba
su so zuwan Bayajidda wannan yanki na Barno ba suka rinka kai wa sarki
suka suna kai gulmar Bayajidda suna cewa sarki lallai Bayajidda ya zo annan yanki na Barno don ya yaki sarki ya kwace masa kasa.
Rannan dai sarki ya tara ‘yan majalisarsa don ayi shawara, yace;
‘Gashi dai mun yi bako amma ga duk kan alamu ya zo ne don ya
yake mu, ina shawara?’
Aka yi shawara da aga karshe aka yanke hukuncin aba Bayajidda
auren diyar sarki, watau dai a daure bakinsa, in ya zama sirikin
sarki babu shi babu yakar sarki, in aka yi haka sai sarki ya yi
amfani da wannan dama ya rinka aron sadaukan sarki yana tafiya da
su yaki har su kare, daga nan Bayajidda bashi da katabus! sai sarki
ya yi yadda yake so da shi.
Bayan kwana biyu kuwa aka kira Bayajidda aka yi masa bushara
da auren diyar sarki mai suna Magaram, Bayajidda ya yi na’am aka
daura aure amarya ta tare gidan miji.
Da gani wannan amana da sarki ya bashi, sai Bayajidda ya
saki jikinsa ya rinka ba sarki aron sadaukansa in za shi yaki.
Tun da sarki ya zama sirikin Bayajidda sai ya shiga aron
sadaukan bayajidda yana zuwa yaki da su, a hankali har suka kare,
Bayajidda ya watsa sadaukansa kowa ya kama gabansa, da sarki
ya tabba ta bashi da kowa sai nya tasamma kashe shi.
Bayajidda ya fahimci irin tuggun da sarki da mutanensa suka
kulla masa, sai ya yi niyyar guduwa ya bar garin, ya tattara
kayansa ya bar kasar Barno da kuyangarsa daya da matarsa, cikin
dare Bayajidda ya gudu, ya yi yamma har ya isa Garun Gabas
da ke kasar Hadeja a yanzu.
BAYAJIDDA YA ISA GARUN
GABAS
Garun Gabas babban gari ne, yankin kasa ne a cikin kasar Hadeja,
bayan ya bar Barno sai su ka yi ta tafiya yamma da kasar Barno har
suka isa Garun Gabas, saboda tsananin wahala ga ciki ga kishirwa da
yunwa gashi Magaram tana da juna biyu sai Bayajidda ya bar matarsa
Magaram a nan Garun Gabas tare da wasu bayi, shi kuwa ya tafi.
Suka samu masauki ba’a jima ba Magaram ta sauka lafiya, ta
haifi da namiji, ranar suna ta zagayo aka sa wa yaro suna Biram,
shi ne dan Bayajidda na farko, shi ne kuma ya fara kafa sarauta
a Gabas-ta-Biram, ya riki Sarautar Biram. Shi kuwa Bayajidda
ya yi ta tafiya har ya isa kasar Daura.

HAUSA BAKWAI
Bayan Bayajidda ya bar duniya sai dansa Bawo dan Sarauniya Daurama ya gaji Sarautar Daura, bayan daula ta kafu ana ta adalci cikin kasar Daura, a wannan lokacin kuwa sauran Daulolin kasar Hausa babu zaman
lafiya,

BAYAJIDDA YA ISA GARIN
GAYA
Shi kuwa Bayajidda bai yi wata-wata ba sai ya yi wa dokinsa sirdi ya yi
limzami ya nausa ya yi ta tafiya, ya bar matarsa da dansa a Grun Gabas
Ya yi ta tafiya har ya isa wani dan kauye mai suna Gaya, yana kusa da
kasar Kano, yanzu haka Gaya tana cikin kasar Niger. A nan kauyen
Bayajidda ya samu wani kwararren makeri ya kira masa wata kyakyawar
takobi mai hubba da kaifi da daukar ido da kwarjini a idon duk wani
sadauki da ya ganta. Da gama kera masa wannan takobi sai Bayajidda
ya sake yin sirdi ya yi limzami ya nausa cikin daji.
DAULAR DAURA
Kasar Daura Daula ce mai dadadden tarihi, tsohuwar masarauta ce da sarauniyoyi suka mula tun kafin karni na tara, tana daya daga cikin kasashen Hausa masu tarihi har ma wasu na kalllonta da matsayin asalin Hausa, watau inda Hausa ta samo asali. Daular Daura yanzu haka tana cikin yankin kasar Katsina.
Kabara lo Magajiya shi ne nakalin da ake wa sauraniyoyi a kasar Hausa
Musamman a Daular Daura in da sarauniya ce ke mulkin kasar har tsawon lokaci.
