Skip to content
Home » Android App:Yadda ake hada Android Application

Android App:Yadda ake hada Android Application

Android application yanzu kusan duk bubuwn da muke yi a cikin waya babu wanda za’a ce bai hada da amfani da Apps ba don harkokin mu na yau da kullum kuma shin  mai karatu ko ka san cewa kasuwar Appklication na wayoyi yanzu takai kusan fiye da dalar america billion daya.

A dalilin haka mutane da yawa suke ta tururuwa wajen shiga harkar application musamman na sanannar wayar hannu ta android wadda ta dauke kusan kashi 80 na kasuwar smart phone na duniya.

A cikin wannan post din mun shirya tsaf don kawo maku yadda ake hada Android Application, Hanyoyin da ake bi wajen hada shi da Kuma inda zaka daura shi mutane suyi sauke a wayar su.

Sanarwa

Akwai littafin PDF dinda muke hadawa gameda Hada Android App tareda yadda ake samun kudi dashi 

 kucigaba da kasancewa damu a koda yaushe muna gab da fara dora litattafai 

Facebook Page www.facebook.com/hausawasite

Wadanne Hanyoyi ne ake bi a hada Android Apps

Bari mu dauki Android mallakin  kamfani Google saboda tafi yawa a duniya kuma anfi amfani da ita musamman a nahiyar mu ta Africa fiye da ace Iphone ko windows phone.

Idan kana son ka fara hada Application dinka na Android ko kuma ka hada Application na kasuwancin ka to yana da kyau kasani #hanyoyin sun rabu gida biyu, zamu lissafa su tare da yin bayani gameda su.

 Hada Apps Batare da Programming ba

Wannan sananniyar hanyace wadda ake amfani da ita wajen hada Android application a cikin sauki.

 

yadda abun yake shine ana amfani da wasu websites na online wanda suka tsara software ta online domin ta hada ma mutane application din ta hanyar hotuna, rubuto ko kuma videos dinda suka daura.

wannan hanya mafi akasari na biyane amma suna bada damar gwaji ko ka hada na free kafin ka je zuwa matakin biya wasu daga cikin websites da suke irin wannan aiki sun hada da Andromo, Thunkable da kuma Appypie.

Wadannan suna daga cikin sanannu

Ta Hanyar Programming

Kashi na Biyu shine hadawa ta hanyar programming languages wanda kusan shin yafi, a wannan sashe zaka samu ilimin programming language wato yaren da ake amfani da domin ba computer umurni.

Amma sananniyar hanya da mutanen duniya suke bi shine su iya yaren kotlin ko java sai su tafi wajen android API din wanda zasu yi amfani da software wadda ake cema android studio su cigaba da kirkira application a ciki.

Kuma ka sani yana Bukatar kana da Computer mai karfi da sauri ba saboda babbar softwarea ce karanci 4GB RAM.

Karanta: Muhimman Abubuwan da zaka Lura dasu kafin sayen Computer

Akwai yaruka da dama da ake amfani dasu wajen hada android application gasu kuma kamar haka.

                            

Yarukkan da ake amfani dasu wajen kirkira Application na Android

 • Java
 • JavaScript
 • C++
 • C#
 • python da sauransu

Karanta:

Yadda Zaka Kirkira Game da Kanka

Koyon Programming na Computer cikakken bayani akan yaren computer

HANYOYINDA MASU HADA APPLICATION SUKE SAMU DASU

A yanzu wannan zamanin damuke ciki hada android application koma ince hada app kowane irine yanada amfani domin kusan duk kasuwancinda yakeson ya bunkasa sai yashiga fannin fasahar zamani.To adalilin haka masuhada android application suna samun kudi sosai gaskiya musamman idan manhajarka (application) yasamu karbuwa ta hanyar saukeshi cikin wayoyin dubban mutane, domin sanin kowane bama a app ba kowane kasuwanci yana bukatar jama’a.Adalilin hakane nikeson in lissafo hanyoyin da ake samun kudi dasu gamasu hada manhaja wato application na android.

