Skip to content
Home ┬╗ Android App: Abubuwan aiki da ya kamata ka samu kafi ka fara hada android app da Programming

Android App: Abubuwan aiki da ya kamata ka samu kafi ka fara hada android app da Programming

kamar yadda a baya a cikin wannan website ta WWW.HAUSAWASITE.COM.NG muka yi bayani akan yadda ake hada android app to a wannan post din inshallahu zamuyi bayani akan wasu daga cikin muhimman abubuwan da ya kamata a ce wanda yake son ya koyi hada app na android ya mallaka da kuma na koyo.

Domin akwai abubuwa da yawa da ya kamata ka sani kuma ka malla ke su, duka dai inshallahu zaniyi bayaninsu dalla- dalla amma bari mu fara da wadanda zaka mallaka na softwayoyi.

SOFTWARE DATA KAMATA KA/KI MALLAKA

Akwai softwayoyi ko in ce manhaja da yawa wadda ake hada android app da ita amma sananiya wadda kamfanin google ya fi ba mahimmanci ita ce android studio.
                  Yadda ake Hada Android App
                  
                   Yadda Zaka samu kudi a Internet

Android Studio

Android Studio
Android studio babbar manhaja ce ta android wadda ake hada android app da ita da yaruka na programming irinsu java, c++, kotlin da sauransu wadda tana nuna maka/ki abunda kake a cikinta.
Tana da saukin aiki ga yan koyo a wani fannin kuma tana da yar rikitarwar ta amma ba wani abun wahala bane ba sosai, to ina ba wanda zai fara shawara da yayi amfani da ita kusan ma dole ce ga wadanda zasu amfani da yaren java.
To ga link dinda zaka yi download din android studio a computer

Bayan ka dauko ita wannan software ta android studio to akwai aikin da zakai mata shinea zaka sa data ka ida sauran matakan intalling dinta a cikin computer dinka. 

Yana da kyau ka sani cewa ita wannan software ta android studio kafin ka daidaita ta domin ka fara hada android application ka tabbata computer ka tana da karfi wanda shine ya kasance kana da ram kamar 2GB haka da kuma isasshen hard disk a cikinta.
Karanta:

Wane Ilimi Nike Bukata idan ina so in fara Hada Android App?

Dangane da ilimin daya kamata na programming languages wadanda ake hada android application dasu suna da yawa amma daga cikinsu akwai java, kotlin, c++ da sauransu.

Amma dai a nan tunda na baka shawara kayi amfani da android studio kana ka iya java ko kuma kotlin duk wanda ka zaba a cikin su to lafiya lau. 

Da farko dai zaka koyi java ko a cikin sati ukku ko biyu sun isa ya danganta ga kokarinka, sai ka tafi akan yadda ake amfani da framwork na android wato yadda ake android programming kenan. a nan zaka cigaba da hada android apps to.

Ta wace Hanya zan koyi java da Android Programming

 Akwai hanyoyi da dama da zaka iya koyon java kana iya koyon su a youtube ta hanyar kallon youtube videos, inshallah zaka iya indai ka sa kwazo a ciki.

Da farko kaje ka koyi yadda zaka saita java a cikin computer dinka sannan ka koyi yadda zaka yi installing din android studio a cikin computer dinka.
Sannan kuma ka ringa yin browsing a cikin computer dinka na website a cikin computer dinka inda ake koyar da hada application da kuma downloading din littafi mai koyar da hakan

Kammalawa

A karshe dai abunda zance shine duk abinda kake son yi ya kasance kana son shi yadda zaka jure kuma ka sani duk abinda wani yayi tofa kaima kiana iya yinsa duk wahalarsa ko rintsi kawaio  dagewa ce ake so dakuma kokarin bincike da habbaka kai musamman abubuwa irin wadannan