Sauraniya Daurama ko Magajiya Daurama sarauniya ce da ta shahara a kasar Hausa, ita ce kabara ta karshe wace ta mulki kasar Daura, tarihi ya nuna cewa; sarakunan Habe sun mulki kasar Daura, sarauniyoyin
habe da suka mulki Daura su ne kamar haka;1.Kufuru 2.Shata 3.Gino 4.Walzama 5.Shawata 6.Daurama 7.Batatume 8.Yanbamu 9.Inna-gari 10.Ga-mata 11.Sanda-mata 12.Ja-mata 13.Zama 14.Yakumo 15.Yukuna 16.Gizir-gizir 17.Hamata 18.Daurama ||

MAGAJIYA DAURAMA
Tarihi ya nuna cewa; sunan mahaifiyar Magajiya Daurama Hamata, an haife ta wajajen karni na tara, ta yi sarauta Daura a wannan karni na tara. A wannan zamanin mata ne ke sarautar Daura, haka kuma Masarauta ta haramta wa duk sarauniyar da ta hau gadon
Sarauta yin aure.
Sarauniya Daurama || ita ce sarauniyar karshe da ta mulki Daular Daura. Tarihi ya na tuna wa da ita a matsayin Sarauniya kuma
mahaifiyar Sarakuna da suka kawo zaman lafiya tare da hade kan al’umma a kasar Hausa musamman Kasashen Hausa bakwai
da banza bakwai.
A karni na tara ne Magajiya Daurama ta mulki kasar Daura, tarihi ya nuna cewa, ta gaji sarautar Daura wajen danginta wadanda suka kasance tsatson Habe.
BAYAJIDDA YA ISA KASA DAURA
Bayan makeri ya kera masa takobinsa sai ya yi sirdi ya ja linzami ya nausa ya yi ta tafiya, kwana da kwanaki yana tafiya har ya isa kasar Daura.
Ya isa Daura cikin dare, ya ci gaba da tafiya har ya kai kofar wani gida, ya sauka saman dokinsa ya yi sallama, aka yi masa iso tsohuwa mai suna ayyana.
Ga gajiya ga yunwa gashi yana jin kishirwa, sai ya tambayi tsohuwa da ta sauke shi gidan ta, ya ce ta bashi guga zai ba dokinsa ruwa, sai tsohuwa ta ce; ai gari ba a samun ruwa daga kwana bakwai sai kwana bakwai ake samun ruwa a rijiya.
Ayyana ta kada kai ta ce;
‘ina? Ai mu a wannan gari bama samun ruwa sai ranar juma’a kawai, kayi hakuri’
Sai Bayajidda ya tambaye ta ya ce;
“me yasa ba ku samun ruwa sai bayan
mako daya kawai?”
Sai Ayyana ta ce;
‘Akwai wata katuwar macijiya mai karfi da tsawon shekaru sunanta ‘sarki’ a cikin rijiyar da muke samun ruwa, ita ce ta hana mu dibar ruwa sai ranar juma’a kawai, duk kuwa wanda ya saba dokarta ya je diban ruwa in ba ranar dibar ruwa ba sai ta kashe shi’
Da Bayajidda ya ji haka sai ya ce da Ayyana ta bashi guga dai ya je ya gani ko ya dace, ya ce;
“Bani madibin ruwa”
Ayyana ta ce;
“Me za kayi da madibin ruwa?”
Sai ya ce;
“Ke dai bani madibin ruwa”
Tsohuwa Ayyana ta dauko guga ta bashi,
ya fita daga gidan ya tafi rijiyar wace ake kira ‘kusugu’ inda Macijiya da take hana dibar ruwa ta ke.
BAYAJIDDA YA KASHE MACIJIYA
Da ya je ya zura guga a cikin rijiyar kusugu,guga ta fada cikin rijiya
ta bugi ruwa, ruwa suka kada.
ita kuwa macijiya da taji sautin kadawar ruwa sai ta fito daga cikin kogonta da take cikin rijiya, ta sanya bakinta ta rike guga ta jawo guga, shi kuwa Bayajidda ya ji an ja guga sai shima ya jawo gugar da karfinsa, sai macijiya watau ‘sarki’ ta karasa fitowa daga kogonta ta kanannade guga, ashe macijiya ta kanannade guga, Bayajidda ya jawo guga da macijiya kanannade.
Yana fiddo guga sai macijiya ta fasa kai, cikin zumma da zafin nama ya kai mata sura ya kama macijiya, yab fiddo takobinsa da makeri ya kera masa a garin Gaya, ya kama kan macijiya ya sare da takobinsa.
Ta jibge gawar macijiya bakin rijiyar Kusugu, sannnan ya sanya kan macijiya cikin jakarsa, ya debo ruwa ya kawo gida ya sha ya ba dokinsa sauran ruwa da ya rage ya ba tsohuwa. wannan rijiya ta kusugu tana nan
har yanzu a daura ana zuwa ziyarar gani da ido.
