Ilimin Engeineeering ilimi ne mai zaman kansa wanda yanzu a duniya babu wani aiki da ya kai shi samun kudade a fadin duniya kuma yana da fannoni da dama wanda za’a iya karantawa a samu alheri. Shiyasa a cikin wannan post din mukace bari muyi bayanin kan ilimin engineering da kuma muhimman abubuwan da suka kunshe shi gami da shawara akan wanda ya karanta shi yadda zaya dogara da kanshi ko yake son karantawa.
Amma da farko bari mu duba mi ake cema engineering kuma wadanne ne manyan fannoninsa da yake da su?
Table of Contents
Minene Engineering
Engineeering ana yana nufin wani fanni ne da ake amfani da shi domin kere-kere abubuwan da suka shafi kimiyya da fasaha wanda dan adam yake amfani da su.
Yana da fannoni da dama amma babar manufar sa shine kirkirar kayan masarufin da mutum zayyi amfani da su yau da gobe misalan abubuwan da enginiyoyi sukayi sun hada da mota, jirgi, gida keke da sauransu.
Kafin zama engineer ana son mutum ya kware a fannin karatu kamar su lissafi, physics, chemistry da kuma Biology sai fanni zane amma duk wannan ya danganta dai da mi mutum yake son ya zama a fannin.
Kamar yadda binciken kasar amurka na US BERAU OF LABOUR ya gabata sun kamata karamin albashin engineer a kan dalan $600, 500 kamar yadda bincike ya tabbatar
Kasashe kamar su Nigeria idan mutum yana son samunsa a matakan makarantu irinsu jami’a ko kuma polytechnic ana bukatar ya ci jarabawar jamb maki fiye da 180 akalla domin samun saukin shigaya danganta ga makarantar.
Ga wasu daga cikin muhimman fannonin engineering da ya kamata ka sansu
Manyan Fannonin Engineering da Ake Samun Kudi sosai
Civil Engineering
Ya shafi fannin gine ginen zamani kamar su gada titi da sauran abubuwan da ake ginawa na kwangila wandan za’a iya ba mutum yayi.
Mechanical Engineering
Wannan fanni ya kunshi abubuwan da suka shafi karafuna da sarrafa engina yadda zasu bada abu mai amfani ta fuskar motsi.
Electrical Engineering
Wannan fanni ne da ya shafi sarrafa wutar lantarki ta hanyar kirkira circuit wato rumbun engina ta yadda zasu bada wani abu, kamar su wiring na gida da sauransu fanni ne da shafi raba wutar lantarki da sarrafa ta ta hanaya mai amfani
Chemical Engineering
Idan mukayi magana akan chemical engineering fanni ne da ya kunshi abubuwan sinadarai yadda mutum zai iya juya chemicals su bada wani abun amfanin da mutum zai iya amfani da shi kamar kayan shafe shafe turare da sauransu
Software Engineering
Shi kuma fannin software engineering sashe ne da ya kunshi na’aura mai kwakwalwa wanda za’a iya kirkiro manhajojin da za’a iya amfani da su a na’ura mai kwakwalwa ko kuma waya kamar apps ko softwares ta hanayr amfani da yaren computer programming languages.
Karanta:
Abubuwan aiki da ya kamata ka samu kafi ka fara hada android app da Programming
Biomedical Engineering
Wannan fannin engeneering ne da ya shafi fannin lafiya ta hanayr kirkiro abubuwan da zasu taimaka wajen maganuguna da kuma kiwon lafiya
Hanyoyin Zama Engineer
Akwai hanyoyi da dama da ya kamata kabi domin zama cikakken engineer wanda gasu kamar haka zamu yi bayaninsu.
- Karantashi a Matsayin Course
- Koyon Aikin
- Kirkira Ayyukanka
- Samun Lisense
- Hada Hulda Da Mutane
Yadda Zaka Dogara da Kanka a Matsayin Engineer
To yawancin mutanen da suka karanta engineering a kasashe masu tasowa kamar Nigeria wani lokacin saboda rashin samun aikin yi sai ka gansu haka nan wannan sai in kai ka so.
Saboda ka karanta abu mai amfani ka tashi ka gina kanaka kayi kokarin gina kamfaninka ko ka hadu da sauran abokai ku hada team saboda indai zaku hadu ku hada abu mai amfani za’a saya.
Dalilin shine a kasahe irin namu ba’a cika kere kere ba duk wanda ya fara sai kaga yana samu kar ka damu kace babu kayan aiki da zaka hada, a’a je online kana iya sawo kaya daga china kana nigeria zaune kurika hulda da kasashen waje saboda cigaban internet da aka samu yanzu sosai.
Misali wanda ya karanta Electrical Engineering ya rika hada abubuwan da suka shafi solar installation cikin gidaje ko wiring wannan duk aikin shi ne.
Ko kuma wanda ya karanci Chemical engineering yana iya fara kasuwancin saida kayan chemicals yana hada irinsu man shafawa, air freshner da sauransu.
Karanta:
Nau’in Kamfani 5 da Zaka Iya Fara su a Natsayin Karamin Dan Kasuwa
Author Profile
Latest entries
- Sana'o'iJanuary 6, 2025Koyon Sana’a: Muhimman Abubuwan Dubawa kafin koyon sana’a
- Kiwon LafiyaJanuary 3, 2025Maganin da Ganyen Parsely yake da suka hada da sanayi, cancer da sauransu
- KasuwanciJanuary 1, 2025Hanyoyi 5 na Juya Kudi da Suke da Riba mai Yawa
- Sana'o'iJanuary 1, 2025Gyaran Waaya: Yadda ake Fara Sana’ar Gyaran Waya