Skip to content
Home » Canjin Yanayi da Muhumman Abubuwan da ya Kunsa

Canjin Yanayi da Muhumman Abubuwan da ya Kunsa

canjin yanayi abu ne mai matukar mahimmanci a rayuwar Dan Adam wanda ko muna so ko bamu so dole mu tsaya mu kula da shi kuma mu yi masa kyakyawar fahimta yadda ua kamata yanada tasiri wajen habbaka tattalin arzikin kasa ko kuma nakasa shi shin ka taba tunanin yadda ada bamu dadewa un muna tona kasa muke ganin ruwa? yanayin daidaitunar yanyi na garuruwan mu ya canza? yanayin samun abinci ta fannin noma yadda ya ragu?

Duk irin wadannan abubuuwa suna da matukar amfani dangane da dumamar yanayi ko kuma in ce canjin sa gabadaya to a cinkin wannan post zamuyi bayaninsa da illolinsa da kuma yadda in aka gyara zaya taimaka sosai wajen habbaka tattalin arki baki daya .

Mi ake nufi da Canjin Yanayai?

Canjin yanayi yana nufin sauye-sauye na dogon lokaci a yanayin zafi, yanayin hazo, da sauran yanayin yanayi waɗanda ke haifar da ayyukan ɗan adam, da farko fitar da iskar gas kamar carbon dioxide (CO2), methane (CH4), da nitrous oxide (N2O). Wadannan iskar gas suna kama zafi a cikin yanayin duniya, wanda ke haifar da dumamar yanayi a hankali.

abubuwan da suka shafi canjin yanayi

Yawan fitar da hayaki yana haifar da illoli da dama musamman ta yadda ake karaa samun raguwar shukoki kuma idan muka gyara kanmu muka gyara kuma zaya amfane mu saboda zamu samu abinci mai yawa da kayan itatatuwa,

Misali a da iyayenmu sun kasance suna yawan shuke shuke na lambuna da gonakai amma yanzu hakan yana raguwa wanda kuma kamar yadda masana suka fadi yanayin yawan itatuwa yanayin yadda waje zai yi dadi sabosa za’a samu isakan oxygen mai sanyi kowa yasan idan akwai yawan itatuwa akwai dadin yanyi ko shakka wannan babu.

Domin a china akwai wani project a china da suka sama suna Green Wall of China ta hanyar shi suka yi ta kokarin shuke-shuke har suka maida sahara zuwa daji wanga hakan ya taimaka wajen karuwar ruwan yankin wanda manoma suka samu sauki sosai.

yanzu yanyin yadda muke tsadar abunci shin ko ka san cewa har a cikin buhunnan zaka iya noma abinci a karamin buhu ka samu amfani mai yawa da zai iya maka tasiri.

Karanta:

Fasahar Noma ba tare da kasa ba da yadda abun yake kasancewa(Hydroponics)

So akwai hanyoyi da dama na zamani da zamu iya noma wanda zasu taimaka ma yanyi da kuma tsare-tsaren shukoki na yayan itatuwa wanda mu mu amfana kuma mu amfanar da yanayin muhalin mu.

Ya Alamun sa ya bayyana ta fannin illoli

Canjin yanayi ya nuna ko kuma ma in ce maka yana cin nuna alamomi manya a fadin duniya wanda wasu abubuwan ake rasa su kuma hakan illa ce ga lafiya da tattalin azriki gabadaya. ga wasu muhimman kamar haka.

1. Rashin saurin samun ruwa da an tona

kowa ya san a da da ake yawan noma kuma ba’a yawan sare itatutuwa a tona a yi saurin samun ruwa bashi da wahala amma yanzu kullun sahara kara tunkaro mu take yi hakan yana taimakwa wajen kara samun dumamar yanayai da kuma raguwar ruwan sama.

2. Raguwar Ingancin Kasa domin Noma

Inagancin kasa yana raguwa idan aka ce yanayin iatatuwa ta shike-shuke na raguwa saboda ganyayen da ke faduwa da kuma yawan dabbobi da kwari ke rayuwa a waje yana raguwa wanda hakan illace ga yanyi , shiyasa da zaka ga a kana ganin wasu dabbobin daji amma saboda sunji yanyin wajen ya canza sun bar wajen saboda yanayin bau musu dadi ba.