Tun da sanyin safiya. mutanen gari suna ta hidimominsu, wasu sun tafi gona,
wasu sun nufi kasuwa, wasu kuwa sun tafi harkokin yau-da-kullum, nan mutane suka ga gawar macijya ‘sarki’ babu kai, sa aka yi ta murna.
Duk wanda hanya ta kawo shi bakin rijiya kusugu in da gawar macijiya take babu kai sai yab ga abin mamaki, watau ga gangar jikin macijiya nan kwance mace, amma babu kanta, nan da nan mutanen gari suka cika wajen ana kallon abin mamaki, aka je aka gaya wa fadawan Sarauniya Daurama. Da labari ya kai fadar Sarauniya Daurama, fadawa suka garzaya aka gaya wa Sarauniya abin da ke faruwa cikin gari.
Sarauniya ta taso don ta ga abin mamaki da idon ta, tana ganin gawar macijiya sai tayi murna don macijiya ta dade tana gana masu azabar rashin ruwa, don tsananin murna sai Sarauniya ta yi rantsuwa
ta ce;
“Na rantse duk wanda ya kasha macijiya zan raba gari nan nawa biyu na bashi sarautar rabi”
Da jin wannan babban alkawari na Sarauniya sa kowa ya yi gurin ya kasance wanda ya kashe macijiya, don haka sai mutanen gari Sadaukai da majiya karfi kai har ma da fadawa tare da masu kudi su kayi ta cewa sune suka kashe macijiya suna samo kan maciji, ita kuwa Sarauniya duk wanda ya zo ya ce mata shi ya kashe macijiya sai ta ce;
“ina kan macijiya?”
Haka dai mutanen gari su kayi ta kawo kan macizai ana gwadawa da na Macijiya amma sai a ga bai yi daidai ba. Ana cikin haka sai wannan tsohuwa Ayana ta zo wajen Sarauniya Daurama ta ce;
“Akwai wani mutum da ya zo gidana bisa wani abu kamar saniya jiya da daddare (tana nufin doki, wannan zamani babu dawakai a kasar Hausa) ya ce na bashi guga, ya je ya debo ruwa ya sha ya ba wannan dabba har ma ya rage mani, watakila shi ne ya kashe wannan macijiya”
BAYAJIDDA YA AURI SARAUNIYA DAURAMA
Da jin haka sai Sarauniya ta sa a nemo mata Bayajidda don a tambaye sa ko shi ya kasha macijiya? Fadawa suka bazama aka nemo Byajidda aka kawo shi gaban Sarauniya.
Sarauniya ta ce masa;
“Ko kai ne ka kashe macijiya?”
Ya ce;
“Eh ni ne”
“To ina kan macijiya?”
Sai ya fiddo da kan macijiya ya ce;
“Gashi”
kowa ya ga kan macijiya, aka gwada aka tabba ta kan macijiya ne, sai Sarauniya ta ce;
“nayi alkawarin raba gari na biyu na ba duk wanda ya kashe macijiya rabin gari, tun da kai ne ka kashe macijiya zan raba gari biyu na baka rabi”
Sai Bayajidda ya ce mata;
“A’a bar rabin garnki, ni dai kyautar
da nake so kiyi mani, ina son ki aure ni”
Sarauniya ta yadda da bukatar Bayajidda, aka daura masu aure, ya tare gidan Sarauniya ita kuwa ta bashi kyautar
kwarkwara.
Mutane suka sanya wa Bayajidda suna
“Makas-sarki” daga baya kuwa aka daina fadar ‘Makas’ sai ‘sarki’ kawai, an ce daga nan ne sunan sark ya samo asali, amma kafin Bayajidda yazo Daura ya kashe wannan Macijiya ba’a san sunan sarki ba, ita dai Sarauniya ana kiranta ‘Kabara’ watau ‘Ubangiji’
A wannan zamani kuwa al’adar kasar Daura ta haramta wa Sarauniya aure kamar yaddda muka karanta can baya, shi yasa Sarauniya ta ba wa Bayajidda kwarkwara kafin ta karya asirin da ya hana su aure.
Ana nan, ana nan sai kwarkwara ta samu juna biyu, bayan wata tara ta haifi da namiji aka sanya suna ‘Karab’ da gari ma’anar wannan sunan shi ne; tun da Bayajidda ya samu magaji, zai karbe Garin Daura daga hannun Sarauniya Daurama.
kwanci tashi, ita ma sarauniya sai ta samu juna biyu, ta haifi da namiji aka sanya masa suna ‘bawo’ ma’anar wannan suna shi ne; a kawo garin da aka karbe, har yanzu na wa sarakunan Daura kirari da cewa; ‘karab- da-gari kai ab bawo’. Sarauniya ta mayar wa kwarkwara martani kenan.