 

BAYANIN HANYOYIN DA MASU HADA ANDROID APPLICATION SUKESAMUN KUDI

 1. Tallace – tallace
 2. Sayayya a cikin manhajar (application) din
 3. Sayen manhajar gaba daya (paid apps).

Hanyoyin samun kudi da android app

Bayani game dasu

Hanyar talla

a cikin manhajar (application) tana daya daga cikin hanyoyin da masu hadawa suke amfani da ita kusanma tafi yawa ko ince kaso mai yawa sunfi amfani da ita.Hanyar dake kawo kudi sosai gawadanda suka iya hadawa kuma suka maida abun sana’a.Idan kalura idan kabude application ko manhajar android zakaga tallace-tallace wadanda suke fitowa to yawanci tanan masu app din suke samu.

Wani lokacin masu manyan application kamar xender wadanda suka bunkasa a harkar zakaga wani kamfani zai basu manhajarshi (application) susa,to daka farama dan uwanka wani abu misali saikaga hada wani app yajemashi wanda bakai katura mai shiba to shima yana daga cikin talla da wancen kamfanin yabasu.

Sayayya aciki (fremium)

Wannan wata hanyace damasu kirkira application suke samu da ita, yadda abun yake shine suna sake wani abunda za’a saya aciki daka danna wajen saye zakaga inda zakasa lambobin katinka ka biya sai subaka abun.MISALI

A cikin game zakaga ana saida coins wanda zasu taimaka maka don zuwa wani mataki zakaga ansamasu kudi. A wadansu application ma zakaga sunayin shop fannin shago kenan wanda zaka sayi wadansu abubuwa.

Sayen manhajar gaba daya (premium)

premium apps hanyace ta samun kudi wanda masu hada manhaja suke amfani da ita.Yadda abun yake kuma anan shine application din ko manhajar basu hadashiba don kyauta ,ma’ana yadda kowa zai sauke a kyauta.A’a bayan sun bude account na daura application a google playstore misali suna bude marchart account wanda zasu rinka saida apps dinda suka hada.dazaran suka budeshi suka cike abubuwa ko addreshin bankinsu da lambarsu ta account to da ansaya su playstore zasu cire haraji in akwai sai su turomasu kudin ta banki,shikuma duk wanda zai sauke irin wadannan apps din bai iya safkewa ba saiyafara biyan kudi. Daya biya anzare ta banki sai yasamu damar saukeshi a cikin wayarshi.

Karanta:

Fasahar ChatGPT da Yadda take

Yadda zaka fara Sana’ar Saida Data

ABUBUWAN DASUKE TAIMAKAWA WAJENSAMUN MASU SAUKE APPLICATION DAYAWA

Bayan kahada manhajarka ko app dinka kana bukatar masu safkeshi ko shakka babu,wanda ta hanyar samun masu safke app din ne kadai zaka cimma burinka musamman idan wani abu kake saidawa ko ka saka wata talla dolene sai kanada yawan downloads.

Adalilin hakane a wannan littafi na kawo wasu muhimman abubuwanda yakamata kakula wadanda zasu taimaka maka wajen samun masu sauke apps dinka a wayoyinsu wanda gasu kamar haka.

 1. Inganta application din yadda yakamata
 2. Tallar app din
 3. Samun backlinks/masu rubutun akanshi a cikin shafinsu na yanar gizo (website) ko a bidiyo ta youtube channel.

Shawara Gareni

Idan zaka hada android apps ta hanyar programming language to ka tafi ga abubuda mutane suka fi iyawa shine yaren java ko kuma na Kotlin.
Su yi Download din Software wadda ake cema Android Studio su cigaba da hadawa.
Muna nan muna kokari hada Littafin PDF wadda zamuyi maka bayani dalla- dalla da hotuna akan Yadda ake hada Application tareda Bayanin hanyar da zaka samu kudi da abun Ku cigabada da kasancewa da Hausawasite.com.ng don samun post masu amfanin musamman na sana’oi.