3. Samun Karancin Ruwa da Fari

wannan abu ne wanda ya ke a bayyane kowa yasan damana ta da tafi yanazu a zamanin iyayen mu na da sun fi samun ruwa mai yawa fiyae da yadda mu muke samun su a yanzu wanda hakana yana da nasaba da dumamar da yanayin mu yake a ciki idan muka kyara muna koakarin inganta noma da suka itatuwa cikin ikon Allah za’a shawo kan wannan matsalar

4. Narkewar da kankara ke yi da hauhawar matakan teku:

A wasu sassan dunuya da su ke da teku Yanayin ɗumamar yanayi yana haifar da ƙaƙƙarfan ƙanƙara da glaciers narke cikin sauri, yana ba da gudummawa ga haɓaka matakan teku. Wannan yana haifar da babbar barazana ga al’ummomin bakin teku, ababen more rayuwa, da kuma yanayin muhalli, wanda ke haifar da karuwar ambaliyar ruwa, zaizayar kasa, da kutsawar ruwan gishiri.

Karanta:

Maganin Hawan Jini: Hanyoyi 5 Masu Amfani Domin Magance Hawan jini

5. Tasirin Lafiya

Canjin yanayi na iya yin tasiri sosai ga lafiyar ɗan adam, da ta’azzara cututtuka na numfashi saboda rashin ingancin iska, da ƙara yaduwar cututtuka, da yin illa ga abinci da ruwa. Jama’a masu rauni, kamar yara, tsofaffi, da waɗanda ke fama da talauci, suna cikin haɗari na musamman.

saboda au ba za a iya cin abinci mai gina jiki ba mai lafiya sai da ruwa anyi noma kuma to shiyasa canjin yanayi yana da rawar da yake takawa sosai a fannin lafiya.

6. Asarar halittu masu rai

Canjin yanayi na ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke haifar da bacewar nau’ikan dabbobi, saboda yana canza wuraren zama da kuma rushe yanayin muhallin su. Yawancin nau’o’in suna kokawa don daidaitawa da saurin canje-canje a yanayin zafi da hazo, wanda ke haifar da sauye-sauye inda za su zauna domin su ji dadin rayuwa wanda wasu dabbobin suna kara ma kasa tattalin arziki musamman irinsu zaki, giwa da sauransu.

Yaya za’a amfana da shi idan aka gyara?

Magance matsalar sauyin yanayi na bukatar hadin gwiwa a duniya, da kokarin hadin gwiwa don rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli, da mika wuya ga hanyoyin samar da makamashi, da kara karfin makamashi, da kariya da dawo da yanayin halittu, da daidaitawa da sauye-sauyen da aka riga aka samu. Yana da mahimmanci a dauki mataki cikin gaggawa don rage munanan tasirin sauyin yanayi da kuma kare duniya ga al’ummomi masu zuwa.

habbaka yanayi

Ga wasu daga cikin muhimman abubuuwan da za’a amfana da su idan aka gyara wanda ko yanzu akwai dammar makin sana’oi da mutum zai iya samu ta hanyar su.

Samun Abinci mai sauki

Ta hanayr komawar mu noma hakan zai taimaka sosai wajen inganta yanayin da muke zaune da kara samun kudin shiga saboda kamar yadda na ambata yanzu sai kaga mutane a gidansu suna noma dankali da sauran kananun shukokin da suke fitowa da wuri cikin buhuna da jarkoki kuma su samu amfanu mau yawa kaga hakan yana rage mamu wahalar tsadar abunci.

Samun aikin yi

ta hanyar inganta canin yanayi daga rashin kyau zuwa kyau hakan zai samar da aikin yi sosai ga matasa da kuma mutenen kasa bakidaya saboda za’a rika samun cigaban kere-keren abubuwa kamar na solar da kuma windmill wanda hakan suna samar da aikin yi da kuma rage yawan amfani da mai wajen samun haske ta hanayr generator.

Karanta:

Kananun Sana’oi 10 Masu Saurin Kawo Riba Wanda ake Iya Farawa Da karamin Jari

Kiwon lafiya da Haɓakawa

Magance sauyin yanayi na iya haifar da ingantuwar lafiyar jama’a da yawan aiki. Ta hanyar rage gurɓacewar iska, haɓaka sufuri mai aiki, da haɓaka samun ruwa mai tsafta da tsafta, al’ummomi na iya fuskantar ƙarancin matsalolin lafiya da haɓaka yawan ma’aikata, wanda ke haifar da fa’idodin tattalin arziki.

Kammalawa

A karshe dai kowa zai iya daukar mataki na habbaka canjin yanayi kuma abun ma yana da tushe daga addinin mu saboda duuk wanda ya shuka wani dan icce yana samun lada kuma sadakatu jariya ce bayan haka kuma mai noma ko turwa ta ci daga kayan amfaninsa zai samu lada bug da kara idan mutum yayi tunanin dama ce wadda har kasuwanci yana aiya farawa ya kirkiro wani abunda zai taimaki al’umma kuma shima ya samu kudi ga kuma shima an inganta yanyin mhallin da muke zaune