You are currently viewing Kasuwancin Application da yadda ya Habbaka a Duniya

Kasuwancin Application da yadda ya Habbaka a Duniya

Idan mukayi magana akan application ko kuma idan ana son a rage mashi dogon zango a turance a ce apps wanda fassararsa a yaren hausa a ke cema Manhaja, to kasuwar apps ta habbaka yanzu sosai a fadin duniya wanda kamfunna da dama suna dosar billioyoyin kudade.

A cikin wannan post din inshallahu zamuyi magana akan ita wannan kasuwa yadda take da kuma yanayin su masu daura apps shin android apps ne koko na irinsu iphone ne  hadi da kuma hanyoyin da suke samun makudan kudaden shiga.

Ya Kasuwar Application Manhaja take

Ita wannan kasuwar ta apps tana daya daga cikin hanyoyin samun kudi na zamani na digital marketing wanda ake samun kudi ta abubuwan da ba ganinsu a ke a fili ba.

kasuwancin apps

Haakan ne ya samu bayan yawan da wayoyin zamani sukayi yawa kamar amdroid da Iphone wanda biliyoyin mutane suke amfdani da su a kullum kuma suna bata yawancin lokuttan su musaamman matasa masu tasowa.

A dalilin haka ne manyan kamfunnan wadanda suke da operating system suke cabaya sosai saboda babu wani wanda zai dora application dinsa a store dinsu face ya biya su kudin register.

Baya ga haka kuma suna da wasu hanyoyin wanda zamu yi magana akan su suma a nan gaba amma yanzu ga bayani akan manyan kamfunnan da kuma aikace aikacen da suke yi a fadin duniya.

Bari da farko mu fara dubawa akan wadannan kasuywannin da kuma abubuwan da ake daurawa kafin mu je ga yadda ake samu da su.

Google Play Store

Google playt store yana daya daga cikin sanannun kasuwar apps ko kuma ince daular application wanda suyka shafi operating system na android kamar wayar hannu ta android, agogon android, Tv da dsauran muhimman abubuwan da google suka hada.

Kasuwar google play

Google play ya samar da sana’oi sosai ga daukacin mutanen duniya musamman ma a kasashen da suka cigaba inda suke ba kimiyya da fasaha mahimmanci sosai.

Hakan ya samu ne a dalilin yawaitar da android ta yi wanda ta kere abokiyar hamayyar ta wato iphone ta fuskar masu amfanin da manhajar android din.

Kididdiga tana nuna cewar kusan kasi 80 cikin dari 100 na wayoyin da mutanen duniya suke amfani da su android ce sauran wadda ta biyo baya iphone da sauran opertaing systems na waya wanda suke biye a bayanta.

Hakan ya samu ne ta dalilin kwazon da kamfanin Alphabet ko ince maka Google suka yi wanda tun bayan sayen android da sukayi a 2008 suka bada lasisin ta ga kamfunna kyauta.

Kuma suka cigaba da aiki ba dare ba rana domin suga sun tabbatar da cewar sun inganta ta dama da sauran takwarorinta a fadin duniya.

Karanta: Android Apps: Applications Biyar masu amfani na Kamfanin Google wanda suke da matukar amfani a rayuwar yau da kullun

Abubuwan da ake daurawa a play store

  • Manhajar Applications
  • Litattafai
  • Finafinai
  • Games
  • Wakokin da sauran kayan sauti

App Store

App store kasuwar application ce itama maallakar kamfanin Iphone wadda take dauke da biliyoyin applications a cikinta domin yin installing ga masu amfanin da abubuwan iphone kamar waya tab da kuma computer.

kasuwar iphone

Developers da dama a fadin duniya suna dora applications dins a kasuwar kuma suna samun kudi sosai musamman masu dorawa domin a saya.

Saboda yawancin masu amfani da iphone a fadin duniya kamar yadda bincike yake nunawa sunfi saurin su kashe kudi fiye da wadanda ke amfanin da android.

Dalilin hakan kuma shine saboda yadda ita kanta wayar iphone din take tsada kuma abubuwan su ana yawan kashe kudi sosai hakan yasa subscription da kuma sayya a store din yafi  na androd sosai.

Ga wasu daga cikin abubuwan da ake dorawa a cikin store din kamara haka.

Abubuwan da ake daurawa a App store

  • Applications
  • Games
  • Manhajojin Agogon iphone
  • Fina finai da sauransu.

Yadda zaka fara

Idan kana da sha’awar ka zama developer wato mai kirkira apps kana dorawa a cikin wadannan kasuwannin akwai muhimman abubuwan da ya kamata ka sani wanda zasu taimaka maka wajen ka cimma burinka kamar haka wanda zaniyi maka bayaninsu kamar haka.

Tunanin Kasuwar da Zaka fada

A cikin duka wadannan wuraren da na ambata kafin ka fara yana da kyau ka tsaya ka natsu kayi tun ani sosai akan mi wace kasuwan kake son shiga.

Shin kana son kayi target din masu android ne? koko masu iphone? kuma kayi tunani mai zurfi akan mi zakayi masu wanda zaka taka rawa sosai saboda akwai apps ko abubuwa da yawa yana da kyau kaga ina rauni yake inda zaka shiga ka taka rawarka wajen inganta abun.

Ta hakan ne zaka gane inda zaka dosa tare da tsara yanayin kasuwancin yadda zaka yi shi sabaoda komai a duniya yana da bukatar a yishi a bisa tsari yafi tafiya daidai yadda ya kamata.

Karanta: Yadda ake fara kasuwanci da karamin jari

Koyon Ilimin kirkira

Abu na gaba kuma mai mahimmaci shine ina zaka samu ilimin abunda zaka kirkira ko kuma idan ka iya taya zaka cigaba da kwarewa yadxda ya kamata domin kayi ficce.

Mafi yawancin wadannan kasuwannin ana dora apps ne a cikinsu ko dai Andoid Application kom kuma Iphone Application to dole sai ka koyi yadda zaka yi su shin da programming ne koko ba da shiba.

A baya nayi magana akan yadda ake hada android application kana iya duba shi da kuma shi kanshi koyon programming na com[puter baki daya.

Karanta:

 Abubuwan aiki da ya kamata ka samu kafi ka fara hada android app da Programming

Abubuwan aiki da ya kamata ka samu kafi ka fara hada android app da Programming

Hada kasuwancinka

Abu na gaba kuma bayan ka samu ilimin hadawa ka hada ko ka kirkira abunka to sai kuma kayi kokarin maida yanayin kasuwancin zuwa kamfani yadda abun zai cigaba da tafiya.

Da haka ne turawa suka zarce mamu a cikin abubuwa da dama da kuma sauran kasashen da suka cigaba kullun suna kokarin kirkiro sabbin kamfunna saboda da haka ne za’a rage zaman banza wanda in kayi kokari zakaga mutane da dama suna aiki a kalkashinka.

Bunkasa kasuwancin

A karshe kuma shine sai kayi kokari kaga cewar idan ka fara samun kudi ta hanyar kasuwancin ka ka bude kamfanin ka koda karami ne to ya zaka bunkasa shi.

Daman bambanci tsakanin manyan kamfunna da kuma kananu shine bunkasawa wanda daga cikin hanyohyin bunkasa kamfani sun haada da yawan talla, kara zuba jari mai yawa da kuma kara aikace aiukacen wanda zasu habbaka kasuwancin da kuma kara samaun hanyoyin samun kudin shiga.

 

 

Author Profile

Ibrahim Buhari
Ibrahim Buhari