Skip to content
Home » Yadda ake Hada Website ko App ta Saida Data da Abubuwan da ta Kunsa

Yadda ake Hada Website ko App ta Saida Data da Abubuwan da ta Kunsa

Website ko Application  ta saida data abu ce wadda mutane a wannan zamani suke yawan yi kuma suna samanun kudi sosai idan suna da customers inda ba’a iya iyakance abunda mutum zai iya samu da VTU platform.

Ko kasan abubuwan da ta kunsa yadda take da kuma yadda ake farata a cikin wannan post din inshallahu zamuyi bayani akanta da yadda kaima idan ka tashi kana iya fara wannan sana’a.

Micece VTU Site

VTU site ko Manhajar App platform ne ko kuma manhaja ce wadda take bada damar sarar da data ko abubuwan services uwa ga yan kasuwa, ma’an mai sarin data da yawa da a kasansa yana da wadanda suke da app dinshi wanda yana sarar masu da datar.

A da kafin a samu cigaba sosai na saida data bama app yan kasuwa suke amfani da shi ba a’a suna sayen data ne mai yawa daga kamfunna irinsu MTN, Airtel da sauransu mai yawa su rika saidawa daidaya.

To da’aka samu cigaba ne ya amto cewa ta hanyar manhaja ko shafin yanar gio ake saidawa wanda yafi sauki da kuma kwanciyar hankali da kuma rage yawan asarar da ake samu a harkar kasuwancin.

Karanta:

Yadda Zaka Bude Kamfanin Abunda Ya Shafi ko Abun Sha Abinci a Nigeria

To yanada kyau ka fahimci cewa wannan kasuwancin ya rabu ne uwa gida biyu a yanayin yadda ake saro datar wadda a’a saida kamar haka:

  1. Masu API
  2. Masu SIM Hosting

Masu API

A wannan fannin yanayin yadda ake saro datar daga api na wani ne wato akwai connection da wani kamfani wanda yana bada damar sarar da services dinshi ga manyan yan kasuwa ta hanyar hadaka ta abunda ake kira da API.

A irin wannan mutum zaiya da jari kadan wanda ya kunshi saida data, katin waya, exam pin, Bills da sauransu cen ya zuba kudi ana dauka daga cikin wallet din API dinda ya zuba shi kuma ya daura ma na kasansa riba.

Masu SIM Hosting

Masu SIM hosting suna samo developer ne ya hada masu manhajar yadda zasu sayi data mai yawa daga kamfunnan sadarwa a cikin layukansu na waya inda za’a dora sim din online yadda ko an kashe shi data zata iya fita ko kati.

Idan suka saya da yawa sai a hada masu da manhajar saida datar su yadda da yan sara sun sayi daya daga layin wayarsu ya fita, wannan yana da bukatar babban jari kuma abu ne wanda yake da bukatar kula da taka tsantsan.

Mi Ake Saidawa

abubuwan da zaa iya saidawa

A irin wannan manhaja idan aka hada mutum yana da damar saida abubuwa da yawa wanda mutane suke yawan amfani da su yau da kullun kamar haka

  • Data
  • Kati
  • Recharge card
  • Data Card
  • Exam Pins
  • Electricity Bills
  • Subscriptions na Channels

Illolin VTU Site

VTU site tana da amfani sosai amma kuma a dayen bangaren kuma akwai abubuwan da ya kamata ayi taka tsantsan da su sosai don gudun mummunar asara.

Daga cikin abubuwan babban abu shine asara wanda shine ma jagora, akwai hackers wanda ka hada abunka kullun suna nan suna kokarin yadda zasu yi hacking din abunka su kwashi katin waya suje su sayar basu daukar data saboda sun san in aka turata na’a cika yawan turawa ba.

Amma kati amfi saurin saida shi cikin hanya mai sauki, shiyasa yana da kyau idan mutum yana da irin wannan website din ya rika taka tsantsan da kula da abunshi sosai saboda akwai barayi sosai da gaske.

Ya Zaka Mallaki Taka

Yadda zaka mallakin mahajar taka shine musamman idan baka da ilimin programming kana bukatar ace ka samu developer amma in ka iya programming kuma ka fahimce shi sosai abu ne mai sauki.

Karanta: 

Yadda zaka fara Sana’ar Saida Data

Domin in ka iya kana iya sayen script ka duba ka hada taka ka dora a hosting dinda kake da shi koma ka kirkiro taka da kanaka ba sai ka kaima wani yayi maka ba.

Idan baka iya ba kar ka damu akwai developers masu hadawa kudi zaka mallaki da kuma jari mai kwarin  gaske domin farawa ba tare ilimin programming ko coding ba.

Karanta: 

Skyly: Ƙungiyar Koyon Sana’o’in Zamani Domin Dogaro da Kai

CIKAKKEN BAYANI AKAN SAMUN KUDI ONLINE TA FREELANCING

Muhimman Abubuwa 10 na Waya da ya Kamata ka Sansu