‘YA ‘YAN BAYAJIDDA
Ya’yan bayajidda uku kenan, na farkon su shine; Biram wanda Magaram ta Haifa a Garun Gabas, sai Karab-da-gari wanda kwarkwarar Bayajidda ta haifa, sai kuwa Bawo wanda Sarauniya Daurama ta haifa.
Bawo ya haifi ‘ya’ya shidda watau jikokin Bayajidda, su ne suka mulki garuruwan Hausa Bakwai in aka hada da Biram watau dan Bayajidda na farko.
Karab-da-gari kuwa ya haifi ‘ya’ya bakwai suma jikokin Bayajidda ne, su suka yi sarautar garuruwan Banza bakwai.
YADDA SARAUTAR KASAR HAUSA TA RABU A GIDAN
BAYAJIDDA
Bawo ya haifi ‘ya’ya shidda, bayan Bawo ya rasu sai dansa na farko mai suna Gazori ya yi Sarautar Daura, na biyu kuwa shi ne Bagauda, lokacin da kasar Hausa babu zaman lafiya sai Bawo ya tura ‘ya’yansa kasashen
Hausa don su samar da zaman lafiya, Bagauda shi yayi Sarautar Kano a wannan zamani.
Na uku kuwa shi ne; Gunguma shi ya yi sarautar Zazzau, sai na hudunsu shi ne;
Doma shi ya yi sarautar Gobir, sai na biyar shi ne; Kumayau shi ya yi Sarautar Katsina, sai na shidda shi ne; Zaman-kowa shi ne sarkin Rano. Na cikon bakwai din kuwa yayan Bawo ne watau Biram shi ya yi sarautar Garun Gabas.
Wannan su ne garuruwan Hausa bakwai, ga jerin sunaye garuruwan Hausa bakwai da Sarakunansun a wan can zamani;
Daula Sarki
Daura Gazobi
Kano Bagauda
Zazzau Gunguma
Gobir Doma
Katsina Kumayau
Rano Zaman-kowa
Garun Gabas BiramWadannan garuruwa da bawo ya tura 'ya'yansa Sarakuna su ne ake kira Hausa Bakwai.

HAUSA BAKWAI
Bayan Bayajidda ya bar duniya sai dansa Bawo dan Sarauniya Daurama ya gaji Sarautar Daura, bayan daula ta kafu ana ta adalci cikin kasar Daura, a wannan lokacin kuwa sauran Daulolin kasar Hausa babu zaman
lafiya, zalumci ya yawaita a kasar Hausa da yawan yake-yake.
Lokacin da bawo ya hau gadon Sarautar Daura, an yi wata yunwa a kasar Hausa, babu in da ke da abinci sai in da a yanzu ake kira kasar Kano, sai mutane su ka yi ta tasowa daga garuruwansu suna dawowa
kasar Kano, sai kabilu suka yawaita a kasar Kano kowace kabila ta na zaman kan ta, zalumci, sata, fashi, kisan kai suka yi yawa a
kasar Hausa.
Sai wasu suka hada kai suka kai kukansu Kasar Daura saboda a wannan lokacin kasar Daura ce kawai ke zaman lafiya
da adalci.
Da tsogumma da kararraki suka yawaita sai Bawo ya yi shawara ya kafa Sarakuna a wadannan garuruwa.
Ya tura dansa Yakano wanda aka fi sani da Bagauda zuwa Kano, ya tura Gunguma zuwa Zazzau; ya tura Duma zuwa Gobir, ya tura Kumayau zuwa Katsina, ya ba Gazobi rikon Daura.
BANZA BAKWAI
Akwai kuwa kishiyoyinsu da ake kira Banza Bakwai wadanda aka ce Bawo ya tura wasu daga cikin ‘ya’yansa su mulki daulolin Banza Bakwai, wani kaulin na tarihi kuwa cewa ya yi;
Garuruwan da ake kira da Banza bakwai, suma garuruwan Hausawa ne, amma ana kallonsu ba cikakkun Hausawa ba, watau yarensu na Hausa yana da garwaye da wani yare. Karab-da-gari ya haifi ya’ya bakwai, su
wadannan ya’ya su ne suka yi mulkin garuruwan banza bakwai, garuruwan Banza bakwai su ne;
Zamfara
Kebbi
Yawuri
Gwari
Kwararafa
Nupe
Illori

ya hau gadon Sarautar Daura, an yi wata yunwa a kasar Hausa, babu in da ke da abinci sai in da a yanzu ake kira kasar Kano, sai mutane su ka yi ta tasowa daga garuruwansu suna dawowa

K