Skip to content
Home » Hanyoyin Zamani da ake bi Domin Samun Customers Masu Yawa

Hanyoyin Zamani da ake bi Domin Samun Customers Masu Yawa

Kowane irin kasuwanci ne a duniya indai yana son ya tsira to tabbas ta hanyar customers zai bi watyo masu saye tunda sune suke kawo kudin shiga ga wannan kasuwancin suna kawo masa karuwa ta fannin kudin shiga.

A yanzu zamani da muke ciki akwai wasu muhimman hanyoyi na zamani da idan dan kasuwa ya bi su yana amfani da su suna taimaka masa wajen habbaka kasuwancinsa da kuma tallata ta shi a fadin duniya baki daya.

Dalilin haka ne muka dauki wannan ma’uduin a yau zamu kawo su tare da bayani akan yadda zasu amfani dan kasuwa a kasuwancinsa yadda zai samu kudi sosai.

Idan mukayi magana akan hanyoyin zamani kuma muna nufin fannin yanar gizo ko kuma ta hanyar fasahar sadarwa ta zamani wadda duniya yanzu ta raja’a akanta.

Sai kuma fanni na biyu wanda shine fannin abunda ya shafi design da abubuwan da ake gani wadanda suke jan hankalin mutane wanda ta nan ne zasu ji suna son su zo su sayi hajar.

Fannin Fasahar Yanar Gizo

Fasahar sadarwa ta yanar gizo ta zo da cigaba sosai ta yadda tana taimakawa kwarai da gaske wajen habbaka kasuwancin mutane a a fadin duniya bakidaya kuma ga muhimman rassana ta ko in ce misalan hanyoyinta da ake bio.

Karanta: Koyon Internet da Abubuwan da Suka Shafe ta

Facebook Market Place

Facebook market place wuri ne wanda zakayi iya tallata hajarka ta hanayar daura ta a kyauta da kuma farashinta gami da yanayin yadda take wato ta hanyar bayani akanta.

yadda ake amfani da facebook marketplace

Wannan kafa ko dama da kamfani facebook ya ba yan kasuwa yana taimakama mutane da yawa saboda da yawa ana sayen hajarsu, dalilin kuwa shine yawanci na area ko garinku suke sawa.

Yadda za kayi magana za’a kawo ma to idan kana da haja ka daura haka zakaga an turo ma sako ana tayawa wanda yawanci yan garinku ne sai ya tura kudi ka kaimashi ko kuma kuyi mahada a wani wuri.

Karanta: Muhimman Abubuwan da suke Taimakawa wajen samun Nasara a Kasuwanci

Whatsapp Business

Whattsapp suma ba’a bar su a baya ba domin ta kafar kana iya saita yanatin kasuwancinka wanda zaka bude shagonka na kasuwa a samansa.

Ta hanyarsa zaka iya daura kaya kan tuyrawa groups na mutane wanda idan suka bude zasu gani wanda yai masu suna iya yim magana kai tsaye su turo maka sako.

tallar kasuwanci ta whatssapp

Akawai kuma masu dubara wanda suke hada facebook dinsu da whattsapp sai su Tallata hajarsu a facebook yadda da an danna

Shafin Internet

Shafukan internet na daya daga cikin muhimman wurare da ake sayen talla a dora ma mutum ta hanyar biyan kim yan kalilan a dora mashi.

Yadda abun yake kuma shine mutum idan yanada wani kasuwanci nasa zai je shafin da ke da ke da mutane dawa inda ana yawan ziyartar wajen ya saye talla a dora masa.

Kamar a wannan website ta Hausawa Site mun bude wani shiri na taimakon yan kasuwa ta hanyar tallata masu kayansu a kudi yan kalilan da kuma yi masu banner wato hoton talla idan kana son ayi ma kasuwancinka a kawo ma customers to ka tuntu bemu kamar haka.

Whattsapp +2349037157675

Email: fasahaltd@gmail.com

Fannin Zane da abunda ake gani

Kamar yadda muka yi bayani a fanni na farko na fasahar yanar gizo da kuma sadarwa to kuma akwai fanni na biyu wanda shine shine na designs da kuma abubuwan da ake gani wanda ake amfani da su wajen jan hankalin wanda zai sayi haja.

Banoni na Hoton waya

Bana tana taimakawa sosai saboda misali a wajen status ka huta kawai saidai ka dora design dinda aka yi maka na kasuwanka ka yi tallarsa yadda abokanka zasu gani daga nan wani zai saya kai tsaye.

Hotuna ne na jan hankali wanda idan mutum ya gansu zai ji yana son sayen abun saboda yadda aka tsara su soisaia kamar yadda mukayi bayani a baya akan yadda ake habbaka kasuwanci ta hanyar design da banners hotuna kenan.

Karanta: Yadda zaka kyara kasuwancinka da hanyar hotuna don jawo hankullan masu saye

Bugaggun Banoni

Suma wadannan suna taimakawa sosai amma sun fi amfani ne ga wadanda suke da shaguna na satar da wasu abubuwa kamar na saman da mukayi bayani ne design ne amma bambancin shine su an buga su manya a fili ana ganinsu.

Ba kamar na cikin waya ba hoto ne kawai yawanci zaka ga masu shaguna suna sasu a gaban shagonsu ko kuma a cikin shagon domin bayani akan hajar da suke saidawa a shagon ko kuma wajen kasuwancin.

Suna taiamkawa sosai domin suna haska wauri tare da kayata shi gami da bayanin abunda ake saidawa a wurin yadda mai saye zai fahimci inda aka dosa.

Karanta:

Yadda ake fara kasuwanci da karamin jari

Yadda Zaka Samu Kudi a Wayarka ta Hanyar Zuba Hannun Jari a Kamfanoni

Nasara a Kasuwanci: Muhimman Abubuwan da suke Taimakawa wajen samun Nasara a Kasuwanci

 

 

 

 

 

 

 

Tags: