Skip to content
Home » Kasuwanci: Yadda ake fara kasuwanci da karamin jari

Kasuwanci: Yadda ake fara kasuwanci da karamin jari

Kasuwanci dai abu ne mai kyau kuma shine wanda ya fi aiki domin a duniya idan ana maganar kudi ba’a kawo ma’aikaci ace wai shine yafi kowa kudi misali amma a kullu kaw zakaji yan kasuwa sune a gaba saboda tarin abubuwa dasuke a cikinsa.

Kasuwanci

 

 

 

 

 

 

 

A wannan post na yau zamuyi magana akan kasuwanci ne kamar yadda ma’abota ziyartar wannan shafi suka sani muna yawan kawo maku abubuwan da suka danganci kasuwanci kala-kala kamarsu yadda zaka fara kasuwancing printing da photocopy, Man shafawa, Air freshner da sauran Sana’oi daban daban.

Mi Ake nufi da Kasuwanci?

Kasuwancin yana nufin juya wasu kudi ta hanyar sayen wani abu da saida shi ta hanyar da za’a samu fiye da kudin da aka zuba wanda shi ake cema riba. Wanda yake yinshi shine hausawa ke kiranshi dan kasuwa.

Tun da dadewa bahaushe yana da nau’ikan kasuwancin dayake kala-kala kamar su saida kayan noma saida kayan kira da sauransu.

Tunda munyi matashiya kame da shi bari mu tafi akan yadda zaka fara naka da karamin jari.

Yadda zaka fara da karamin jari

Kafin ka fara kasuwanci yana da kyau kasan wane zakayi, a ina yakamata kayishi kuma suwanene zasu sayi hajar da kake son saidawa da kuma ya zaka tallata hajarka. sanin wadannan abubuwa shi zai taimaka maka kwarai da gaske cikin ikon Allah.

Domin yana da kyau ka sani shifa kasuwanci ana iya cin riba kuma ana iya faduwa a koda yaushe, saboda haka shi kullun dan hakuri ne.

Karanta: 

Bayani kameda Tallar haja a Facebook

Abubuwan da yakamata ka iya a Computer

Matakan da zaka dauka idan kana da karamin Jari

Akwai matakan da mai karamin jari ya kamata yabi ko yaringa kamanta su domin habbaka kasuwarsa, kai bama mai karamin jari ba har ma babban dan kasuwa ya kamata ya kiyaye don habbaka nasa kasuwancin.

Lokaci

Lokaci nada matukar tasiri a cikin harkar kasuwanci saboda wanda yabada awowi da yawa yafi wanda bai bada ba kuma akwai wani sirri a cikin bude shago ko kasuwanci da wuri shine samun albaraka.
Lokacin Kasuwanci

 

Wanda yake budewa da wuri a addinence ma yafi samun albarka wanda idan ka lura wadanda ba hausawa ba kamar yarbawa sun ruga mamu a nan to loakaci nada mahimmanci yawan budewa da kuma budewa da wuri saboda baka son wani yazo bai iske ka ba.

Jalafta Jarin

A matsayinka na mai karamin jari ya kamata ka koyi jalafta jarinka ba komai kaga wani yafyi ba kace sai kjayi musamman idan abun ma yafi karfinka.
Da hakane musamman ake rudar mtasan mu kaga matashi bayadakudin kasuwanci ko bai fara ba amma kullun jira yake sabuwar waya kirar kamdfanin iphone tazo ya saya kaga akwai matsala shi kullun ya iya ya kashe ba ya tanada ba.

Inganta Hajar

Ya kasance hajar da kake saidawa ko aikin da kake ma masu saye kana bada abubuwa masu inganci  ba jabu ba domin idan mutane suka san kana da ingancin kaya to ko daa ina ana iya zuwa amma hajar ba inganci akwai matsala a kasuwancin ba karama ba.
Karanta: 

Adana Kudi don Gobe

Idan ana kasuwanci ana son a ringa aje kudi saboda wata rana kana iya bukatar ka sayi sabon kayan aiki.
ko kuma wani lokacin ma kwatsam ba zato da tsammani sai kaga kayan aikin ka wasu sun lalace to idan akwai ajiya ko wani abu da aka adana kaga cikin sauki sai a fiddo kamar yadda abahaushe ya ce ajiya magnanin wata rana.

Bincike Game da Kasuwancin

Yawan bincike akan kasuwancin da kake yana taimakawa wajen kyara shi saboda idan wasu hanyoyi na zamani sun zo yadda zaka yi saurin amfani da su.

Misalin da zan iya baka irin wannan shine kamar a da babu yanar gizo wato internet gabakidaya ana ta kasuwanci kara zube da tazo yana da kyau a matsayinka na dan kasuwa kayi bincike akan yadda zaka habbaka naka kasuwancin ta hanyar ta.

Karanta:

Hanyoyi 5 na Juya Kudi da Suke da Riba mai Yawa

Kasuwancin Saida Gidaje da yadda ake Samun Kudi da shi

Na’oin Kasuwanci masu Riba Sosai

ya danganta shin kai karamin dan kasuwa ne ko kuma babba da ya kake tunanin zaka fara da kuma yanayin karfin jarin da kake son ka saka a cikinsa, amma ga wasu daga cikinsu wanda na zakulo masu saurin kawo riba sosai imma kai karami kake son ka fara ko kuma babba dukansu link ne kana shiga a kowanen su.

Kammalawa

kamar yadda nike yawan ambato cewa shiu kasuwanci dan ahankali ne kuma abu ne wanda yake da ukatar hakuri domin musamman idan kana farko abun akwai wahala wani lokacin kana iya zuwa ka tafi ba’a yiu ko sisiu ba, amma wani lokacin kaji aljihu ya cika, akwai hasara akwai kuma riba duyka duk sai an yi hakuri da su don samun cimma burina abunda ake so